SANADIN LABARINA 36


   Page (36)


***


"Na shiga uku." Tace tana jin kamar k'asa ta bud'e ta shige ciki, 


"Fada min ina so na sai wasu kaya ne."


Turo bakin ta tayi gaba, ta wuce taja kujerar mirror ta zauna, murmushi yayi ganin dabi'ar tace turo bakin,ya kuma san maganin ta, cigaba da duba kayan yayi ya zabi dogayen riguna da kiyasin tsayin ta da nasa amma dan ya sake tabbatar wa sai ya janye system din ya mike ya nufi in da take a zaune ya saka hannu biyu ya mikar da ita, sannan ya karata a jikin sa, yar karama take tashi a duk sanda suka tsaya a tare, saboda shi yana da tsayi sosai.


"Menene tsayin doguwar rigar ki?"


"54." 


Tace tana kauda kai ganin kamar leken wuyan rigarta yake yi wadda take v-shape, duk a takure take 


"Ashe daidai nayi guessing, nasan ba zaki fi hakan ba, little Jiddah."


"Little?"


"Yes." Ya d'age mata gira, 


"Zo kiga wani abu." Yaja hannun ta, ta kalle shi da sauri shima ya kalle ta saboda yadda sukayi wa juna shocking


"Like charges repel, unlike charges attract."


"Na'am?"


"Haka akace a physics."


"I'm not a science student."


"I see, amma zaki iya fadamin?"


"Me?" Tace tana daga kanta ta kalle shi, shiru yayi kamar ba zai magana ba, sai kuma yace bayan ya rike mata hannun kakam 


"Size of your underwears."


"Wayyo Allah na, Dan Allah ka daina."


"I need to know, ina siyan kayan lefe ne."


"Lefe?"


"Yes, ba ana lefe ba idan za'a yi aure ba."


"Aure zakayi?" Ta samu kanta da tambayar sa, gid'a mata kai yayi


"Aure zan, shiyasa zan hada lefe kuma ke zaki tayani zaba."


"I can't." Ta janye hannun ta fuskar ta na chanjawa nan da nan, kallon ta yake yana karatar yanayin ta,ya kuma hanata kwace hannun nata, shafa kansa yayi da hannu daya yayi murmushi yace


"Muje ki fara zabar min masu kyau kuma kar amarya tace ban iya zabe ba."


Wajen da ya ajiye system din ya jata, ta haye gadon ya zauna a gefen ta yana saka system din a tsakanin su, ya shiga nuna mata kayan tana kallo, duk wanda ya nuno sai tace be kyau ba, har suka dau lokaci a haka ba tare da ta zabi kowanne ba, sunan Yasmin ne kawai yake mata yawo aka, tasan ta gama haduwa iya haduwa dan tasan Tariq bazai kula yarinya kamar ta ba. Zamewa tayi ta kwanta bayan ta dan matsa zuwa dayan side din gadon, ta rufe idon ta taja duvet ta rufe har kusan kanta. Tattare system din yayi da  wayoyin su ya dora a saman chest of drawers, ya karo sanyin dakin ya kashe wutar ya hawo gadon ya kwanta a wajen da ya tashi, ya bar space a tsakanin su. Juye-juye suka dinga yi dukkan su, kowa da abinda yake sakawa a ransa


"Little Jidda?" Ya kira sunan ta yana matsawa zuwa tsakiyar gadon,amsawa tayi ciki-ciki, ya saka hannu ya juyo ta suka kalli juna ta dan hasken da ya shigo ta corridor din dakin


"Tell me about you, everything about you kinji?"


Dan motsawa tayi ya sake jawota sosai zuwa jikin sa, 


"Fada min, bani labarin Jidda."


"Yanzu? Bacci nake ji fa."


"Ba wani, inajinki kina ta juyi, kin kasa baccin."


"Ni da gaske bacci nake ji har na fara ma."


"Oh okh, to bari na saka ki wartsake."


Sai ya matso da fuskarsa wajen tata, ya rufe idon sa ya hade bakin su waje daya. 

   Kamar yadda ruwa yake idan ya dauke haka tunanin jidda ya dauke, ya kwasheta ya sauke ta a wani bigire na daban, kasa ko da kwakkwaran motsi tayi, tana jin shi cike da mamakin sa, sai da ya gaji dan kansa, sannan ya matsa da kansa baya ya dora shi a saman pillow yana kallon saman daki, 


_"Me ya same ni ne?"_ Ya tambayi kansa.


_"Me yasa nake kasa controling kaina when I'm with her?"_ Ya sake tambayar kansa. Tana da wani irin tasiri akansa,  a kanta yake bude baki yayi magana sosai fiye da yadda take yi masa kuma shima yake yiwa kowa, baya tunanin komai da kowa a duk lokacin da take gabanta. Murmushi yayi yana jin taste din salivar dinta a cikin bakin sa, dama he has been longing for this , ya dade yana imagining kansa kissing her small lips, he never expected her to be this sweet, a dah kallon karamar yarinya yake mata wadda yake ganin ba zata iya masa ba, kuma ba zata iya da needs nashi ba, but ya fara proving kansa wrong, and he is developing feelings for her, duk da babu yawa amma kuma yasan ko yaya ne dai. Juyowa yayi da kansa yaga ta sake juyawa dayan side din, yasan kunya taji, sai ya kyale ta kawai ya juya ya rufe idon sa, ko minti biyar be kara ba bacci yayi awun gaba dashi.


***Da asubah ta riga shi tashi, ta kalle shi babu ko riga a jikin sa sai 3quater wando, duk kuwa da sanyin dakin, ta rasa dalilin da yasa ko sanyin baya ji bayan ita har hancin ta ya toshe saboda sanyi ya kure AC kuma ya cire riga, shi jin zafin nasa ma extraordinary ne, toilet taje tayi alwala ta fito ta sameshi ya tashi ya kunna hasken dakin,alwalar da tayi yasa sanyin da take ji ya karu, yazo ya wuce ta ya shiga toilet din shima, rage sanyin tayi sosai ta kudundune da blanket sai da taji sanyin ya dan ragu sannan ta tashi ta dauko Hijab din ta saka ta shinfid'a sallaya zata tada ikama ya fito da ruwa a jikin sa yana gogewa da towel alamun wanka yayi, jallabiyar ya dauka ya saka ya ciro hula irin wadda ake kira da tashi ka fiya naci fara ya dora akansa ya fice da sauri dan kar ya rasa jam'i.


   Tana nan akan sallayar ya shigo dakin da sallama, ta amsa kanta na kasa bacci na fizgarta, zuwa yayi ya duka a gabanta ta dago jin shi a kusa da ita


"Baki bacci ba?" Ya kalli idon ta, da suka dan tasa, girgiza masa kai tayi


"Nayi."


"Ok, yau daurin auren yaran chan, munyi waya da Baba yanzu da wuri zan fita,dan Kano zamu a sumaila za'a daura auren ki kwanta kiyi bacci kinji?"


Ware idon ta, tayi da sauri taji ta nemi baccin ta rasa


"Ni ba zan je ba? Ba zani gidan ba?"


"Eh." Yace mata kai tsaye


"Ni kadai zan zauna?"


"Eh." Yace mata nan ma


"Dan Allah kayi hakuri, wallahi tsoro nake ji, kuma duk su Amira suna nan har kayan da zamu saka yau an karbo, dan Allah ka barni dan Allah."


Sai ta fashe masa da kuka wiwi, yana durkushe akan digadigin sa,yana kallon ikon ALLAH, abu kad'an sai kuka? Me zata je tayi toh kuma? Baya son duk abinda zai faru tsakanin shi da Mama ya shafe ta, yasan nata sai yafi zafi shiyasa yaga gwara tayi zaman ta. 

  

"I'm sorry kinji, zan turo su Amiran sai su zauna dake."


"Ba zuwa zasuyi ba, biki ake fa."


"Toh shikenan, babu abinda zai sameki ai,akwai masu aiki a waje, Fauwaz zai kawo duk abinda babu a kitchen."


Sai ya mike ya isa wajen kayan sa, ya dauko sabuwar shaddar sa fara kal da babbar riga, ya dauki takalmi, agogo da hular sa, da sauran abinda zai bukata, dan a gidan zai shirya, mota yaje ya kai ya dawo har lokacin kukan take sosai, baya so ta karyar masa da zuciya har yace taje, sai kawai ya tsaya daga kofar yace mata ya tafi, ko dagowa batayi ba, yayi jim a tsaye sai kuma ya juya ya fita dan baya so Baba ya kuma kiran sa dan babban aiki ya sashi, kuma sune zasuyi gaba kafin su Baban su iso shiyasa ma ko breakfast be tsaya yayi ba.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links