SANADIN LABARINA 32


  Page (32)


***Kofar motar a bud'e take, taje ta shiga ta sunkuyar da kanta k'asa zuciyar ta na tururi, agogon hannun sa ya kalla ya kalli cikin motar, ya kad'a kansa ya tako zuwa wajen motar, ya rufe mata kofar ya zagaya ya shiga ya zauna.


"Ki daura seatbelt." 


Yace yana jan tasa ya daura, ya kunna motar, hawaye ne ya shiga sauko mata na bakin ciki, duk kawayen su na school zasu je Amira ta fada musu Safeera ma zata wuce daga chan dan ta shigo tana gidan aunt dinta. Sake kallon ta yayi yaga bata daura seatbelt din ba, matsowa yayi jikin ta,ta dago ya kalle ta yayi mata murmushi, irin murmushiin na ci karfin ki, kauda kanta tayi ya jawo belt din ya daura mata, ya tsaya daf da ita bayan ya daura matan, k'in juyowa tayi tana jin ji daf da ita, k'ashin wuyan ta ya kalla, yaga rami, hannu ya kai ya taba ta juyo da sauri


"Har ajiya za'a iya yi a wuyan nan naki." 


Yace hannun sa yana kan wajen, fuskar sa a sake yana so ya kure ta, banza tayi masa tana jin yadda yake tafiya da hannun sa akan wuyan nata, wani irin take ji amma ta fuske dan sosai take cikin bacin ran hanatan da yayi wanda bata ga dalili ba. 


"Kina wannan kamshin turaren zaki shiga wajen da yake da garadan maza? Baki san darajar aure bane?"


Yace yana kokarin saka idanun sa acikin nata, 


"Haramun ne, ki bari mu samu solution sai kiyi ma duk abinda zakiyi, amma dai yanzu na hana,."


"Sai ayi sauri a samu solution din, I'm sick and tired, na gaji." 


Sai ya fashe masa da kuka dan ba karamin haushi maganar sa take bashi ba, kullum sai yayi kokarin shiga rayuwarta haka kullun sai ya jaddada mata jiran lokaci yake, ta gaji kawai ya yanke hukuncin da duk ma zai yanke dama ta riga ta shirya. Tsayawa yayi chak yana kallon ta, kukan take bil hakki da gaskiya, ya rasa kwakkwaran dalilin da zai saka ta dinga irin wannan kukan, be sani ba ko zama kusa dashi ne bata so, ko ganin shi ma gaba daya ne bata so. Gashi shi kuma yana jin shi very comfortable duk sanda suke tare, yanzu ma yana samun labarin zasu dinner ya taho hankalin sa ba a kwance yake ba, baya so taje wajen ayi ta kallon ta, ba kuma dan yana so ko kishin ta ba a nasa tunanin, sai dan kawai ya kare martabar auren sa da yake kanta.


"Komai kuka, kuka baya maki wahala ne?"


 Ya tambaya yana maida kansa ya jingina a jikin kujerar motar yana duban ta, kamshin turaren ta, na fuzgarshi zuwa gareta, sai dai yayi matukar kokarin hana kansa, yana jaddadawa kan nasa cewa . Kokarin daidaita kanta tayi, ta goge fuskar tana hana kukan cigaba da zuwa, kukan bakin cikin abinda yake mata ya kuma nuna sam be san ma me yake ba, yanzu da tayi magana maimakon ya amsa mata sai ma ya tsaya kawai yana kallon ta, ya kuma sauya zancen zuwa wani na daban. Jin tayi shiru ne yasa shi tashi ya sake kunna motar ya ja suka fice daga wajen.

   Kasancewar babu nisa tsakanin nan da gidan ya saka su saurin isa, hakan ya kara tabbatar mata da ba zata je din ba kenan. Sai da ya shiga har cikin gaban part din Auntyn sannan yayi parking, bata jira komai ba, ta bud'e kofar ta fice, maimakon ta shiga nasu bangaren sai ta chanja hanya zuwa part din Yaya. Parking ya gyara ya bi bayan ta da sauri dan ya hango wasu samari a wajen suna zaune, kasancewar da sauri yake tafiya yasa yayi saurin cimmata, ya rufa mata baya yana kakkareta. Ta ganshi sarai amma tayi kamar bata ganshi ba, suka cigaba da tafiya tana daga kafa yana sauke tasa har suka shiga. Yaya na zaune ita da Gwaggo da wasu a falon ta shigo, ta shige dakin Gwaggon da saurin ta, bude baki Yaya tayi zatayi magana sai gashi ya shigo 


"A ah, tare kuke ne?"


"Eh." Yace yana shigewa ciki shima bayan ya gaishe su a gajarce


"Ina wajen bikin kuma?"


"Ko har an dawo? Gwaggo tace


"A ah be isa an dawo ba, bari naje naji dan yadda Jidda ta shigo kamar ba kalou ba."


"Toh Allah yasa lafiya."


"Amin." Tace tana mikewa da k'yar dan kafarta ta fara matsa mata sosai. A tsaye ta same shi daga kofar ita kuma jiddaa na saman gadon ta rufe fuskarta, duk kwalliyar da akayi mata ta baci ga shi sai kiran wayarta su Safeera suke Aunty ma ta kirata ta kasa dagawa.


"Ya akayi me ya faru?" Yaya tace tana kallon sa


"Wai dan nace ba zata je dinner ba, shine take kuka."


"Kamar ya ba zata je b? A wanne dalilin yasa ba zata ba?"


"Menene amfanin zuwan toh?"


"Abinda suka dade ana shiryawa zaka hanata fisabillillah, gaskiya baka kyauta ba wallahi, Jidda tashi kinji, daina kukan haka nan kiyi hakuri, kai kuma sai ka gaya min kwakkwaran dalilin da ya sa ka hanata wallahi, dan ni banga dalili ba."


"Ni ba wani dalili, kawai bana so ne, ta bari taje idan babu aure na akanta."


"Ahayyye!" 


Tayi shewa tana tafa hannu, kicin-kicin yayi da fuska Yaya ta rasa me ma zata ce


"Ai be kamata ba, tunda dai shi aure daraja ne dashi, kuma ni bana son irin wadannan abubuwan, ta bari a samu hanyar da za'a kawo karshen komai."


"Kai tafi chan, wacce hanya ce da ba za'a iya samar da ita ba har sai an ta maganar ta, ai kawai yanke hukunci ake idan har da gaske har zuciya ana neman hanyar, ba a fatar baki ba.".


"Tashi kinji Jidda, ki rabu dashi bakin hali ne yayi masa yawa da mugunta, idan ba haka ba a gama shirya abu dan gadara ya hanaki zuwa haba."


Tashi tayi idonta har sun daga saboda kukan bakin ciki, gaba Yaya tayi tazo zata raba ta gefen sa ta wuce ya tare hanyar yana mata wani irin kallo da idanun sa suke a shanye, 


"I'm sorry." 


Ya samu kansa da furtawa dan da gaske yaji babu dadin abinda yayi mata, kin amsa wa tayi zata wuce ya sake tarewa


"Please kiyi hakuri."


"Zan rungume ki idan baki hakura ba."


Kallon sa tayi da sauri, ya gid'a mata kai, 


"Da gaske nake Allah."


"Na hakura." 


Tace ganin yana matso ta, amma duk da haka sai da yayi hugging din nata,abinda yake taso tun dazu, yana so ya shaki kamshin jikin nata sosai amma kuma yana hana kansa, daga karshe yaga ba zai iya ba, tunda dai ba wani abu yayi ba, kuma ai ba haramci ya aikata ba. Yaya ce tayi saurin fita dan da ta labe a falon, dariya ma ya bata dan tasan dama wuyar ta yazo hannu, irin su masu sum-sum din nan sun fi kowa iya shege


"Almuri." Tace tana zama a in da ta tashi, 


"Me ya faru Yaya?"


"Wai ya hanata zuwa wajen bikin dan shegen kishi."


"Abinda kake so ai shi kake kishi Yaya."


"Bar dan bantan uba, yana so yana yare, zai gane shayi ruwa ne, dama ai dan hakkin daka raina..."


"Haka ne, kina ga a yadda ya shigo fa, kamar ma da fari be lura damu ba."


"Ina zai lura so ya rufe masa ido."


"Kai Yaya." 


"Allah kuwa, yaga yar karamar yarinya duk ya rude babban kwabo, da yana cika bakin shi baya so yan-yan-yan." 


***A yadda yake ji kamar kafarsa ba zata dauke shi ba, gashi duk yadda taso ya kyale ta, ya kasa, sai da wayar sa dage cikin aljihun gefen rigar sa tayi kara sannan ya saketa yana matsawa baya, da sauri ta koma cikin dakin ta kule chan karshen gefen gadon shi kuma ya d'aga wayar ganin Mama ce


"Wai Tariq me kake nufi dani ne?"


"Na'am Mama?"


"Eh, Jidda bata zo wajn nan ba, sai naji labari na yawo a wajen wai kaje ka dauke ta a gidan makeup kace ba zata ba, me yasa zaka je ka dauke ta? Kuma me yasa zaka hanata zuwa? Bangane maka ba kwata-kwata."


_"Ba zan iya bari tazo wajen nan ba."_


 yayi maganar kasa kasa amma duk da haka sai da taji shi, 


"Ba zaka iya bari ba? Saboda kana kishin ta ko?"


" Ni? Noo ba haka bane, kawai dai tunda ba wai an riga an rabu bane, dole na kare martabar auren, shine kawai amma ba wani abu bayan nan."


"Kasan da yake kai ka haife ni TARIQ, son yarinyar nan kake."


"Mama!"


"Ka dauka ana wa namiji auren dole ne kuma baya son matar yayi hakuri ya cigaba da bin ta kamar jela, ina lura da kai wallahi, duk take-taken ka na gani."


"Amma Mama ba haka bane, ni ba haka bane, ba spec dina bace ba, no ba haka bane gaskiya."


"Sai kayi kuma, na bar baki."


Ta katse kiran, rike wayar yayi saroro a hannun sa yana jujjuya maganar da Mamsn tayi masa a ransa. Duk maganar da sukayi tana ji kuma ta san akan ta ne, kekashewa taji zuciyar ta, tayi lokaci daya, babu amfanin cigaba da zubar da hawayen ta akan mutumin da ya cika da son kanshi, tasowa tayi tazo har gaban sa, ta tsaya sannan tace.


"Kayi sauri ka kawo karshen wannan drama din, kaga sai ka samo daidai da kai din."


Daga haka ta wuce shi kawai ta fice daga dakin, ta wuce part din Aunty ta shiga dakinta,tayi kwanciyar ta,tana hana kanta sake kuka akan sa.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: _SL__**


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links