SANADIN LABARINA 34

 

  Page (34)


***Wajen Yaya ta nufa dan tasan itace kai tsaye zata saka Baba ko ta hanashi. Ta kuma san ta yadda zata bullo mata ta daina ragawa Mama dan ta lura shirun ta yasa take ganin har yanzu tana da ikon taka ta. Bedroom din Yayan ta shiga ta sameta a kwance tana hutawa bayan ta idar da sallar walaha, tashi tayi zaune suka gaisa sannan tace magana tazo su yi


"Ina jinki Halima, mecece matsalar? Dan nasan dole akwai magana."


"Yaya dama akan maganar Jidda ce, ni a gani na tunda har Tariq ya dawo Jidda ya kamata ta tare a gidanta, dama taron bikin ake so ayi kuma ya nuna baya ra'ayi ni a ganina kawai ta tare shine mafi a'ala."


"Ni kaina nayi wannan tunanin kuma jiran Alhaji nake ya shigo, dan na ga alama dan ku bashi da ta ido sam, gwara su je chan su karata."


Dariya ta saka Yayan ta cigaba da bayani


"Al'muri da yake munafuki ne ai kinga yadda yake ko? Irin masu halin nan ke dai kawai ki kalle su, sun fi kowa iya shakiyanci."


"Yanzu ki barmun komai, a yau ba sai gobe ba zata tare, dan babu amfanin zaman."


"Allah ya kaimu Yaya, dama dai maganar kenan abun ya soma damuna."


"Ai dole, yarinya ma tayi hakuri ki bari zanyi maganin shi a yau din nan, sai kisa ta shirya duk abinda zatayi zuwa anjima."


"Toh bari naje Yaya, Allah ya kara girma."


"Amin kinji? Allah yayi albarka."


***Komawa tayi ta saka jiddah a gaba, da Safeera da ita suka taimaka mata ta hade koman ta waje daya, hannu bata saka ba ita a lallai ba in da zata tunda be san worth din ta ba, babu wadda tabi ta kanta musamman Safeera da tasan munafurci ne kawai ba har zuciyar, take maganar ba. Falo ta dawo tayi zaman ta, tana kissisima yadda zata kaya a zaman nasu, duk da kaso hamsin tana tsoron Mama amma kuma sauran kason na kwadaituwa da son zama dashi din.

   Fitowa Safeera tayi ta sameta a falon suka cigaba da zama sai ga Isma'il ya kirata, dagawa tayi jidda tayi kamar bata gane da wanda suke waya ba, suka dan jima suna magana daga karshe ta kashe tana murmushi


"Ya Isma'il ne, kinsan ya kusa zuwa gida."


"Allah sarki, Allah ya taimaka." 


"Amin, ni tunda tafiya zakiyi ma ai ba amfanin zama na, zan koma gidan Aunty Sajida kawai."


"Wai waye yace miki tafiya zan? Ki jira mana ki gani, nasan ba in da zanje."


"Toh zamu gani, yarinya gwara ma ki saka ranki tafiya dole."


"Idan nace ba zani ba ai babu me daukata. "


"Wallahi tsaf zai dauke ki din, tab!"


"Ke kika sani." 


"Ke ma kin sani ai."


***Ran Mama ya kai karshe a baci, dawowar ta kenan daga wajen Yaaya da ta turo aka kirata ta fada mata yau matar Tariq zata tare, da k'yar ta amsa da toh ta taso tazo ta fadawa su Aunty Nafi, suka kuwa hau fanfata akan karta yarda.

  Kiran TARIQ tayi be daga ba, sai ta kira Fauwaz shima sai da ta katse sannan ya biyo kiran tace masa ina Tariq yazo maza-maza, baya nan dan tun safe da ya fita training be dawo gidan ba, gidan sa ya wuce a chan yayi wanka ya shirya sannan ya koma bacci dan yasan idan be more baccin sa ba ya koma sai ya samu matsala, shiyasa har Maman ta kira be ji ba. 

 Sai da rana tayi sannan ya tashi ya dan sake gyara jikin sa sannan ya hau mota ya dawo gidan. Tun a hanya dama Fauwaz ya fada masa Mama tana neman sa, shiyasa yana zuwa part dinta ya wuce tana ganin sa tace ya shigo suka shige chan dakin ta in da babu kowa.


"So nake ka saki Jidda a yanzu ba sai anjima ba."


 Kawai tace masa ko zama bata iya yi ba. Kallon ta yake hankalin sa a tashe, ta hade rai taki bari ko kad'an yaga saukin ta, kasa furta komai yayi, ya dinga kokarin tattaro kalaman bakin sa amma ya gaza furta su, idan har yace zai iya sakin Jidda yayi karya, duk da ba wai yana mata son da ba zai iya rabuwa da ita ba, amma ba zai zo ya samu matsala da iyayen sa akan ta ba, haka kuma ba zai taba so hakan ta shafi iyayen sa ba


"Mama dan Allah mu bari mubi komai a sannu, dan Allah "


"Babu wani bin komai a sannu, yau kwana nawa kaana min alkawari amma ka gaza cikawa sai bin yar karamar yarinya a baya kamar wanda aka gama dashi."


"Wai Maama waye yace bin ta nake?"


"Kasan ni yarinya ce ai, bansan me nake ba."


"Ba haka bane Mama."


"Toh naji, duk ba wannan ba, bana son zaman ku karkashin inuwa daya, dan haka sai ka sawaake mata tunda ka kasa samun mafita."


"Baba fa? Zai yi fushi dani sosai."


"Ka barni dashi kawai, kai dai kayi abinda nace, ba zan iya jure ganin ta a matsayin sirikata ba."


"Amma Mama, mesa kika tsaneta haka?"


"Tambaya ta kake?"


" A'ah, kawai dai naga kamar yayi yawa ne mama, kiyi hakuri dan Allah mubi komai a sannu, Dan Allah muyi wa Baba biyayya kar muzo muyi abinda zai bata masa suna shi yanzu da yake a idon duniya abu karami zaki ji ana yi dashi."


"Ba zan ba, akan yarinyar nan zan iya batawa da kowa, idan har jinin Halima ce zata auri jini na, na gwammace komai ya faru."


"Mah?"


"Idan har na isa da kai, ka rabu da ita."


"Menene laifin ta a gareki Mama?"


"Babu komai, ba abinda tayi min kawai bana son ta ne."



"Shikenan mama, zanyi abinda kike so, amma ina zuwa Dan Allah."


Fuskarta ce ta fadada da farin ciki, t


"Dan Allah da gaske kake?"


Daga mata kai yayi


"Toh madallah, ka gama min komai Allah yayi maka albarka."


"Amin Ya Allah." 


Ya juya ya fita ita kuma ta koma wajen su Aunty Nafi zuciyar ta cike da farin cikin zata kuntata wa Auntyn dan dama tayi alwashin sai ta mata abinda zata dade tana jin ciwon sa.


 Ko da ya fita sai ya rasa abinda yake masa dadi, ko giyar wake yasha ba zai iya aikata abinda Maman take so ba, dan ba itace akan gaskiya ba, Baba yafi ta gaskiya dan haka dole ne yasan yadda zai yi be bata wa daya daga cikin su ba.

  Iyaye dole ne ka bisu kayi musu biyayya kuma mahalifiya tafi karfin wasa shiyasa yake matukar yi mata biyayya domin samun rabauta. Amma kuma a wannan gabar be san me yasa ba, baya jin yana tare da Maman.

  Zaman sa yayi a waje tare da masu gadin gidan lokaci zuwa lokaci yana dan saka musu baki a hirar dan yadda gidan yake cike da mutane bazai sake shiga ciki ba, tunda dai hankalin Maman ya kwanta for now zai tafi da ita a haka kafin yasan abun yi.

   Sai da akayi la'asar sannan ya tashi daga wajen, ya shiga cikin dakin su ya hau tattare muhimman takardun sa waje daya, ya zuba su a yar karamar jaka ya saka a bayan mota, sannan ya tafi kiran Yayan da ta turo tana neman sa. Chan cikin dakin ta, ta kule dan ba kowa take so yasan maganar da zasuyi ba. Mamakin ganin ta a nutse a zaune yasa shi shan jinin jikin sa


"Lafiya Yay?"


"Lafiya ta kalou wallahi."


"Menene ya faru?"


"Takardr jidda zaka ban?"


"Takarda kuma Yaya?"


"Eh, tunda baka son ta ba, ka sakar musu 'ya taje ta auri wanda yake son ta."


"Wanene?" Ya bata fuska 


"Ina ruwan ka? Wani ne yazo tun kafin ma  ayi maganar ka, wai mu masu shishigi da son gwaninta muka ce gida be koshi ba,ashe zaka zo ka watsa mana ido?"


"Aina yake shi din?"


"Oho ba zaka ji ba, ka bata takardar ta ba sai ta sake kwana da igiyoyin auren ka akanta ba."


"Kuma ita ma tana son shi?"


"Kaji mun yaro, ina ruwanka da wannan kuma? Kai tunda ba da gaske kake ba, ai sai kawai ka yanke hukunci Amma ba zai yiwu ka hanata kula kowa ba kai kuma baka so."


Mikewa yayi ransa a baci ya fice be sake cewa komai ba, dariya suka kwashe da ita, Fauwaz dake makale ya fito suka tafa da Yaya


"Kinsan ta kan tsiya Yaya."


"Ni din ta wasa ce? Sai shegen kishi amma girman kai ya hana shi gane halin da yake ciki."


"Ya sani fa Yaya, kawai yana hana kansa yarda da hakan ne, bari muga abinda zai yi kuma, bari naje naji yadda ake ciki."


"Karka manta kazo ka fesa min."


"Akwai amaana ai ni dake tawan."


"Amanar kad'an ce, tunda ka kusa kashe ni na dawo daga rakiyar ka, bakin mugu."


"Ai ya wuce sai zamu Kano sallah, da kafarki zaki taka ki shiga jirgin ma Hajiya Yaya."


"Bana so, babu kuma shegen da zai saka ni shiga."


"Zamu gani dai, bari naje nagano."


"Munafuki." Tace tana kallon sa, be ji me tace ba, ya fice dan da yaji sai ya dawo sun yi ta da ita.



Kai tsaye part din Aunty Tariq ya nufa ransa a bace fuskar nan tasa a hade tamau, babu kowa a part din Aunty na side din Baba, ita kadai ce sai Usman da yake wasa a falo yana kallon Disney World, tasowa yayi da sauri yayi hugging din Tariq din, ya d'aga shi sama yana kokarin daidaita fuskar sa


"Wasa kake?" Yace yana sauke shi k'asa


"Eh tare muke yi da Yaya Jidda tace zatayi sallah."


"Ina Aunty?"


"Ta fita."


"Ok zauna kayi wasanka ko? Ina zuwa."


Yace ya nufi dakin Jiddan, ta idar da sallah kenan taji rigar dake jikin ta, ta takura mata, sai kawai tayi deciding ta cire ta, data raka Safeera ne ta sakata amma dama bata iya zaman gida da ita, riga da wandon ta ciro na bacci masu dan kauri rigar iya guiwa sai dogon wando, ta saka tana gyara gashin kanta da ya barbazu akan nata ya murd'a kofar ya shiga da sallama muryar sa a chunkushe kamar wanda ya saka wani abu a makoshin sa ya tokare wajen. Kasa dagowa tayi tayi tsam a wajen da take ya shiga takowa yana karewa dogon gashin nata kallo. A daf da ita ya tsaya ta kalli kafarsa dake sanye da takalmi sau ciki. Muryar tasa a ciki-ciki yayi magana


"Ina Hijab dinki?"


Bata amsa ba, dan bata ga amfanin tambayar ba, wurwurga idanun sa yayi tayi a cikin dakin ya taka zuwa wajen da kayan ta suke, ya bude wardrobe din yana kallon jerin kayan dake gyare a cikin wardrobe din.


"Lefe." Ya fado masa a ransa, hannu ya sa ya ciro Hijab guda daya a cikin jerin kayan, pant dinta ne ya fado, ya sunkuya ya dauka ya kalli wajen da take a tsaye, da sauri ta kautar da kanta kunya matsananciya na kamata, ciki ya mayar ya rufe ya dawo ya mika mata, sannan ya dauki wayar ta dake ajiye a saman gadon, yace tasa Hijab din.


"Ina zamu?" Tace rike da Hijab din bata saka ba


"Gidan Mijinki zaki." Ya amsa mata kai tsaye, yayi hanyar barin dakin sai da ya kai karshe sannan yace


"Karki bata min lokaci."

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links