ELHAJJ 2


 ðŸ¤ŽðŸ¤ŽðŸ¤ŽðŸ¤Ž

                    *ELHAJJ*

                                  🤎🤎🤎🤎


Free page 2

    

   Written by

        Mrs A.M


Marubuciyar 

*NOOR*

*TASWIRAR KADDARA*


Wannan book din na kudi ne akan farashi mai sauki 300, ki biya kudin ki, ki karanta cikin salama ngd.


Ga mai son biyan kudin book din ku tuntubi wannan number din.

09066728387



*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃



*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*


*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*



*LOCATION KANO*


08062073990


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



      Ba ita tashi ba sai da Yaya Hajara tazo ta tashe ta, lokacin sallah yayi.


Mika nai na mike ina fadin "gaskia da baki katse min bacci naba Yaya Hajara, ina cikin mafarki mai dadi ynxu kin katse ni".


Banxa Yaya Hajara tai mata ta shige warta dakin mijin ta, ganin haka yasa na mike ina turo baki, alwala nai nayi sallah.


Kallon Agogo nai dake makale a jikin bangon palourn, da sauri na mike nace "wayyooo an shiga islamiyya tun dazu, ynxu ya zanyi".


Shiru nai ina tunani nasan in na tafi islamiyya tofa daga nan gida zan wuce knn baxan dawo gidan Yaya Hajara ba na Jira dawowar Baban Aisha, dakin Yaya Hajara na shiga na dauko hijab dinta dogo har kasa nasa, duk iskanci na bana wasa da islamiyya don anan kam brain dina yana mugun ja, last year na gama haddar Qur'ani ynxu littafai kawai nake yi sai kuma muraji'a da muke kullum.


Fitowa nai dai-dai lokacin da Yaya Hajara ta fito daga dayan dakin, kallona tai tace "sai ina kuma sarkin yawo".


Turo jajayen lips dina nai cike da shagwaba nace "Islamiyya fa zanje, lokaci ma ya kure sosai amma dai zanje gaskia".


Daga kai tai tace "daga nan gida zaki wuce knn koh".


Daga kai nai nace "insha Allah, ki kawo kudi na siya wa Aisha alawa a makaranta".


Zama tai akan kujera tace "ynxu ke alawar da za'a siya wa Aisha ma sai kince na bada kudin, ina zaki kai son kudi ke kuwa Dije".


Kamar zan kuka nace "gaskia ku daina cemin Dije sai kace wata yar kauye, suna na Khadija suna mai dadi amma an bata min ai duk laifin Kaka ne data bata min suna haka kurin sbd sunan ta aka samin sai tace sai dai a cemin Dije shi kuma Baba ya yadda nidai an cuce ni gaskia".


Yaya Hajara data saki baki tana kallona tace "ynxu dai ita kakar kike fada wa haka, bayan ta mutu ma baxa ta huta ba Dije".


Daga kafada nai nace "ni ai ba Allah ya isa naja mata ba kawai dai nayi yan fad`e-fad`e ne akan yadda ake batan suna ynxu dai shiknn kawai bara naje islamiyyar sai wata ran kuma, don ba nan kusa zan Kara zuwa ba kullum nazo sai kin sani nai wanka haba.."


"Allah ya kiyaye" kawai Yaya Hajara ta ce mata don ita ta gaji da surutun Dije ko gajiya bata yi.


Fita nai a gidan a kafa nake tafiya ta a nutse har na isa karkasara unguwar mu, a kasan layin mu islamiyyar take ko da naje ba wanka ya tare ni akan makara, aji na shiga na zauna na maida hankali na sosai, dama kuma ni bani da kawa bama a kawancen dani wai na cika kazanta, kawata Yayata ce kawai da ita nake shawaran komai.


Sai 6 muka tashi ban tsaya komai ba ma nufi kanti, ina zuwa na mika dari biyun hannu na nace "gashi bani omo na 100 da sabulun 40".


Miko min yai ba tare daya min magana ba don ya san halina ina karba na wuce gida.


A hankali nayi sallama yadda nasan ba Wanda zai ji ba kowa tsakar gidan da alama duk suna dakin su ko yaran kuma basu kai ga dawo wa daga islamiyya ba.


Labule na daga na shiga dakin mu ina sanda kamar wacce tayi sata, saki Mama tai tace "zaki shigo ne ko sai na janyo ki mara kunya".


Shigowa nai ina bubbuga kafafu a kasa cike da shagwaba nace "kai Mama don Allah maimakon ki dinga riritani kina dora ni akan cinyar ki tunda nice auta amma sai hantara ta kawai kike....."


Girgiza kai tai tace "a haka Zan dinga ririta ki din kina kazanta da rashin kunya ai sai dai kiga ana ririta wasu badai ni na ririta kiba".


Zama nai ina turo baki, kamar zanyi kuka na nuna Aisha dake bacci akan cinyar mama  nace "kin ga fah mama kin wani dora wannan yarinyar akan cinyar ki bayan nice nan autar ki ba ita ba".


Girgiza kai Mama tai tace "ynxu dai da Aishan kike kishi yarinyar da bata fi shekara hudu ba".


Daga kai mai ina mar mar da ido, girgiza kai kawai Mama tai tace "wannan kayan Hajara ce ta saki wanka koh?".


Daga kai nai ina murmushi na cire hijab din nace "har wanke min kai tai amma sai da ta bani 200 sannan na yadda".


Rangwashi na Mama tai tace "Allah ya shirye ki, wankan ma wanda ke zai amfana sai kin karbi kudi".


Turo baki mai ina sosa kan nawa na Mika mata ledar hannu na nace "Mama kinga fa nace ta bani ne sbd na siya mana Omon wanki da sabulu namu ya kare kuma Baba baxai bada kudin da zamu siya ba sai karshen wata kin san shi fa".


Shiru Mama tai tana duban Dije cike da kauna, Ashe duk shirmen ta tana kula da sabulun su daya kusa karewa, murmushi tai tace "Allah ya miki Albarka amma da baki karbar mata kudi ba'ai koh, ki wa kanki fada don Allah ki dinga tsafta aure fa za'a miki wata ran Dije".


Boye fuskata nai a bayan Mama nace "tab ba auren da zanyi mama ina nan tare dake kawai sai nayi aure nifa ko saurayi ban da shi, ina kallon yadda Hajjo take ta tara samari amma ni ba Wanda yake cewa yana Sona".


Dariya Mama tai tace "taya za'a ce ana sonki bayan kazanta kike, ita hajjon baki ga kullum take wanka ba tana sa turare amma ke turaren ma sai ana fama kafin kisa".


Sosa bayan wuya na nai nace "toh Zan kiyaye Mama, zan dinga tsallaken kwana daya daya ai nayi kokari ko kuma xan dinga sa alumun".


Tabe baki kawai Mama tai tana kara volume din radion ta.



********

  Cikin takun sa cike da kasaita yake fitowa daga building din, gefen sa Salim ne magana suke akan wani business da Elhajj din yake son fara wa, na sabon companyn da zai bude wanda za'a dinga leda da robobi.


Mota Elhajj ya shiga yace "sai gobe ma karasa Salim na gaji sosai".


Dariya Salim yai yace "tab! Lallai tunda yau Elhajj guda ya gaji dole kowa ma ya gaji".


Murmushi Elhajj yai Wanda ya sa dimples dinsa lotsawa gaba daya, girgiza kai yai yace "Allah ya shirye ka".


Dariya sosai Salim yake yace "sai anjima a gaida Madam".


Daga kai yai ya rufe motar, ba tare da ya kalli Driver din ba yace "Gidan Momma"


Cikin bin Umarni yace "ohk sir"


Yana bayan motar yana zana wani sample na atampa da yake son a masa irin su, ya dukufa a zanen har suke iso, bai fita daga motar ba sai da ya  gama zanen ya tura sannan ya fita daga motar.


Masallacin dake jikin gidan ya fara shiga yai sallah, tare suka fito shida Papa suna tafiya a tare amma ba Wanda yai ma wani magana.


Sai da suka shiga cikin palourn suka zauna sannan ya kalli Papa yace "ina wuni"


Daga kai Papa yai yace "lafia Elhajj, kuna lafia?"


Daga kai yai a hankali ba tare da yai magana ba, murmushi Papa yai yace "miskilancin naka har yau dai bai sauka akai naba koh".


Sunkuyar da kansa yai yana sakin murmushi kadan


Shigowa Momma tai bayanta masu aiki ne dauke da flask na abinci da tray, Zama tai tana dariya fuskar ta a washe tace "son sannu da zuwa ynxu kazo amma koh".


Murmushi yai ya daga Kai yace "Ina wuni Momma".


Murmushi tai tana kallon sa tace "lafia qalau son, ya gida da harkokin?"


A gajarce yace "Alhamdulillah"


"Masha Allah", ta fada tana mikewa zuba masa zobo Mai sanyi tai ta mika masa tace "gashi nasan tunda ka fita ba lallai kaci abinci ba".


Bai Mata musu ba ya karba yana kaiwa bakin sa idonsa akan TV, sai da ta tirsasa shi yaci abincin kadan don baya cin abinci sosai sai fruits.


Mike wa yai zai fita bayan yai musu sallama da sauri tace "son kaje gurin Malam kuwa, ya min magana rannan yace kana lafia dai koh".


Hade rai yai sosai kawai yasa kai ya fita, kallon Papa tai kamar zatai kuka tace "ban san me yake damun son ba ya dauke kafa daga zuwa gurin Malam gaba daya, kuma in an masa magana ya shiga hade haden rai".


Daga kai Papa yai cike da jimamin sabon sauyin da yake gani a tattare da dan nasa yace "Nima na lura da hakan don ya chanja sosai ba kamar yadda yake ba, duk da miskili ne amma ynxu abin yafi worst".


Rausaya kai Momma tai tace "sai addu'a kawai zamu cigaba da yi masa".


Sai da ya tsaya ya siya wa Saudat tsire don yasan tana son sa sosai sannan suka karasa gida.


Cikin nutsuwar yake tafiya hannun sa rike da jakar sa sai ledar tsiren ta, da sallama a bakin sa ya shigo tana kwance akan kujera tana kallon Sunna TV, da sauri ta mike ta taho a guje ta fada jikin sa.


Dan murmushi ya saki yana tapping bayan ta yace "sannu da zaman gida".


Sakin sa tai tana turo baki tace "uhm sannu koh, ai kai xanwa sannu Elhajj kai ka gaji sosai muje kayi wanka".


Bai ce komai ba yayi gaba tabi bayan sa, Sama suka hau inda dakin sa yake, fita tai ta barshi don tasan bai cika son takura ba a irin wannan lokacin daya dawo a gajiye.


Wanka yai ya zira jallabiya ash colour, turare ya fesa ya fito palourn saman Wanda ya kasance nasa, a nan ya sami Saudat ta tasa tsiren a gaba tana ci.


Murmushi ya mata kawai ya sauna a kan kujera, watermelon juice din da take masa kullum ya dauka ya fara sha yana kallo, sai da ya gama shayewa tas sannan ya kalli Saudat da zuwa lokacin itama ta gama cin tsiren nata.


Mike wa yai yace "muje mu kwanta", 


Dan mika tai tace "muje Elhaji na".


Tare suka kwanta ba tare daya neme taba don yasan koya neme tama sai dai ta sa masa kukan shagwaba, tun yana kokarin neman ta sosai har ya hakura sai in ita ta nema da kanta tunda bata cika son yana neman ta ba....



*********


Yau Monday zamu koma school, tunda na tashi nake kunkuni da bata rai bana son makarantar boko kamar me, bama yadda ake kirana da kazama, kuma ina gane karatun dai-dai gwargwado kawai dai bana son zuwa ne don ana takura min da tsokana.


Mama tana lura dani ta min banxa, sai kunkuni nake shiryawa nai cikin uniform dina Riga da wando sai hijab mai girma har ya kusa gwiwa ta, nayi kyau sosai kuma anyi sa'a yau nayi wanka ga kayana a wanke.


Jakata na rataya a baya na kalli Mama nace "nidai gaskia Mama wannan abun ya ishe ni ynxu haka zamu tafi ba'a gama abinci ba gaskia su Umma suna gasa mu wallahi, koko ne fa zasu dama kawai amma sun tsaya nauyin jiki haba don Allah kamar ba Mata ba".


Make mata baki Mama tai tace "ke ban hana ki wai yin rashin kunya ba don gidan ku, na rasa ina kike koyar wadannan maganganun haba, kullum baki da aiki sai yiwa manya rashin kunya".


Buga kafata nai a kasa nace "Mama lokaci fa ya tafi haka zamu tafi ban sha komai ba haba haba ayi adalci a lamarin nan".


Hajjo ce ta turo kofar palourn tace "ki fito zamu wuce ko zaki tafi da kanki".


Hararar ta nai nace "toh sarauniyar iyayi gani nan zuwa, an gama kunun ne?"


Tsaki Hajjo tai tace "aikin banxa mutum sai shegen ci kamar gara, to ba'a gama ba sai ki zo mu wuce ai koh".


A harzuke na taho kusa ita nace "ni kike fadawa maganar banxa, sa'ar kice ni?".


Wani kallo ta min tana Jan tsaki tace "aikin banxa kawai, ai baki kai matsayin da zan tsaya ina fada Miki magana ba wallahi, banxa kazama nafi karfin ki".


Kut** bansan lokacin danai jifa da jakata ba na rarumo wuyanta, cikin duka karfin da Allah ya bani na hankada ta wajen kofar ta fadi ban bata damar mikewa ba na mara mata baya na hau ruwan cikin ta ina danna Mata naushi na baki.


Da sauri Mama ta fito daga dakin kokarin daga ni Mama take amma sai kara sukuwa nake akan cikin hajjo ina bata naushi, ita kuwa ta kasa ko cizo na don duk na hana ta damar da zata cije ni ko ta dake ni.


Ihun yaran gidan ya fito da Baba daga dakin sa da sauri, jan burki yai yana kallon yadda Dije take dukan hajjo duk ta hada mata jini da majina,.


Zuwa yai ya sa kafa ya hambare ni nayi baya na bugi da bango, wani ihu nasa ina mikewa tsaye da sauri ina sosa hannu na inda na buge.


Kallona Baba yai yace "wata iriyar muguwa ce keh, zaki hau cikin ta ki dinga duka".


Sosa hannu na nake na kalli Hajjon dake tsungunne Umma na zuba mata ruwa tana wanke bakin ta daya fashe.


Turo baki gaba nai nace "rashin kunya ta min fa".





*BOOK DINNAN NA KUDI NE AKAN FARASHI MAI SAUKI 300 KA/KI SIYA KI KARANTA CIKIN SALAMA DUK WANDA YAKE SON SIYA YA TUNTUBI WANNAN NUMBERN*


09066728387



Comments Nd share plz



Mrs A.M

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links