SANADIN LABARINA 30


    Page (30)


***Wani abu yaji tunda tsakiyar kansa har zuwa tafin kafarsa, yaji kamar duniyar na juyawa baki daya a tsakankanin su, su biyu kadai, kokarin zare jikinta take ya matse ta sosai ya hana mata ko da kwakkwaran motsi. Lamo tayi tana jan numfashin kadan-kadan. Bugun zuciyar ta ne ya hadu da nasa, har tana iya jin yadda tasa ke beating very fast kamar wanda yayi gudun tsere. 


"Why are you always crying?" 


Yace cikin muryar sa da ta shiga chan ciki, bata amsa ba, sai dan motsawa da tayi kad'an ya sake kankame ta


"Tell me? Ba kya son auren?"


Wani irin faduwa gaban ta yayi, ya cigaba da magaanar cikin kunnenta


"Nima bana so... So ki daina kuka zamu samu hanyar da ba zamuyi hurting iyayen mu ba, I promise you."


Baki daya tunanin ta ne ya tsaya na dan dakiku, taji gaba daya duniyar na juya mata, a tunanin sa saboda bata son auren take kuka? a tunanin ta kuma ta dauka he's ready to accept her, a tunanin ta ba zai iya furta mata baya son auren ba duk da bata da yakinin dama yana so din, a karo na biyu ya sake breaking heart dinta, into pieces. Fizge jikin ta tayi da karfin gaske, ta matsa daga jikin motar ta juya masa baya. Kallon bayan ta yake yana jin duk babu dadi. Kukan ta cigaba da yi yana jinra, yana jin wani irin zafi a cikin zuciyar sa, be san meyasa kukan yake taba shi ba, duk da dama shi a rayuwar sa ya tsani yaga mace tana kuka, kallon su yake a matsayin wasu weak mutane da kukan kawai zai iya haddasa musu babban al'amari. 

   Zuciyar ta ce ta dake, taji a lokaci daya kukan da take ya dauke, taji bata son sake ko da minti daya ne a zaune a cikin motar, babu amfani, kwata-kwata babu amfanin cigaba da kukan ta, duk da tasan da gasken gaske take son shi, amma kuma babu amfani tunda shi baya so, zata sakawa zuciyar ta salama ta karbi duk wani abu da yazo mata, ba zata sake bata hawayen ta ba, balle murfin motar tayi, zata fita yayi saurin fincikota, ya rike ta k'akam yana saka idon sa acikin nata


"Menene matsalar ki?" Ya fada yana zagaye idanun sa a kan fuskar ta


"Ka kyale ni dan Allah."


"Me yasa? Tell me? Ki bud'e bakin ki, kiyi magana."


"Gida nake son zuwa." Tace tana kauda kanta gefe ganin yadda yake motso da fuskar sa daf da tata. 


"Zaki je gidan, just tell me menene yake saki kuka? Are you sick? Baki da lafiya ne?"


Girgiza masa kai tayi


"Toh menene? Tell me dan Allah..." 


"Ba komai, ni ka kaini gida."


"Ba zan kaiki din ba, anan zamu kwana babu in da zaki."


Kallon sa tayi ya gid'a mata kai, kwace hannun ta, tayi ta motsa kafarta  tana kokarin sauka yace


"Idan kika fita wallahi sai na baki mamaki."


Kamar bata ji ba, ita burin ta kawai ta je gida, ta gaji da zama waje daya dashi knowing fully baya son ta, he's just concern akan kukan da take, which yake tunanin ma son auren ne bata yi shiyasa.


 Folding hannun sa yayi yana kallon ikon Allah, ta sauka daga motar tayi gaba. Da sauri ya fito daidai lokacin da wata mota ta haske ta, ya hango gashin kanta ta dan mayafin dake kanta da ba wani na kirki ba da wanda ya bayyanar da kusan gashin kanta, wasu maza sake  kusa da ita suka kalle ta, da saurin sa cikin baci rai ya riko hannun ta, ya shiga janta zuwa motar, ya turata ya danna lock sannan ya koma ya shiga cikin motar, yaja suka bar wajen.

  

Kukan ta cigaba da yi masa, ransa ya sake baci sosai, ya dinga gudu sosai a titin ya dauke hanyar gidan, kanta na k'asa har suka karasa in da zasu, yayi parking sannan ya zura kansa baya ya bud'e ledar kayan da ya siyo dazu, ya dauko jacket din sa, ya zauna sosai sannan ya dora mata ita a saman bayan ta, dagowa tayi idanun ta da sukayi ja sosai ya kalla sai ya kauda kansa, ya shaki iska ya fezar da bakin sa, sannan ya juyo yana tamke fuskar sa sosai, ya dauki rigar ya bude ta, ya sa hannu ya janye mayafin dake jikin nata, ta kalle shi da sauri ya dalla mata harara ya shiga saka mata rigar akan doguwar rigar dake jikinta, ya balle botir biyu na jiki ya bar sauran, sannan ya dauki mayafin ya nannad'a mata akanta, ya sake zagayo dashi ya rufe kan nata, ya d'an ja baya ya kalle ta kad'an sannan ya zagaya ya fita ya bude mata.


"Fito." Yace yana kauda kansa gefe


Kallon wajen tayi, ta ki fitowa, 


"Fito nace kafin ranki ya baci."


Yayi maganar still yana kallon gefe, share hawaye tayi, ta zuro kafafunta ta fito, ta tsaya a gaban sa, yar karama sosai akan sa, bata fi ya hadiye ta ba


"Strong head."


 Ya furta sanda ta tsaya a gabansa kanta na k'asa. Hannun ta, ya kama cikin nasa, ya shiga takawa zuwa cikin building din, wanda yake dauke da tsirarun mutane saboda yadda lokacin ya dan fara ja, reception yaje ya karbi key ba tare da yace komai ba,suka haura sama ya ciro key ya saka a jikin kofar ya bud'e,suka shiga ciki ya maida kofar ya rufe. Guest house din Baba ne, anan yake saukar duk wasu bakin sa, daki ne babban gaske, me dauke da madaidacin gado, tv, fridge da yar madaidaciyar wardrobe. A jikin kofar taja ta tsaya,yayi gaba abin sa ya zauna a gefen gadon yana zaro wayar sa, tun dazu yake jin kiran amma yaki dagawa saboda baya son yin magana a yadda yake jin sa. Ta gefen idon sa ya kalleta tana tsaye a jikin kofar ya dauke kansa, yau sai ya kure ta duk miskilancin ta kuwa, kuma sai ya nuna mata shi din gaba yake da ita ba daidai suke ba, shiyasa ya fasa komawa dasu gidan, yaga yadda zatayi yasan dole a karshe ta magantu,daga nan sai ya maida ta din.

   

Tsawon lokaci tana tsaye a kofar har kafarta ta fara sagewa, kamar be san da ita a wajen ba yadda ya dinga sabgogin sa, zamewa tayi ta zauna kawai a wajen ta hada kanta da guiwar ta. Tashi yayi ya duba time yaga sha daya har ta kusa, sai ya shiga toilet ya dauro alwala yazo yayi akan dan madaidacin carpet din dake wajen, ya idar ya haye kan gadon ya kwanta bayan ya kashe hasken dakin ya zama sai kad'an 

  Dagowa tayi tana kallon wajen da yake a kwance, da gaske yake kenan ba zai maida ita gida ba, me zata ce wa aunty? Gashi bata fito da waya ba balle ta kira, tana nan a durkushe a wajen cikin zulumi gashi ta gaji da kukan da bata san ma'anar sa ba. Shiru tayi cikin tunanin me ya kamata tayi, sai kawai ta yanke daukar wayarsa ko text ne ta turawa aunty, duk da tasan kila Amira ta fada mata amma tasan dole zata damu da bata dawo ba, ita duk nauyi da kunyar Auntyn ma take ji amma dole sai ta kira ta ko text message. Tashi tayi sad'af-sad'af ta nufi wajen da yake kwance, dama a gefen sa ya ajiye wayar, ta kai hannun ta zata dauka ya damke hannun yana bud'e idon sa, suka had'a ido da sauri tace


"Aunty zan kira." 


Kallon bakin ta yayi, yaki sakin hannun ta, ya jawota jikin sa gaba daya yana matse ta, ya shiga wajen kiran ya kira Aunty duk da bashi da tabbas din batayi bacci ba a lokacin, kira daya ta dauka kuwa, yayi sallama ta amsa


"Aunty afwan na tashe ki kina bacci."


"A ah ban ma kwanta ba Tariq."


"Ok dama wannan ce take so zatayi miki magana."


"Jidda wai, ba komai mayi magana da safe kawai."


Bata jira yayi magana ba ta kashe wayar, 


"Kinga ni ko? Aunty ko yanka ki nayi na cinye ba zata ce min komai ba."


Ya rad'a mata a kunne, muskutawa tayi ya sake jawota yana hade ta da jikin sa.


"Ki yi bacci kawai dan ba tafiya zamuyi ba, ki barni zan samo solution yadda za'a yi, sai ki daina kuka dan an aura miki ni."


Daga haka be sake ce mata komai ba, ya rufe idonsa yana jin wani irin nutsuwa na saukar masa. Rufe idon ta, tayi kamshin turaren sa na cikata, tayi luf ko kwakkwaran motsi ta kasa yi, tana jin shi ya soma jan numfashi, alamun ya fara nisa a cikin baccin sa, kallon fuskar sa dinga yi, a hankali a hankali abinda take ji na rashin nutsuwa ya dinga gushewa, wata nutsuwa na maye gurbin sa.


***Idan tace ta san lokacin da bacci ya dauke ta, tayi karya, bacci tayi sosai irin wanda ta dade bata yi irin sa ba. Bangaren Tariq din ma haka ne, bacci yayi peacefully har yaso ya makara tashi. Shi ya fara farkawa ya dan janye jikin sa yana kallon fuskar ta, very cute da dan karamin lips dinta da ya dace da yar fuskarta. Duk da ta chanja masa sosai amma shi har yanzu kallon baby yake mata, dan a yanzun ma yar karama ya ganta a gabansa. Samun kansa yayi da yin murmushi ya tashi yaje yayi alwala yazo daidai saitin kanta ya shafa mata ruwan hannun sa a fuskar ta, da sauri ta bud'e idon ta, ta tashi zaune tana zazzare ido, tamke fuskar sa yayi, ya wuce gaba zuwa wajen da zai yi sallah, tashi tayi ta shiga toilet din tayi alwalar itama ta fito ta tsaya tana tunanin da abinda zatayi sallah dan mayafin kanta babu yadda za'a yi yayi sallah. 

  Yana zaune yana addu'a tunda ta fito, bata ce masa komai ba shima be ce mata ba, tana ta tsaye har ya gama ya taso yazo ya kwanta yana kulle idon sa


"Za.. n..yi.. sallah." Ta fada a rarrabe kamar me jin tsoro


"Yi mana." Yace still idanun sa na rufe


"Mayafi na ba zai ba." 


"Kinsan ba zai sallah ba amma kika yafa kattin banza da wofi suna kallanki?"


Ya fada a hasale tunowa da abinda ya faru jiya


"A cikin gida ne ai."


"Cikin gidan babu Maza? Ko muharraman ki ne? Eh?"


Yace yana tashi zaune, shiru tayi ganin daga magana har ya harzuko, kwafa yai ya tashi ya fita ya sauka kasa, ya samo mata madaidacin mayafi a wajen ma'aikata wajen, ya kawo mata ta yafa a kasa tayi rolling da nata, sannan tayi sallar. Ta zauna a wajen har gari yayi haske sosai, yana ta baccin sa hankali kwance. Baki daya hankalin sa yayi gida, tana ta sake-sakn ko ta gudu ne sai gashi an kirashi, ya sa hannu ya kashe kiran aka sake kira a karo na biyu, sai da ya dan ja tsaki sannan ya daga yana kara wayar a kunne


"Hello..."


"Tariq kana ina ne wai?" Muryar Mama ta fito ta cikin wayar har tana juyowa daga in da take zaune, dan bude idon sa yayi ya murza kansa cikin yanayin baccin dake kansa yace


"Bana gidan Mah, anjima zan shigo."


"Da gaske ne kenan" tace gabanta na faduwa dan taji Amira da Fauwaz suna maganar kasa -kasa


"Me?"


"Ba komai, kazo gida kawai inason ganin ka."


"Shikenan, I'm on my way." 


Ya katse kiran yana leko ta daga wajen da take zaune, ya d'an ya mutse fuska ya mike tayi saurin dauke kanta zuwa dayan side din, kamar be gani ba, ya shiga ya gyara jikin sa ya fito yace ta taso, da sauri ta mike har tana kusan bashi dariya.



***Mama na compound din zata fita Tariq din ya shigo, idon ta akan motar tana son gasgata abinda take gani, Jidda ce a zaune kusa dashi, jiri-jiri taji yana neman kayarda ita, kafin ma su gama parking tayi saurin shigewa ciki dan bata jin ko fitar zata iya a lokacin kuma.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links