SANADIN LABARINA 37


  Page (37)


***A hanya Baba ya sake kiran sa, yace masa gashi nan ya taho, ya katse kiran sai ya kira Fauwaz, yana tare da Maama lokacin tana masa magaanar daurin auren da kuma abinda take so yayi mata saboda bakin ta, manyan bakin da zasu zo gidan. Daga wayar Tariq din yayi dan dama yana so ya kirashi sai kuma wani abun ya dauke masa hankali, 


"Kana ina?" Yace yana dagawa


"Wajen Mama, ka zo ne?"


"No yanzu dai zan shigo gidan, bari na karaso."


"Ok." Ya katse wayar 


"Tariq ne?"


"Eh shine."


"Daga ina zaizo? Dama ba a gidan ya kwana ba?"


"Eh toh ban dai sani ba, amma inaga a gidan sa ya kwana."


"Oh okh, kace ina jiran sa fa."


"Ok ma, bari na je na karasa shiryawa dan Baba yace baya so bakwai tayi bamu tafi ba."


"Ok, shikenan."


Juyawa yayi ita kuma ta wuce kitchen taga abinda ake yi, duk da komai da za'a ci a bikin order akayi amma kuma akwai aikin da ake mata a kitchen shi zata je ta duba. Murmushi Fauwaz yayi bayan ya baro wajen Maman, dan yasan bata san Tariq ya aikata tsiyar ba, kuma yasan idan ta sani akwai matsala sosai, su dai yan kallo ne, gefe zasu koma suka yadda zata kaya. Kallon gate din da aka bude yayi, Tariq din ne, ya shigo ya samu gefe yayi parking Fauwaz din ya karasa wajen motar  ya bud'e masa kofar, ya zuro kafarsa bayan ya fito rike da kayan sa, ya mikawa Fauwaz din.


"Ajiye min a ciki ina zuwa, zan ga Baba."


"Ai tun asubah be shigo ba fa, sai dai Mama ita ce take neman ka dama."


Hannu yasa ya karbi kayan yace


"Bari na fara shiryawa toh, samo min plain tea nayi warming ciki na."


"Ok."


***A gurguje ya shirya cikin shigar farar shadda wadda da akayi wa aiki da bakin zare, tea din ya dauka yana sha da hannu daya, dayan hannun kuma yana daidaita hular kansa, kiran sa akayi a waya ya daga da sauri dan yasan Baba ne, sukayi magana ya ajiye cup din ko rabi be sha ba, ya rige babbar rigar a hannun sa bayan ya saka bakin takalmin sau ciki, ya fito da sauri ya nufi bangaren Maman, part din nata a cike yake sai yaji duk ya takura, Amira da tazo zata fita yace tayi wa Maman magana.


"Ta shiga wanka." Tace tana kallon yadda kayan jikin sa sukayi masa kyau


"Ok, kice mata mun wuce."


"Ok sai kun dawo."


Har yayi gaba itama ta wuce sai ya tuna


"Amira."


"Na'am?"


"Anjima driver ya kaiki wajen Jidda."


"Tana ina?"


"Ban sani ba."


"Wallahi Ya bansan ina ba shiyasa na tambaya."


"Gidana toh."


Saurin toshe bakin ta, tayi alamun laaa, sai tayi dariya, hararar ta yayi yana kallon ta, tayi saurin daina dariyar yace 


"Saura kuma ki bud'e bakin nan naki ki fada wa mama, zan yi magana da ita idan na dawo."


"Ba zan ma fada ba wallahi, ni yanzu ma zan tafi sai na dawo anjima kafin lokacin event din yayi."


"Event din me za'a yi?"


"Anan gidan ne zaa yi, itama Jiddan ta sani ai kayan da zata sa ma yana waje na."


"Ba zata zo ba, kije dai ke sai ki dawo anjima din."


"Toh shikenan bari na chanja kayana, zan ce ma Mama na je a sake gyara min gashi sai na tafi chan."


"Gyaran gashi? Aina akayi?"


"Glamorous Saloon ne, duk fa yau zamu je da Jiddan dama."


"Ok kuje tare din, a gyara mata sai ku koma gida."


"Ok tam."


"Kice mata nace ta saka Hijab idan zaku fita."


"Toh Yah." Tace tana gimtse dariyar da take neman taho mata, juyawa yayi da sauri ya bar wajen, ta kwashe da dariya ta buga tsalle.


Kaamar yadda tace masa zata fadawa Maman haka tace mata, ta dauko ATM din ta, ta bata ta fito wajen takwas bayan su Ya Tariq din sun tafi, ta samu Sam tace ya kaita gidan  Tariq. Jidda na kwance a falon bayan ta gama kukan bakin ciki ta hakura gashi bata ga wayar ta ba, bare ta kira ko Aunty ce tasa ta roke shi taji ana knocking, tashi zaune tayi ta tabbatar da knocking din ake ko kunnenta ne sai taji an sake kwankwasawa, wajen kofar taje tace waye? Da sauri ta bud'e jin muryar wadda bata yi zato ba, suka rungume juna suna ihu kamar wadanda suka shekara basu ga juna ba. Zama sukayi a kujerar Amira ta kalli falon


"Haduwa, ashe kina nan."


"Dama zaki zo?"


"Gashi kuwa, Ya Tariq ne yace nazo na kular masa da matar sa."


"Ba wani nan, ni kyale ni kinsan ya ce wai bazan je gida ba, dan Allah haka ya dace?"


"Kinsan fa shi daban yake, wallahi dan zaki sha fama."


"Allah sarki ni."


"Wai yaushe kika taho? Kuma kin taho gaba daya kenan?"


"Oho nima ban sani ba, bansan me suka kulla shi da Aunty da Yaya ba, yazo ya tiso keyata a gaba har kuka sai da nayi wallahi."


"Ai Ya Tariq, sai a barshi wallahi, haka ya hanaki dinner kina ji kina gani."


"Ki daina tuna min dan Allah."


"Toh sorry, tashi zakiyi ki mana wani abu mu dan ci ko breakfast ban yi ba, yace muje a gyara miki gashin kanki."


"Gashi kuma? Ni ai bana retouching."


"Eh ai ba retouching ba, sake dai gyara mishi kayanshi zaa yi."


"Kayan shi?"


"Eh mana, baki sani ba?"


"Ke kika sani, ta yaya gashi na zai zama kayan shi tsakani da Allah kema dai banda neman magana."


"Ah toh na waye dah? Lallai ma ke din nan wallahi."


"Oho ke kika sani, babu komai a gidan nan sai dai kisha tea da cake."


"Anjima ai za'a kawo garar, wai hadda Ya Tariq a garar da Baba yayi."


Ta kwashe da dariya, 


"Ko da yake yace shi yarsa yayi wa ba Ya Tariq ba."


"Allah sarki babanmu, Allah dai ya saka masa da gidan aljanna."


"Amin Amin. Muje ki shirya dan da wuri zan koma kar abubuwan su hade min, amma zan dawo da daddare idan kina so."


"Eh dan Allah ki dawo, wallahi inaso ko kwana ne ma kiyi."


"Wa? Ni? Tabdijam, Ya Tariq din ne zai barni na kwana?"


"Me zai hana?"


"Ba za'a ji mutuwar sarki a baki na ba, jeki shirya dai bari na sha tea din."


"Kyaji da gulmar ki."


Tace tana yin gaba ta shiga kofar da zata kaita dayan falon kafin dakunan nasu. Wanka tayi a gurguje ta ciro riga da skirt ta saka ta dauko veil dinta da handbag ta fito ta samu Amiran ta kunna TV tana kallo tana shan tea din


"Kira min wayata inaga a gida na barta."


"Ok." 


Kitchen ta wuce ta hado tea din tazo ta zauna lokacin da amira ta kira wayar tata,


"An d'aga gashi ." Ta mika mata, karba tayi ta kara wayar a kunne


"Hello aunty?"


"Uncle ne ba Aunty ba." Da sauri ta ciro wayar daga kunnen ta, ta kalli number din, taga dai number ta ce, 


"Waye?" Amira tayi mata alama da hannu


"Dama wayata nake nema shine nace Amira ta kira min ita."


"Oh okh, tazo kenan, kin daina kukan?"


"Umm.."


"Good, akwai wani abu ne?"


"Um um."


"Okh sai mun dawo." A ciki ta amsa ya kashe 


"Wai wa ya daga?"


"Ya T..." Tace tana mika mata wayar ta


"Wai kina nufin da wayar taki ya tafi."


"Gashi nan, ni ban masan yaushe ya dauka ba."


"Lallai Ya Tariq, ai kamar akwai landline a hanyar kitchen din chan, na ganta a saman wani table."


"Ni wayata nake so,."


"Kika sani ko new one za'a kawo miki."


"Ai bance inaso ba."


"Malama ki daina pretending dan Allah, Amira ce fa, your best friend mene wai ban sani ba,ko yanzu kin daina son Ya Tariq din ne ake bashi I don't care attitude."


"Ni da nace miki ina son sa ne?"


"Fadawa wanda be sani ba."


"Tashi mu tafi, kar ya dawo yace ya fasa."


"Kad'an daga aikin babban Yaya."


Ta mike zata yafa mayafi Amira ta tuno da abinda yace mata


"Wallahi na tuna,yace karki yafa mayafi wallahi"


"Na shiga uku, mayafin ma?"


"Wallahi haka yace mun, kuma yana sane sai ya tambaya."


"Gaskiya ni wallahi."


"Haka zaki hakura, dole abi miji dan a zauna lafiya."


"Ke kika sani." Ta



 suka fito, Sam yana zaune tare da gate man yana jiran su, suka shiga motar yaja suka bar gidan. Ita aka fara yiwa sannan akayi Amiran, sai sheki gashin yake da kyalli musamman ita da take da gashi sosai, ita kanta me salon din sai da ta yaba da tsantsi da yalwar gashin ta, duk da bashi da cika sosai tsayin da tsantsin ne gashi baki sosai.


A gate aka ajiyeta Amira tace ba zata shigo ba su Salma suna ta kiran ta, kamar zatayi kuka haka ta shiga gidan tana cike da jin haushin Tariq din. 



Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links