SANADIN LABARINA 59


   Page (59)


***Alarm din da ya saita ne na karfe 4 daidai ya tashe su, kallon juna sukayi a lokaci daya sukayi murmushi 


"Morning Baby." 


Yace yana janyewa ya sauka daga gadon,


"Morning dear.". Tace tana maida masa murmushin. Tashi tayi ta sakko ta nufi wajen kayan su shi kuma ya fice daga dakin. Dan sake gyara kayan tayi sannan ta shiga toilet tayi brush da alwala ta fito tayi raka'atanil fajr ta zauna tana addu'a har aka kira sallar fajr din ta tashi tayi sannan ta cire Hijab din ta fito falon tana tafe tana azkar. Kitchen taje ta sake duba abinda bata sakashi wajen da ya dace ba, ta dan dauraye cups din da Ya Tariq din yasha coffee jiya sannan ta dauko wasu cups din ta dora su akan Iceland ta dafa ruwan tea tasa a flask shima ta dora a wajen sannan ta dawo kan falon a gurguje ta sake gyara shi ta tabbatar komai daidai sannan ta nufi dakin sa. Knocking ta fara yi sannan ta tura kofar bakin ta dauke da sallama. Yana tsaye gaban mirror yana rik'e da bathrobe ta shigo,.


"Yanzu zan kiraki dama." Yace yana sakin rigar wankan ya riko hannun ta.


"Muje muyi wanka Fauwaz yana hanya tare da yaran chan wai sai sun rakaki dole."


"Allah sarki yan uwana." Tace tana murmushi


"Oya." Ya kama hannun rigar zai hau cire mata tayi saurin kwacewa


"Zan iya." Tace tana dariya


"Nima zan iya ai."


"Toh na hutasshe ka, kayi wankan anan ni zanyi a daki."


"Why? Me yasa?"


"Zamu bata lokaci ne."


"Ba wani, kawai dai kinsan baki da gaskiya ne."


"A ah fa, kaga sauri muke."


"Yanzun ma saurin zamuyi, tsayawa ma maganar nan bata time ne." Ya fizgota ya jata zuwa toilet din, ba yadda taso dole ta hakura amma tasan shi ba zai tsaya iya wankan BA wallahi, aikuwa be tsaya din ba haka ya dinga shiriritar dasu har su Fauwaz suka iso, jin gidan shiru yasa Fauwaz kiran Ya Tariq din a waya daga toilet din suka ji kiran, da sauri suka karasa suka fito ya dauki wayar ya kirashi


"Muna shiryawa ne gamu nn fitowa."


Ajiye wayar yayi suka shirya a tare a gaggauce sannan suka fito yayi falo ita kuma ta koma bedroom dinta ta dan karasa abinda zata karasa sannan ta fito.


   Tea kawai suka sha shima a tsaitsaye sai snacks din da ta daukar musu wanda Anty ta basu jiya suka tafi. Ita da Amira da Maryam ne a mota daya sai driver shi kuma da ya Fauwaz suma a tasu motar sai wasu motocin biyu har suka isa airport din. Wani kebantaccen wajen suka nufa masu kula da gate din sukayi saurin bud'e musu, suka fito suka shiga cikin building din dake dauke da wani falo a farko sai wani wajn me dauke da round table da kujeru. Falon suka shiga suka zauna suna zama sai ga su Baba nan sun shigo shi da wasu manyan mutane su. Mikewa su Jiddan sukayi bayan sun gaishe su suka koma dayan wajen me round table din suka zauna achan.

   Suna zaune suna hira kad'an kad'an ya Fauwaz ya shigo yace su taso, jikin ta ne yayi sanyi ta rike hannun Amira suka fito daga wajen, wata hanya suka bi zuwa filin jirgin ba wadda sauran mutane suke bi ba, daga dan baya duk suka tsaya Baba ya dafa kan Jiddan bayan ta durkusa a gaban sa ya saka mata albarka sannan ya mikawa Tariq din hannu suka gaisa yana dan russunawa. Hugging din Fauwaz yayi a karo na farko sannan ya dagawa su Amira da Maryam hannu da suke hawayen rabuwa da Jiddan. Ita kanta hawayen take ta daga musu hannu sannan suka juya suka soma tafiya a jere zuwa wajen jirgin. Sai da suka kai wajen matattakalar sannan suka juyo suka sake daga musu hannu sannan suka haura ciki. 


"Allah ya tsare ya kiyaye." Baba yace yana murmushi


"Uwata kuka kike? Da an kwana biyu fa zaku kai musu ziyara."


Yace yana son kwantar musu da hankali. Murmushi sukayi dukka sannan sukayi wa Baban sallama dan daga nan gombe sukayi zasu duba wani aiki.


 Harabar wajen na cike da mutanen da suka yo wa su Baban rakiya, saukin ta motar tasu tinted ce sai kawai suka hade a mota daya sauran motocin suka bi su a baya suka sulalle daga wajen.


***Personal welcoming suka samu a cikin jirgin kasancewar a first class zasuyi tafiyar me full suite dake hade da private bathroom daga nan akayi musu introducing flight attendant din idan suna da bukatar wani abu. Kujerar su irin wanda ke dauke da pod ne da zaka iya converting dinsa zuwa flat bed hade da fluffy duvets. Gefe kuma amenity kit ne da pyjamas sai slippers. 

  Tafiyar almost 13hours ce zuwa Toronto, kanta na saman kafadar sa cikin yanayin gajiya da kosawa saboda bata taba irin wannan doguwar tafiyar ba, an kawo musu menu sun zaba abinda zasu ci amma bata wani iya ci sosai ba sai juice kawai da sandwich. Gyara musu kujerar yayi suka mike sosai ya lullube su da duvet yana sakata jikin sa sosai. Bacci take ji duk da tana tsoro amma kuma kasancewar tare dashi ne sai taji ta sake sosai har ta soma baccin a jikin sa. Ta jima sosai tana baccin kafin ta farka daidai kusan lokacin da saura kad'an su isa.  Gyara mata gefen idon ta yayi da hannun sa ya taimaka mata ta tashi zaune sosai shima ya zauna yana mika mata ruwa tasha kad'an ta maida kanta jikinsa tayi lamo. Bayan wasu mintuna da tashin ta akayi sanarwa isowar su da kuma shirin saukar su. Yanayin fuskar ta ne ya sauya ta nuna farin ciki dan batayi tunanin tayi dogon bacci irin haka ba, ta zata sai ta kara wani zaman sannan zasu iso dan tayi matukar gajiya dan ba akwai comportability a tafiyar amma duk da haka ta jigata sosai amma shi ko kad'an be nuna gajiya ba saboda ba yau ya fara ba. 

  

   

***Wani irin mugun sanyi taji sanda suka fito waje, dunkulewa tayi tana sake tura hannun ta cikin katotuwar rigar sanyin da ya saka mata. Kafadarta ya kama ya rik'e ta sosai a jikin sa zuwa motar da zasu shiga daga train station din zuwa gida bayan sun bar airport din train suka hau zuwa garin su sannan suka iso. Ko kad'an bata wani ganin gaban ta lafewa tayi kawai a jikin sa sanyin na cigaba da ratsa ta.

   Tafiya kad'an suka isa gidan nasu da yake a sama, hannun ta duk ya kankare duk da handsocks din da ta saka har guda biyu, shi ya rike mata jakar hannun ta, da sauran kayan nasu, suna kokarin shiga lift Ishaq ya cimmasu shi da Yasmin da suke ta sauri. Wani kallo Yasmin din tayi ma Jidda itama ta dan kalleta kadan kafin ta yi gaba kawai suka shiga cikin lift din dukka. Ishaq ne ya tayashi da kayan.


"Welcome back Captain" Yasmin tace tana kallon fuskar sa


"Thank you." Yace a gajarce, ya mika wa Tariq hannu alamar ya bashi card din kofar, mika masa yayi yace


"Idan kun huta zamu dawo mu gaida Anty amarya."


Banza Tariq yayi masa dan ba karamin kular dashi yayi ba, akan me zai taho da Yasmin bayan yasan baya so kuma yasan hakan zai yi hurting din Jidda? Tura kofar yayi ya matsa mata ta shiga ciki sannan yatura kayan nasu yana tare kofar ganin kamar Yasmin din neman shiga take yi


"Yasmin muje mu barsu su huta."


"Ok." 


Tace tana kada kanta ta juya cike da tunanin wacece suka zo da Tariq din nata tunda ko da wasa Ishaq be gaya mata yayi aure ba. 


Suna shiga Jidda tayi saurin hayewa saman gadon ta ja katoton bargo ta lullube har saman kanta saboda yadda take jin kamar ta kankare. Ajiye kayan hannun sa yayi ya karo karfin room heater din nan da nan dakin ya dau dumi sosai a hankali a hankali taji sanyin na barin ta. Zama yayi a gefen ta yasa hannu ya bud'e mata fuskar ta suka kalli juna


"Are you feeling better?" Yace yana taba saman forehead dinta


"Yes I'm ok, wai sanyi kaman mutum zaiyi freezing?"


Dariya yasa


"Haka suke kuma kinzo a lokacin sanyin ne shiyasa, amma zaki saba."


"A hakan? Ba zan iya sabawa ba."


"Zaki saba, baki ga su Ishaq ba? Kamar ma ba sanyin ake ba."


"Matar sa ce dayar?" Ta tambaye shi tana kallon fuskar sa


"Itace Yasmin!" 


 Yace yana dago kanta ya dora a saman cinyar sa, shiru tayi tana hango haduwar Yasmin din da mugun wayewar ta. kamshin turaren ta har yanzu yana mata yawo a hanci kana ji kasan irin designer perfumes din nan ne masu shegen tsada da kamshi.


"Don't worry zan yima Ishaq magana akai, I don't want any problem."


Bata ce komai ba, tana jinshi yana zare mata scalf din kanta, sannan ya janye kan nata ya dora a saman pillow ya mike ya wuce toilet yaje ya hada ruwa me zafi a cikin tub yazo ya mikar da ita


"Muje ki rage gajiyar nan."


Tashi tayi ya ja hannun ta zuwa toilet din duk tayi sanyi sosai, shi da kansa ya cire mata kayan jikin ta ya bar mata na cikin kawai dan baya so ya kara mata wata gajiyar akan wadda take ciki. Fitowa yayi ya barta a ciki tayi wankan ta fito ta shafa mai ya taimaka mata ta saka kaya masu dumi sosai sannan ya shiga toilet din shima yayi wankan hade da alwala yazo sukayi sallah daidai lokacin da order din da yayi ta iso ya fita ya karbo ya kawo musu suka ci abincin. 

  Bacci kawai take so tayi dan idon ta har lumshewa yake tana gama cin abincin taje tayi brush tazo ta kwanta ya dan kalleta yana Jona system dinsa dan yana saka sim din sa har ya samu kira amma be daga ba sai ya jona system din ya zauna yana dubawa abubuwan da suka turo masa wanda zai fara gobe as early as 8am. 

   Cikin bacci taji ana gyara mata kwanciyar ta, ta dan bud'e ido kad'an ya rungume ta yana rufa musu blanket din dukka jikinsu.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links