SANADIN LABARINA 58


     Page (58)


***Tun da suka dawo Tariq ya daina zama saboda shirye-shiryen tafiya dan a cikin satin zasu tafi saura be fi kwana uku ba, gashi da shirin tafiyar sa shi kadai yayi da intention din idan yaje zai zo da wuri amma yanzu yasan idan suka shilla suka tafi shikenan kuma sai dai idan haihuwa Jiddan zatayi su zo gida duk da be riga yasan yanayin commitment din da zai shiga achan din ba amma yasan aikin su yana cin time sosai.

   Maryam da Amira sun zo gidan sau biyu suna wuni duk sanda suka zo tare da sakon gaisuwar Mama suke zuwa duk da jin su kawai take amma kuma hakan na mata dadi matuka, bata san halin da ake ciki tsakanin Baba da Maman ba dan yayi fushi sosai akan Maman shine take neman hanyar da zata samu ya sakko kuma a kasan ranta tana jin nutsuwa idan ta tuna Jiddan ce matar Tariq dinta ba irin Salma ba. Akan case dinta dasu Anty Nafin sai da taje Kano tayi mata tatas hakan ya jawo suka dauke kafa ma daga zuwa gidan Hajiya Babban gaba daya dan sosai Anty Nafin ta kullaci abinda Maman tayi mata.

  Ana gobe zasu tafi Anty tazo ita da Usman, kamar Jidda ta zuba ruwa a k'asa tasha saboda murnar ganin Antyn. Dama lokacin tana karasa hada kayan ta waje daya ne sai ga Antyn aikuwa ta tayata suka karasa tare suna aikin tana shigar da sakon da take son nunawa Jiddan cikin hikima da yadda zata kula da mijin ta, ta sake samun fada a wajen sa. Jiddan naji duk tana daukewa dan dama Antyn ce mirror dinta ita take dubawa a abubuwa da yawa saboda tasan babu abinda ya zaunar da Antyn a gidan har ta kawo yanzu sai hakuri da iya zama amma ba dan haka ba da tuni ba wannan labarin ake ba. 

  Ya Tariq ne ya kirata bayan yaji komai lafiya sai take fada masa Antyn tazo shineyace kawai ta bita su tafi tare idan ta tashi tafiya saboda su yiwa Baba, Yaya da Mama sallama dan fitar asubah zasuyi gobe daga nan shima idan ya gama gidan zai wuce sai su dawo tare. Toh tace ta ajiye wayar ta fadawa Antyn abinda yace. 


"Hakan yayi." Tace. 


"Tunda tare zamu tafi ai sai mu hau shiri, komai ya riga ya shiga jaka sannan wadannan abubuwan da na nuna miki su karki wasa dasu wallahi."


"In sha Allah ba zan ba Anty."


"Yawwa, Allah dai ya kaiku lafiya, idan mun koma kika je part din Maman Fauwaz ki zauna sosai kinji? Karki ce zaki taso daga zuwa."


"Sau biyu da su amira suka zo sai suce wai Mama tana gaishe ni."


"Kai haba? Da gaske ko wasa?"


"Allah haka suka ce, na karshen ma Amira tace wai Mama tace mu fadi me muke bukata na tafiyar, shine sai yace tace mata zai zo gidan dan dama yana nan."


"Toh Allah yasa addu'ar mu ce taci ta, hakan ai kinga yafi, a kalla zamu fi samun kwanciyar hankali, kuma kinsan Allah? Maman Fauwaz bata da damuwa ita dai barta da kishi da duk mace kuma tana dashi sai dai kowa da irin yadda yake bayyana nasa, amma ko bayan wannan ba ruwanta da rayuwar ka, ko a sanda nake mata aiki bata da irin takurar nan magana ma bata cika son yi ba shiyasa ake mata kallon mara kirki, amma kishi ne kawai ya sakata yin duk abinda take amma sam babu cutarwa."


"Haka ne gaskiya."


"Allah ya kyauta yasa sakkowar tata kenan tunda dai yanzu ta zame miki dole tunda kika auri dan ta, ba'a kuma san karshen zaman da kuma yayan da za'a haifa ba."


"Ni ba zan haihu ba Anty."


"Saboda me?" Tace da sauri


"Tsoro nake ji fa."


"Kin jiki, ai sakin jiki zakiyi ki haifo mana babies Masha Allah, yadda bamu da yawan nan kinga ai ma kara yawa a daina mana gori."


"Kai Anty."


"Allah gori mana,ni da Yaya duk haihuwar daya ce kuma dama kinga mu biyu ne, dangi da yawa na da dadi wallahi sai baka dasu zaka gane, kuma dai haihuwar ce ke sawa a yi yawan."


"Tou haka ne."


"Tashi kinga kar lokaci ya kara ja mu tafi."


"Toh."


 Ta mike taje ta dauko Hijab dinta ta saka suka fito, Sam na zaune suna ta hira da su Faisal sai ya taso da yaga sun fito yazo suka tafi.

  Bata shiga wajen Antyn ba direct wajen Yaya ta wuce daga nan sai ta je ta gaida maman ta zauna kamar yadda Anty tace.

   Dambu nama Yaya take ci da lemo Jiddan ta shigo, ta zata Fauwaz ne har da saurin ta zata boye Jiddan ta ganta.


"Auw ashe ba al'murin chan bane nake saurin boyewa."


"Rowa dai Yaya,."


"Allah ba rowa ba, in dai yagani sai ya dumbuza nan da nan sai kiga ya kare."


"Ai Yaya ke da Ya Fauwaz kamar Tom and Jerry kuke,ina wuni?"


"Lafiya lou, bismillah ci kad'an."


"A ah Yaya, nagode tsautsayi yasa naci ki zo kina yin mafarki na."


"Kin wa kanki yarinya." 


Ta rufe robar ta tura shi gefen kujera tana karkade hannun ta


"Babar ku ce tayi min da kanta, naga kwana biyu shiri take nema da kowa a gidan nan, inaga dai tasu ce ta hado shi da Baban naku."


"Kai Yaya, saboda haka aka yi miki dambun?"


"Allah kuwa ai ina lura da komai, ina kuma shan kallo na..."


"Kuma tunda dai ina cin riba sai su karata chan." Ta dora


"Hajiya Yaya kenan."


"Uhum, ya akayi da magana ne?"


"A ah babu, zuwa nayi na ganki kuma mu tafi tare ki kwana mu raba dare muna hirar bankwana."


"Allah ya tsareni da zuwa gidan ku wallahi, Allah ya kiyaye ya kaiku lafiya."


"Yanzu ba zaki zo muje ki kwana ba?"


"Ba zani ba wallahi, kar kuma ki ishen da iyayi bayan ba har zuciyarki kike maganar tafiyar ba."


"Allah Yaya har zuciya ta nake yi."


"Toh naji, zuwa ne ba zan ba,ehe."


"Toh shikenan Yaya, amma zaki rakamu airport din ko?"


"Ko gaban gate din gidan nan ba zan rakaku ba bari kiji, salon a hada baki dake a sani a jirgin haka kurum."


"Kai Yaya ana tafiya ne ba visa ba komai?"


"Oho na sani?"


"Toh kuma ai naji zaku je Umrah wannan azumin sannan kuje hajji da babbar sallah, yanzu ya za'a yi kenan?"


"A mota zamu ko a jaki." 


Tace tana gimtse fuska, dariya sosai Jidda tayi har da rike ciki. Tsinken sakace Yaya ta dauka tana sakacen tana hararar Jiddan da take mata dariya


"Jakin ne ya ban dariya Yaya, afuwan!"


"Kece da kayan haushi ai."


"Nayi shiru toh, kinga kar muyi fada tunda dai tafiya zan."


"Ba zamuyi ba ai, ya kike fama da dan dunkum din mijin ki kuwa?"


"Kai Yaya."


"Yo Allah ai sai hakuri irin su."


"Na yanzu ba haka suke ba fa Yaya."


"Toh ya suke? Ban labari."


"A ah, kawai dai suna da kirki da dadin zama in dai ka iya zama dasu."


"Ni rashin iya zama da su ne yasa nasha wuya wajen Malam kenan kike so kice."


"Ni? Bance ba Yaya, a bar maganar toh."


"A barta, dan ni ko Qurani za'a dafa ace min masu irin halin Malam na da dadin zama ba lallai na yarda ba, karshen magana kenan."


"Hahaha, karshen magana kenan kuwa Yaya."


"Ah toh "


"Bari na je na gaida Mama toh, zamu dawo muci dambun naman ni da su Amira."


"Wallahi kika gayyato min su tamu ce ni dake."


"Dan kad'an zaki sammana." Tace tana ficewa


"Karfa ki fara na gaya miki." Ta daga murya, sai kuma ta mike ta dauke robar ta shiga da ita daki ta bud'e cikin kayan ta, ta tura a ciki ta rufe har da saka key sannan ta dawo falon tana sababi.


    Mama ce kadai a falon da ta shiga, tana zaune cikin ado amma kuma fuskar ta, ta nuna tana dan cikin damuwa, kallon Jiddan tayi sanda ta shigo duk sai taji kunya kafarta ta hau harhadewa ta samu ta karaso ta zube a k'asan carpet cikin tsananin girmanawa ta gaida Maman 


"Lafiya lou, kuna lafiya?" Ta dora akan amsar gaisuwa


"Lafiya kalou alhamdulillah." 


 Jiddan ta amsa cike da mamaki doguwar amsar lafiya lou din da Maman ta baya hade da tambayar lafiyar su bayan a dah lafiya kawai take cewa shima a gajarce tana kin kallon Jiddan 


"Goben da karfe nawa zaku tafi?"


"Da asubah yace." 


Gid'a kai tayi


"Ga kayan ku chan da yace kuna bukata idan kun tashi sai ku tafi dasu."


"Ok tam, mun gode Allah ya saka da Alkhairi."


"Amin."


Shiru ya biyo baya kan Jidda na kasa baki daya falon yayi mata wani irin mugun girma sanyin AC yasa ta sake shiga wani irin yanayi


"Akwai wani abun kuma da kuke bukata?"


"A ah babu."


"Ok! Ki shiga wajen su Amira suna ciki."


"Toh." Ta mike ta wuce ciki Maman ta bita da kallo tana son sake gasgata Jiddan a matsayin matar Tariq din ta.

    A dakin su Amira ta dade suka sha shafta anan taji labarin soyayyar Maryam da Ya Isma'il tayi mamaki sosai ko daya Ya Tariq din be fada mata ba, har Isma'il din ma yazo jiya ya tafi yanzu magabatan sa zai turo sai Ya Fauwaz ma da yake so aje ayi masa tambaya. Suna kyautata zaton kuma Baba dukkan su zai hada har Amira tunda duk dama tsiran su a haihuwa ba yawa sosai Tariq ne dama tsakanin su dukka da tazara me dan yawa sai kuma Ya Fauwaz din ma hakan ne amma su matan a kusa kusa duk Mama tayi haihuwar shiyasa suka taso kusan kai tsaya gaba dayan su.

    A waya Mama ta kira Amira tace ta turo Jiddan, ta tashi da sauri ta zura Hijab dinta suka dinga mata dariya wai taji kiran suruka ta rikice, tana shigowa falon ta hango shi a zaune yayi crossing kafarsa yana shan abu a cikin mug, kallon k'asa k'asa yayi mata ta, ta yi saurin sadda kanta k'asa ta karasa ta zauna daga gefen Maman a k'asa tace 


"Gani Mama."


"Wai tafiya zakuyi, kunce babu wani abu da kuke bukata ko?"


"Babu komai Mama, addu'ar ki kawai muke bukata nothing more."


"Toh Allah ya kiyaye ya tsare."


"Amin ya Allah."


 Suka hada baki duk da Jiddan a ciki ciki tayi nata amsawar amma ba karamin dadi addu'ar tayi mata ba.


"Ku tashi kuje wajen Babanku."


Mikewa yayi rik'e da cup din ita kuma ta dan russuna tace


"Mun gode Mama."


"Allah ya bada sa'a." 



 ***Jerawa sukayi har part din Baban suka same shi yana waya, Tariq din ne ya fara shiga kafin yace ta shigo, Anty na dakin sa taji shigowar su ta fito lokacin Baba ya ajiye wayar yana duban su 


"Mutanen turai." Murmushi sukayi dukka har Anty, Tariq yace


"Baba barka da warhaka."


"Barka dai ango."  Ya sake zolayar Tariq din


"Baba ina wuni?" Ta gaishe shi a nutse 


"Lafiya lou 'yata, kuna lafiya?."


"Lafiya lou."


"Toh madallah, sai tafiya ko?"


"Eh."


"Toh Allah ya kaiku lafiya ya bada sa'ar abinda aka je nema."


"Amin Amin.," Anty tace


"Sai a kula sosai, rayuwa irin wannan dole sai kun hada kanku kun yi kuma hakuri da juna "


"In sha Allah Baba."


"Ka rike amana, bana so naji ko na gani dan Allah. Hauwa'u amana ce a wajen ka "


"In sha Allah."


"Yawwa, ke kuma ki rike mijinki da kyau kiyi masa biyayya iyakar iyawar ki, Allah yayi muku albarka baki daya ya kade fitina."


"Amin." 


Fitowa sukayi ita ta wuce part din Anty shi kuma yaje yiwa Yaya sallama, daga nan yace ta fito suka je gidan Umaima suka mata sallama sannan suka je gidan Safiyya, anan ne kawai taga ya dan sake har ya zauna ma sun dan taba hira da mijin nata kafin suyi musu sallama suma su wuce gida.


#Ranooooo


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links