SANADIN LABARINA 35


  Page (35)


***Kasa daga kafarta tayi daga in da take tsaye, taji kamar ana sassara mata su, tsoro ne ya shige ta, tsoron abinda zata tarar idan har ta bishi, bata yi tunanin da gaske aunty take ba,da tace yau zata tafi, sai ta dauka kawai tsokanar ta sukeyi, a yanayin da ya shigo mata ta tabbatar ba da wasa yake ba, me ya kamata tayi? Ta tambayi kanta tana tsaye rike da Hijab din gashin kanta a barbaje dan ko ribbon bata saka masa ba.


"Aunty." Tace tana kallon in da ta ajiye wayar ta da nufin ta kirata a waya tazo tunda tana part din Baba. Babu wayar a wajen, dudubata ta shiga yi amma bata ganta ba, tasan kuma a saman gadon ta ajiye ta, cigaba da dubawa tayi tana rike da Hijab din tana tunanin abinda ya kamata tayi.

   In da yasan zai samu Auntyn ya nufa, yayi knocking a kofar ya tsaya rataye da hannayen sa a bayan sa. Bude kofar tayi, 


"Tariq?"


"Aunty zamu tafi ne dama, shine nace bari na fada miki."


Wani irin sanyi taji a k'asan ranta, tayi murmushi tana gid'a masa kai


"Ba komai ai, akwai kayanta a wata trolly sauran sai a kawo mata da safe, Allah ya tsare ya taimaka."


"Amin , Baba be dawo ba?"


"Yana hanya, zamuyi magana dashi."


"Nagode Allah ya kara girma."


"Amin Amin."


Tace ta kasa boye farin cikin ta, wucewa yayi sai da ta daina hango shi sannan ta rufe kofar zuciyar ta cike da farin cikin Jidda zata samu nutsuwa da sauyin rayuwa irin wadda take mata fata.


Tana tsaye ta gama dube-duben wayar bata ganta ba sai gashi ya shigo, be kalli in da take ba, ya saka hannu yaja akwatin yayi gaba. Yanayin fuskar sa kadai ta ishe ta ta gane ba da wasa yake ba, dole ta saka Hijab din ta tura ribbon din a hand bag dinta tabi bayan sa a sanyaye.

  Har ya shiga mota tunda a gaban wajen yayi parking dinta dama, ta hasken da ya haska cikin motar ta hango shi yana kokarin tada motar, kofar gaban a bud'e take, ta karaso ta shiga a sanyaye ya yi reverse suka fita daga gidan. Babu wanda yayi ko tari a cikin su, tukin sa kawai yake har suka isa gidan dake dauke da me masu gadi da securities saboda yadda rayuwar ta zama yanzu. Gida ne madaidaci wanda be cika girma sosai ba, amma kuma ya yi kyau sosai ya dace da masu gidan. Idanun ta akan compound din gidan sanda yayi parking a gefen wata mota dake fake a cikin gidan baka me kyau. Kashe motar yayi ya fita, itama sai ta fito duk da be ce mata ta fito din ba, ya mikawa wani matashi car key din sannan suka haura saman balcony zuwa kofar da zata sadaka da cikin gida. Yana gaba tana bin shi a baya suka shiga cikin falon da yake a matukar tsare, ko ina fes fes komai na ciki sabo ne kal an kawata falon da kaya kalar golden masu daukar ido. 

  Hular dake kan sa ya cire ya ajiye a saman centre table din dake tsakiyar falon ya wuce zuwa bedroom din da ya maida shi nasa, dan tuni duk ya tattaro kayan shi daga gida ya kawo su. Cire kayan da yake jikin sa yayi ya sauya zuwa doguwar sakakkiyar jallabiya milk colour ya fesa turare a jikin sa. Ya zauna yana ciro wayar sa da tata, ya bud'e ya saka number sa ya kira yaga tata number din yayi saving sannan ya jona su a jikin chargy ya kwanta a kan sofa yana mike kafarsa. Be san ko hukuncin da ya yanke yayi daidai ba, shi dai kawai yabi abinda zuciyar sa ta fada masa ne.

   Kiran wayar sa akayi, ya tashi yaje ya dauko sai yaga Baba ne yake kira, nauyin Baban yake ji a yanzu dan be san yayi abin kunya ba sai da yaga kiran Baban. Kamar ba zai daga ba ganin zata katse yasa ya daga.


"Baba barka da dare." Yace yana kokarin danne kunyar da yake ji


"Barka dai Tariq, ashe kuma kun wuce sai da na dawo nake samun labari."


"Na'am..." Yace yana sosa kai, dariya Baba yayi


"Shikenan ka shigo da safe inason ganin ka, kar kuma ka manta da maganar da mukayi akan zuwa gaida Baffan naku."


"In sha Allah ba zan manta ba."


"Toh madallah, Allah yayi muku albarka."


"Amin ya Allah, sai da safe."


"Mu kwana lafiya ango." 


Baba yace cikin sigar tsokana, ai be san sanda ya danna power button ya kashe wayar gaba daya ba. Sai kuma yayi murmushi tunanin abinda ya aikata na dawo masa, da kunya matuka amma ya zai yi? Hakan ya kamata dama tun farko, ya kuma tabbatar hakan ya farantawa Baban rai dan yadda yake masa magana zakaji muryar sa a sake take cike da annashuwa.


***Shiru shiru be fito ba, har ta gaji da tsaiwar ta zauna shiru, mikewa tayi tana kallon kofar da ita kadai ce a cikin falon, nan kuma taga ya shiga, yanke shawara shiga ciki tayi kawai dan ba zata yi ta zama ba. Kofar ta bud'e a hankali ga mamakin ta sai taga wani falon nan dan karami sai kofofin dake ciki, wadda take kallon ta, ta nufa ta murd'a a hankali ta tura kanta, sukayi ido biyu dashi idon sa akan kofar, saurin sakin handle din tayi zata koma muryar sa ta dakatar da ita


"Zo nan." 


"Na'am?" 


"Kinji me nace ai."


Shigowa tayi ta tsaya daga hanya, ya kalle ta ya kalli Hijab din jikin ta.


"Ki cire Hijab din kizo nan ki zauna."


"Ba tafiya zamuyi ba?"


"Kinzo kenan." Yace yana d'age mata kafadar shi


"Toh ai na zanje na kwanta? "


"A kaina."


 Yace mata kai tsaye, saurin kallon sa tayi ya d'aga mata gira, sai ta kauda kanta daga kallon shi cike da mamakin amsar da ya bata 


"Oya zo nan kafin na taso, kina bata min lokaci."


Matsowa tayi tana turo baki, ya girgiza kai yana sake kishingid'a sai da tazo daidai in da yake a kwance, sannan yace ta cire Hijab din, ta dade tana wasa da Hijab din ta kasa cirewa shi kuma yana kallon ta, da k'yar ta cire sai ta yafa shi a saman kafadarta zuwa chest din ta.


"Zauna."


 Ya nuna mata saitin cikin sa tunda shi a kwance yake, dan dosanawa tayi ta zauna duk a darare take, tashi zaune yayi yasa ta a tsakiyar jikin shi, numfashi taja da sauri tana kokarin gyarawa ya sauke kafafunsa kasa ta zama dai tana gabansa a zaune kafafun sa sun sakata a tsakiya, kunya da wani irin yanayi me wahalar fassarawa ta shiga, yayi kamar be san me yake ba, ya kai hannu zuwa saman kanta ya hau shafa mata gashin kanta da ya dade yana burin tabawa. Duk ta rikice ta kasa zama sai motsi take ta cigaba da abinda yake yi.


"Ina ribbon din?" 


Ya rad'a mata a kunnenta, tayi saurin bud'e jakar ta ciro ta mika masa, yayi murmushi ya kama gashin ya saka mata, be yi sosai ba tunda ba wai ya iya bane dama, tana jin shi yana cirewa yana sake maidawa a dole sai ya kama shi da kyau.


"Gashin doki ne?" Yace bayan ya gama daidaitawar a ganin shi


_"Na jaki ne."_ 


 ta fada a ranta, amma a fili shiru tayi kawai dan ko yayi tayi motsi sai taji ta a jikin sa gaba daya. Maimakon da ya gama ya barta ta tashi sai yaki, suka cigaba da zama a haka. Ya kunna wayar sa dake gefen su, ya kira Ishaq dan dama dazu yaga missed calls dinsa yana tuki lokacin. 

   

  A handsfree ya saka wayar bayan Ishaq din ya d'aga, suka gaisa sannan ya tambaye shi amarya dan Tariq din ya fada masa in brief, 


"Kana da matsala." Yace yana girgiza kansa


"Matsalar me? Daga cewa ya amarya? Ai wallahi kai dan gata ne, ga gida ga mota ga mata wallahi ka godewa Allah."


"Akace maka ban gode ba?"


"A ah kawai dai tuna maka nake ne, yawwa dazu ma Yasmin ta kirani zata dawo cikin week d'in nan har tace na fada maka."


Gaban Jidda ne ya fadi, jin an ambaci sunan Yasmin, ta yunkura zata tashi ya sake matsewa yana zagayo da hannun sa ta cikin ta.


"Karka dameni da magaanar wata yarinya pls."


"Ai dole na isar da sakon ta, ka sani ko da ita zakayi ta biyu? Yarinya me so da kaunar ka."


"Ni bana son ta."


"A ah fa, kar reshe ya juye da mujiya, ka sake tunani sosai."


"Idan ka shirya waya dani ka kira."


Ya katse kiran yana jan siririn tsaki, hannun sa dake cikin Jiddan yasa ya shafa cikin nata wanda yake flat kamar ba'a taba saka masa abinci ba.


"Bakya cin abinci ne?"


Banza tayi masa dan baki daya wayar da taji yanayi ta sakata a yanayi, gumi ne ma yake ta keto mata ta cikin jikin sa.


"Dole ki dinga cin abinci sosai, naga alamar bakya son ci shiyasa, ji cikin ki, wannan ai sai na balla shi."


"Zanje na kwanta." Tace a muryar haushi


"Oya kwanta mana, waya hanaki?"


"Dayan dakin zanje." Tace 


Sakin ta yayi yana ware hannun sa, ta tashi da sauri ta fice. Lumshe idon sa yayi ya bud'e, be san dalilin da yasa yake acting haka, ko dai magaanar Mama gaskiya ce son Jiddan yake?



***Dayan dakin ta shiga, ta jefar da Hijab din da jakar hannun ta, ta zauna tana kallon kofa, "yarinya me son ka da kaunar ka" ta tuno abinda na wayar yace, "ka sani ko da ita zakayi ta biyu?" Wani kululun abu ne yazo ya toshe mata a wuya, tana son ya Tariq sosai dan bata sake gane tana son sa ba sai da ta samu kusanci dashi sosai, ya iya duk abinda yasan zai tafi da hankalin mace, in a cool and matured way, ko kallon ta yayi sai taji wani iri bare yayi mata magana, closeness dinsu shi yafi komai taba ta. Duk da tasan baya son ta kamar yadda take son shi, amma zuciyar ta, taki barin ta, ta cire shi daga cikin ranta.

   Tsawon mintuna arba'in tana nan a zaune a wajen, dan bata da shirin tashi ma, ta saka wannan da kwance wanchan hankalin ta gaba daya yana wajen sa, ko ya cigaba da wayar sa ko ma ya kira wadda aka kira da sunan Yasmin din duk dama pretending yake da yace baya son maganar, tasan kadan daga aikin maza,toh amma ita a matsayinta na wa da har zai yi pretending a gaban ta? Ai bata jin tana da wannan matsayin ma baki daya.

   

   Kitchen ya nufa bayan ya fito daga dakin, yaje ya dauko yoghourt ya duba akwai ragowar cake din da yaci da safe, ya samu silver cup ya hado mata dashi ya nufi dakin nata, ya kwankwasa tayi saurin gyara zaman ta, ya turo ya shigo rike da plate din, kin kallon sa tayi ya ajiye ya kasan rug din gaban gadon ya zauna yana tankwashe kafarsa


"Ga dinner, na duba bamu da komai a kitchen din."


"Na koshi."


"Wallahi karya kike, sai kinci kuma."


"Ikon Allah."


"Ikon gaske, sakko malama, bana son iyayi." Yace yana gimtse fuska, kaamar zatayi kuka ta sakko, ya matso daf da ita har kafarshi na gogar tata,daukar cake din tayi ta soma ci cikin k'asa kasa da murya yace 


"Ki cinye tatas so nake cikin nan ya dago ko kad'an ne kar kizo ki kasa daukata."


Kwarewa tayi jin abinda yace, ya tashi da sauri ya kawo mata ruwa tasha, kanta a k'asa ta dauki yoghourt din tana sha tana kallon dayan side din, gaba daya ta gama gano ya Tariq bashi da ta ido ko kad'an, idan ya fadi wata maganar sai ka rantse bashi ne yafade ta ba, kuma ya fuske kamar be yi ba. A hankali ta shanye yoghurt din, ya dauke plate din ya fita ita kuma ta shiga toilet dan ta gyara bakin ta, ta dauka idan ya tafi ba zai dawo ba, tana fitowa ta sameshi a zaune ya kunna system dinsa ya dora ta akan kafarsa, gefen sa bakin shayi ne yana fitar da tururi.


"Menene size din underwears dinki?" Ya tambaya idon sa na kan system din, jin tayi shiru ya sashi dagowa


"Zan gane size din dayan da na gani dazu a wardrobe dinki."


 Yace yana mata shu'umin murmushi.

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links