SANADIN LABARINA 33


   Page (33)


Be iya motsawa daga wajen ba, maganganun Mama da nata na cigaba da yi masa yawo akai, toh ko dai son nata yake? Ya tambayi kansa. No ba haka bane. Wata zuciyar ta rad'a masa, tausayin ta kawai kake ji, ya sake jin wata zuciyar ta tunasar dashi. 


"Eh haka ne, tausayi ne kawai nothing more."


Yayi assuring kansa yana samun hujjar da zai rike, kad'a kansa yayi ya fito daga dakin, duk da maganar ta, ta bata masa rai amma kuma ba zai yi abinda suke so ita da Maman ba, sai yayi istikara sannan ya samu gamsashishiyar hujjar da zai rikewa Baba ya yarda dashi. Wani kallo Yaya tayi masa da ya fito, yayi kamar be ganta ba yayi ficewar sa, ta yi dariya tana girgiza kanta, tasan akwai sauran drama amma kuma a chan k'asan zuciyar tana tausayin Tariq din, dan tasan irin su so be iya yi musu da dadi ba.


Tunda ta shiga dakin take juyi a gado, kamar ta tattara kayan ta, ta tafi wajn Baffa haka take ji, baki daya babu abinda yake mata dadi, tana nan kwance har aka soma dawowa, su aunty ne yan farkon tahowa suka taho tare da Safeera da zata kwana a gidan. Tana jin su ta fito da sauri, suka rungume ita da Safeera idon Aunty akanta, sai da suka zauna sannan Auntyn tace


"Jidda me ya faru ne wai?"


Turo baki tayi cikin yanayin rashin jin dadi tace


"Hanani yayi."


"Tariq hoo, amma me yasa?"


"Nima ban sani masa ba, kawai mugunta ce wallahi."


Tace kwala na sake taruwa a idon ta dan ko tunawa tayi sai taji hawaye


"Karki kara cewa mugunta duk tsiya mijinki ne, kuma duk abinda yace shi zakiyi."


"Aunty amma kinsan be kyauta ba ko?"


"Toh me zan ce jidda, tunda shine yake da ikon barki ko hanaki."


"Aikuwa, kuma dole ayi biyayya."


Safeera tace tana dariya, duka Jidda takai mata, tace ta taso su shiga ciki, suka bar Aunty ita kadai sai itama kawai ta wuce dakin ta dan watsa ruwa ta dan warware gajiya. 


  Bayan tayi wankan tana zaune a falon akayi knocking, kasancewar duk masu aikin gidan idan dare yayi basa shigowa suna bq yasa ba kowa sai ita kadai a falon, tashi tayi ta bud'e kofar sai taga Tariq a tsaye, matsa masa tayi ya shigo sannan ya rufe kofar


"Aunty yunwa." 


Yace yana zama idon sa akan hanyar dakin Jidda


"Bari naga ko zaka samu wani abun a kitchen."


"Aunty Indomie nake so, tunda nazo banci ba, a kira sai ta dafa min karki wahalar da kanki."


"Aikuwa Jidda gwana ce, dan tafi ni ma, suna ciki da kawarta Safeera bari na kira ta."


"Nagode Aunty." 


"Ah ba komai ai, bari na turo ta."


Tayi gaba tana murmushi, a kalla yanzu ta tabbatar da Tariq yana son Jiddan ta, abinda dama yake daga mata hankali kenan, sai gashi duk kowa ya gama gano shi duk da shi be gama gano kansa ba, he's so obsessed with her. Knocking tayi musu daga kofar ta dan bud'e tace


"Zo ki dafawa Tariq Indomie yunwa yake ji."


Zaro ido tayi, 


"A daren nan Aunty?"


"Eh yana falo yana jiran ki, ni kwanciya ma zan dan na gaji sosai, sai da safe Safeera."


"Sai da safe aunty."


"Jiran ki yake." Ta maimaita mata ganin tana zaune ko motsi batayi ba, tashi tayi ta dauko Hijab ta zunbula har k'asa sannan ta zura slippers ta fito tana zumburo baki Safeera na mata dariya, 


"Idan naji kin dade zan rufe kofa ta "


tace mata tana dariya


"Allah ya kiyaye na dade, sama-sama zan dafa masa na dawo daki, a daren nan ace ka wani dafa abinci kawai dan a kuntata maka." 


Tayi maganar bayan ta rufo dakin yadda Safeeran ba zata jiyo ta ba, yana tsaye jikin bangon corridor din duk yaji me tace, kallon sa tayi gaban ta, ya fadi, ya kad'a kansa yana nuna mata hanya


"Wuce na fasa Indomie din ma, sakwara nake so."


"Wallahi ban iya ba." Tace da saurin ta, dariya taso bashi ya kanne yana nuna mata hanya


"Ita mijinki yake so dole kuma ki yi masa abinda yake so ko na fadawa Aunty."


Tafiya ta cigaba da yi zuwa kitchen din ya take mata baya, ya samu jikin freezer ya tsaya yana folding din hannun sa, tsayawa tayi tana kalle-kalle kamar me neman wani abu,


"Dafa indomie din amma kikayi min sama-sama sai kin daka min sakwara da tiny hands din nan naki."


Indomie din ta dauko ta, ta dora yana kallon ta, 


"Bana son jagwalgwalo kuma."


"Ni bana iya abu idan aka sakani a gaba."


"In fita kenan?"


"Eh." 


Tsalle yayi ya haye saman deep freezer din


"Karewarta ma kenan, kiyi sauri kuma karki sa yunwa ta kama ni."


Bata sake magana ba, ta cigaba da abinda take yana kallon ta, waya ya ciro ya hau dannawa ta juyo kad'an taga hankalin sa na kan wayar, yaji ta dauko ta kara a Indomie din ta rufe duk be gani ba. Ta gama ta saka masa chicken a ciki amma sai yace ta soya masa egg, nan ma kamar ba zatayi ba ta soya egg din ta hada komai a tray amma sai yace mata saura oat, kamar tace ba zata dama ba amma dai ta daure dan ta lura shi kamar zaman shi a kitchen din be dame shi ba. Dining ta wuce ta dora akai bayan ta gama, ya duro yana maida wayar aljihun sa, ya tako zuwa wajen dining din, yaja mata kujera daidai in da ta ajiye abincin


"Zauna." Yace yana rike mata kujerar.


"Na'am?" 


"Sit down!"


 Zama tayi ya tura ta ya maida kujerar jiki yana tsaye daga bayan ta


"Oya, cinye tatas."


"Bana jin yunwa."


"Wallahi sai kinci, ina kallo kika zuba mun yaji ai, so kike na mutu ko?" Ya zuro mata kansa ta bayan kujerar


"Ai me yaji tafi dadi."


"Oya, ci."


Daukar fork din tayi ta fara ci, wani masifaffen yaji ya shiga har cikin kwanyar kanta, bata son yaji komai kankantar sa, shishi ta fara ya yi murmushi yana cije kasan lips dinsa,


"Yaji ko?"


"A ah kwarewa nayi."


"Ok sannu, oya eat maza-maza."


Jujjuya fork din ta soma yi, ya ja kujerar gefen ta, ya zauna yana tallafe fuskar sa. Narai-narai tayi da fuska kamar zatayi kuka amma ya fuske, ya dauki oat din ya fara sha, yana kallon ta. 


"Dan Allah kayi hakuri ba zan kara ba."


"Me kikayi?"


"Yaji na saka maka."


"Me yasa?" Ya tsare ta da idanun sa, sauke kanta tayi kasa da sauri


"Oya tell me, me yasa kika cika min yaji?"


"Nima bansani ba."


"Toh karki sake."


"Ba zan sake ba."


"Good girl, kije ki kwanta toh, sweet dreams"


Da sauri ta mike, dama jiran kad'an take, tayi gaba ya bita da kallo ya girgiza kansa, yayi sauri ya karasa shan oath din ya tashi ya bar part din.



***Washegari da safe Aunty na dakin ta, Rasheeda tazo ta sameta wai Mama na falo tana magana da ita, abin ne ya bata mamaki dan tunda ta dawo Abujan sau daya Maaman ta shigo shashen ta shima rashin lafiya tayi har da karin ruwa shine tazo a tsaitsaye ta duba ta. Tasowa tayi cike da mamaki ta fito sai ta sameta a zaune tana karewa falon kallo, tana ganin Auntyn ta fito ta mike tsaye


"Ina kwana Maaman Fauwaz?"


"Lafiya, ina Jidda?"


"Jidda kuma? Me ya faru?"


"Bani da damar kiran Jidda kenan?"


"A ah ba haka bane, bari na kira ta." 


Tace, girgiza kafa Maman tayi bayan ta koma ta zauna wajen da ta tashi, zuwa tayi ta kira Jidda, suka fito tare. Ganin Maman a zaune yasa ta samu k'asa ta zauna ta gaishe ta cike da girmamawa, amma maimakon ta amsa sai ta shiga aiwatar da abinda ya kawo ta


"Me kikayi wa Tariq?"


"Na'am?"


"Me kikayi masa? Wanne kalar asirin akayi ma d'ana da har ake so ya zama wani sulobiyo yana bin ki kamar wani jela?"


"Kamar ya wai?" Aunty tace


"Kamar yadda kuka sani,nasan idan har ba wani abun kukayi masa ba wallahi Tariq yafi karfin ya dinga bibiyar ta haaka."


"Haba Maman Fauwaz, mu babu abinda mukayi masa wallahi, me zamuyi ma?


"Oho, wallahi ba zan dauka ba, ba zai yiwu a maida min yaro wani gashi nan ba, tun wuri ki sani wallahi, dan wannan karon da karfi na nake, kuma zan yi komai na karya wannan kaddararren auren."


Sai ta mike,


"Ki shirya bugawa dani a wannan karon, dan bana hada Tariq da kowa saboda haka ba zan taba bari ba wallahi."


Sai ta juya ta fice kamar kububuwa, dariya Aunty tayi bayan ta fice jiddah da ta tsorata ta kalli Auntyn


"Share ta Jidda, wallahi ba abinda zata iya duk barazana ce, kuma idan ta isa sai ta hana Tariq din ko? Amma ba ke zata zo tana fadawa magana ba,na daina yi mata shiru wallahi, duk abinda tazo dashi a shirya nake nima, Tariq kuma in sha Allah sai kin haifa masa yayan da zata goya a bayan ta."


"Aunty ni tsoro nake ji, dan Allah ko a hakura."


"Akan me? Wallahi ba a isa ba, ki zauna shekara guda kina jiran sa ya dawo sai ace a hakura? Saboda mu ne bamu da galihu ko? Toh ba'a isa ba wallahi, kuma a yau ba sai gobe ba, zaki tattara ki tafi gidan ki ai an gama komai, ban ga zaman me kike ba ma."


"Bari kiga." Tace ta dauki veil dinta ta rufa kanta ta fita, tashi Jidda tayi ta koma dakin ta duk babu dadi, bata son tashin hankali kuma bata so Aunty ta yi abinda da batayi ba akanta.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links