SANADIN LABARINA 38


  Page (38)



***Bayan la'asar suka dawo, yana shiga gida ya dauki motar sa ko ciki be shiga ba dan yasan Maman ma tana cikin mutane ya wuce nasa gidan, baki daya wunin ranar tunanin ta yayi tayi, shiyasa suna sauka yayi gidan ya huta gaba daya a chan duk da anjima dole ya dawo gidan nasu kafin a tafi kai yaran.

   Horn yayi aka bud'e masa ya shiga da motar ya samu gefe yayi parking sannan ya fito, hannun sa rataye da babbar rigar da bata fi awa daya a jikin sa ba ya cire ta dan duk a takure yake. Key din ya mikawa faisal ya haura, ya murd'a kofar yaji ta a rufe sai yayi knocking. Idar da sallar ta kenan dan bacci tayi tun da tayi azahar ta kwanta sai lokacin ta tashi, tayi sallar tana zaune jigum tana tunanin yanzu su Amira suna chan ana shan shagali ban da ita, da tuni tana part din Yaya ana ta harka. Knocking din ya sake yi ta tashi daga wajen da take ta nufi kofar ta bud'e ta, yana tsaye hannun sa rike da wayar ta da tashi sai babbar rigar dake sakale da dayan hannun, matsawa tayi ta bashi hanyar ya shiga ciki ta rufe kofar ta juyo ciki. Har ya zauna a kujera ya ajiye wayoyin a gefen sa, ya cire hular kansa yana dan kishingid'a saboda yadda yake jin gajiya. Bata ce masa komai ba, ta wuce kitchen ta dauko ruwa da cup ta kawo masa sannan ta mike ta shige ciki, ruwan ya dauka yasha ya dauki remote ya kunne TV ya mike kafarsa sosai sannan ya karo AC falon.

   Dakin taje ta zauna kurum tayi shiru tana tunanin me ya kamata tayi,shima kuma kamar wanda aka kullewa baki be ce mata komai ba, sai duk taji babu dadi dan ta dauka zai yi mata magana tunda dai shi ya ajiye ta. Ta dan dade a zaune sai kawai ta tashi tace bari ta watsa ruwa duk da tayi da suka fita da Amira, amma kuma baccin da tayi taji tana bukatar ta watsa ruwan dan duk zuciyar ta a jagule haka ta tashi.

   Tana shiga wankan ya shigo dakin, ya zauna a gefen gadon rike da wayar ta da ya kawo mata, motsin ruwa yaji a toilet ya gane tana ciki, maimakon ya fita sai yayi zaman sa idanun sa na kan kofar toilet din yana danna wayar sa. Sam bata ji shigowar sa ba, shiyasa ta fito kai tsaye daga toilet din daure da towel din da yayi amfani dashi dazu, kanta a rufe da karamin towel saboda kar ruwa ya taba. 

   Sai da tazo kusan rabin dakin sannan ta ankare dashi, tayi diri-diri duk ta diririce kamar zata koma sai kuma taga shima komawar da kunya, tsayawa tayi chak kawai a wajen da take ta sunkuyar da kanta k'asa


"Ga wayarki."


 Yace yana daga mata ita sama idon shi na kan ta


"Zan dauka." Tace tana jan towel din a kokarin ganin ta sake rufe jikin ta sosai


"Zo ki karba, ko na koma da ita."


"Ni ba amfani zan da ita ba."


"Ba wani, Aunty ta kira ki, sannan Amira tayi miki text wai zasu zo, na kirata nace bana neman su."


"Toh ka fita idan na saka kayan zan fito sai na karba."


"Ba in da zani."


 Yace yana gyara zaman sa, motsawa tayi daga in da take tsaye a hankali har ta isa wajen wardrobe dinta, ta zaro Hijab zata saka ya mike ya iso ya rike Hijab din yana mata kallon cikin ido


"What are you try to hide?" 


Shiru tayi dan yadda ya matso so close da ita, ya hana ta motsawa yana kuma yi mata kallon k'asa-k'asa.


"I'm asking you, me kike boye wa, show me."


"Dan... Allah... Kayi hakuri.". 


Ta fada a rarrabe ganin ya rike jikin towel din, murmushi yayi yana cije saman lips dinsa, ganin yadda duk ta firgice ta shiga tashin hankali.


"Kema wai kin girma ko?"


"Dan Allah ni dai kayi hakuri."


"I can't, haram ne?"


"Eh." Tace da sauri ba tare da tasan ma ta fada ba. Kallon ta yayi da sauri still yana rike da gefen towel.din itama ta rike kakam 


"Ta ya akayi ya zama haram?" 


Ya kai hannun sa saman kanta ya cire towel din da ta daura ta rufe gashin


"Wow." Yace yana ya saka hannu ya shafa gashin


"Ta ya akayi ya zama haram? Fada min."


"Sanyi nake ji, ka tsaya nasa kaya na, dan Allah."


"Ok, ok.. Saka toh." Ya cika towel din ya jingina da jikin mirror yana folding hannayen sa


"Kaje waje."


"Ba in da zani, idan zaki sa kisa idan kuma sai na taimaka miki fine, I will be glad to help."


"Na shiga uku."


"Da saura ma yarinya." Ya kad'a kai yana murmushi. Doguwar riga ta dauko ta dora ta akan towel din sannan ta zare towel din ta kasa, ta saka Hijab din akai. Dariya ta bashi yadda take ta sauri ta gama ta kai towel din ciki ta sakashi a washing machine, sannan ta fito


"Kin manta baki saka abinda na gani a cikin wardrobe dinki ba, da twin dinsa."


"Bra and pant." Ta fada a zuciyar ta, 


Da sauri ta fice daga dakin dan ta gano Ya Tariq so yake sai ya hanata sakat a gidan. Dariya ya saka, ya mike daga jinginar da yayi yabi bayan ta, ya sameta a kitchen kamar be neman abu. Hannun sa zube a cikin aljihun sa ya tsaya a kofar kitchen din yace 


"Kije ki shirya sosai, ki sameni a mota."


"Gida zamu?"


"Oho, don't waste my time."


Da sauri ta koma dakin, ta dauki underwears din ta koma toilet ta saka sannan ta saka riga da skirt sakakku ta dora veil akanta me dan kauri dan bata so yace mata lallai sai ta saka Hijab. Flat shoe ne a kafarta duk da bata da tsawo chan amma shine raayinta, shi ta saka ma yanzu ta fito ta same shi a zaune a mota yana amsa waya ta cikin kunnen sa dake sakale da Bluetooth. Tana zama ya dora mata wayarta akan cinyar ta, ta dauka ta jujjuya ta, sannan ta kunna ta hau whatspp dan ganin me yake faruwa.

    Wayar yake tayi idanun sa na kan titin ko sau daya be juyo ya kalle ta ba, har suka karasa gida, da murnar ta,ta kalle shi shima a daidai lokacin ya juyo bayan ya gama wayar wadda da dukka alamu akan aikin sa ne.


"Ki ajiye wayarki kusa dake, zan kiraki." Yace bayan ya samu waje yayi parking zata fita, gid'a masa kai tayi ta fita daga motar yana kallon ta, sai da taga ta fita sannan ta kalle shi


"Ba zan koma ba." 


Sai tayi gaba da sauri ta shige part dinsu, dariya ta bashi ma, ya kada kansa yana hasaso yadda zai ciccibeta idan har tace zata masa gardama. Fita ya sake yi daga gidan dan zuwa ya samu Baba a chan guess house dinsa.


   Babu kowa a part din nasu sai masu aiki duk suna chan bayan gidan in da ake taron bikin kafin azo kai amaren gidajen su, Amira ta kira a waya tace ta kawo mata kayanta, sai gata ita da Nu'ayma, ta saka suka fita Amira na tsokanar ta.

   Aunty ce ta hango su da suka taho wajen, ta kalli chan in da Maman take taga tana wani abun bata lura da Jiddan ba, tashi tayi ta riga su isa ta kama hannun Jiddan tace musu tana zuwa. Chan wajen da ba mutane suka je Jiddan ta gaishe ta, ta amsa cike da murnar ganin ta


"Ashe da gaske yake da yace zai kawo ki."


"Kece kika ce ya kawo ni?"


"Eh nice, sannan Baban ku ma yana son hadaku gaba daya yayi muku magana har Maman Fauwaz, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki, duk abinda zai je ya dawo ki rike mijinki kinji? Karki ji tsoron kowa."


"Aunty menene? Akwai matsala ne?"


"Babu ko daya, nasan ba lallai ta amince da tarayyarku ba, musamman yanzu da duk muka gane Tariq yana son ki, zatayi kokarin baki matsala dole sai kin jajirce sannan ki hada da addu'a,."


"Wallahi ni Aunty tsoro nake ji."


"Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki."


"In sha Allah, nagode."


"Muje ciki, kije ki gaishe su ki dake kuma, mahaifiyar mijinki ce ta zama dolen ki."


"Toh." Tace a sanyaye, suka koma ciki Mama ta hango su, ta gimtse fuska sai taga Jiddan na tahowa in da suke a zaune da manyan kawayen ta harda matar gwamnan adamawa da matan manyan koshoshin kasar 


"Jidda." Aunty Mimi ta tare ta tana kusa da in su Maman suke dan suna jin su ma


"Laaa, ina wuni?" 


"Lafiya Lou, ban ganki ba gaba daya a kwana biyun nan, har Amira na tambaya tace kina nan."


Murmushi tayi bata ce komai ba,


"Karasa wajen su Maman ki gaishe su."


"Toh." Tace tana matsawa wajen su, ta russuna har k'asa ta gaida su, suka amsa a sake banda Mama da ta juyar da kanta gefe tana magana.


"Matar Tariq ce, shine babba a yaran Mama." Aunty Mimi tace musu tana murmushi


"Ah Hajiya Aisha har suruka ce dake amma bamu sani ba? Gata nan Masha Allah wallahi."


"Kun sani yanzu ai." 


Tace tana dariyar yak'e, gefe kuma kamar ta jawo Aunty Mimi da Jiddan ta hada tayi musu shegen duka haka taji, tashi Jiddan tayi ta koma chan wajen su Amira, kafin daga bisani ta fice daga wajen ta tafi dubo Hajiya Yaya.


   Da murnar ta,ta shiga kamar wadda ta dade bata ga Yayan ba haka taji, itama Yaya na ganin ta, ta dire abinda yake hannun ta


"Wa nake gani kamar matar malam nabahani."


"Kai Yaya?" Ta kwashe da dariya


"Toh Badamasi." 


"A ah Yaya, ba ruwana wallahi."


"Ah gaskiya, kya tarewa miji wai ke dadi miji daga kwana daya har ya hure miki kunne ko?"


"Kai Yaya!"


"Allah kuwa, kin yi luf dake a dakin miji, yar kumama an san dadin aure."


"Na shiga uku, Yaya daga zuwa na?"


"Zuwan kenan?" Tace tana dariya


"Eh Yaya."


"Ai da naji shiru nace munafukan yara kaji su luf kamar basa duniyar nan.".


"Tsokanar mu dai kawai kike Yaya."


"Yo Allah ,shima munafukin yana fuffukar baya so baya so ashe duk munafurci ne."


"Me zan samu ne Yaya? Yunwa nake ji."


"Na shiga uku ni Hajara, ba dai horon yunwa yaron nan yayi miki ba, kai ni sai naga ma daga jiya zuwa yau kin fada sai uban fari da kika kara, gaya min gaskiya me yayi miki?"


"Innalillahi, Yaya ba komai fa, kawai dai abincin gida nake son ci, shiyasa, amma a kwana daya Yaya sai mutum ya chanja? Jiya ma fa muna tare."


"Toh ai abun nasa ne, kinsan kan sa da motsi har yanzu, sai kin yi hakuri dai."


"Hajiya Yaya kenan."


"Iya gaskiya ta na fada miki, tashi ki duba kitchen akwai flasks din abincin da Babar taku ta aiko, sai ki zuba ki cika cikin ki."


"Yawwa yanzu naji batu." 


Ta mike ta shiga kitchen din ta zubo fried rice da chicken tazo ta zauna tana ci a hankali suna hira da Yaya.

    Har magriba tana wajen Yayan sannan su Amira suka shigo suke cewa Baba ya dawo ya saka a kira masa Ya Safiyya da Umaima part din sa, dan yi musu final nasiha tunda har masu zuwa daukar amaren sun fara zuwa. Kira ne ya shigo wayarta, ta kalli screen din taga an rubuta Capt.T, kai tsaye ta gane shine, ta daga a kasalance ta saka a kunnenta


"Ina kofar part din Baba."


"Na'am?"


"Kizo."


"Ok."


"Ba zai shigo nan din ba? Ko da yake ina yaga idon da zai hada dani? Ai be isa ba."


"Hajiya Yaya ta Ya Tariq." Amira tace tana dariya


"Na Jidda dai, wace ni?"


"Ai kece ta karfen."


"Jeki dai dadi miji, daga kira har kin mike jiki na rawa, ba dan jan ajin nan, ko ni da nake ba yar zamani ba na iya jan ajin nan tun zamanin kakanku, shima yasan Dije ba ta wasa bace, shiyasa ya kasa yi min kishiya."


"Yo ai ke Yaya surutun ki kadai sai ya kori kishiya."


Amira tace tana dariya, ita dai jidda fita tayi ta bar su suna gamzawa, ta hange shi tsaye a kofar part din Baban tsaye shi da kaamar Mama, suna magana amma idonsa na kan ta tunda ta nufo su, a tsorace take dan bata yi zaton zai kirata Mama na wajen ba, bata san me zata tarar ba, shiyasa ta dinga jan kafar ta, har ta isa wajen kanta a k'asa tayi sallama, shi kadai ya amsa ta kalli Maman wadda fuskar ta, take a matukar hade kana gani kasan ranta ya kai kololuwa a baci, bud'e kofar tayi ta shige, ya girgiza kai kawai yana kallo na, fuskar sa babu yabo babu fallasa amma ya nuna kamar ransa babu dadi.


"Muje." Yace yana nuna mata hanya, a tunanin ta part din Baban zasu shiga, amma sai taga ya nuna mata hanyar wajen da akayi parking motar, jiki a sanyaye tabi bayan sa, ya bud'e mata bayan motar ta shiga sannan shima ya shiga, sam yazo ya shiga wajen driver ya tada motar suka bar gidan.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links