SANADIN LABARINA 29

 



                  Page (29)


***Bin Baban yake a baya ran Baban a bace har zuwa wajen motar sa, dama mantuwa yayi ya dawo har ya ji maganar da Maman take, bude masa murfin motar akayi ya shiga, sannan yace Tariq din ma ya shigo driver kuma ya fita ya jira su a waje.


"Yanzu ni zaka watsawa k'asa a ido Tariq? Na nema maka auren yarinyar nan yau shekara guda, mahaifin ta ya bani wuk'a da nama, haka yarinyar da ba haifan ta nayi ba, ta karbi abinda nazo mata da shi sai kai? "


"Ba ki nayi ba Baba, na karba hannu biyu wallahi, nagode Allah ya saka da Alkhairi ya kara girma."


"Idan har ba k'i kayi ba, wacce irin magana naji kuna yi da mahaifiyar ka?"


Shiru yayi dan baya son fadin laifin Maman, girgiza kai Baba yayi yace


"Shikenan, kar naji kar na gani, ka fara shirye-shiryen daukar matarka."


"In sha Allah Baba,kuma dan Allah ayi wa Mama uzuri,zan yi kokarin fahimtar da ita in sha Allah."


"Mahaifiyar ku bata son gaskiya Tariq, uzuri nayi mata sau nwa ma, amma shikenan, kuyi magana da ita, Allah yayi maka albarka."


"Amin." Ya amsa, sannan ya fita daga motar driver ya shigo, yaja suka fice daga gidan tare da motocin DSS dake bin bayan Baban.


Wajen wasu kujeru ya nufa ya zauna, baya son wannan matsalar ta shafi zaman iyayen sa, dan haka ya zama dole ya karbi yarinyar ko da na wucin gadi ne, dan ba zai so akanta iyayen sa su dinga samun sabani ba. Yana zaune a wajen Fauwaz ya fito ya hango shi, sai ya taho ya zauna a gefen sa, dan be yi tunanin Tariq din yana gidan ba. Suna zaune iskar wajen na kada su, ta fito rike da hannun Usman da wata warmer madaidaciya, mayafi ta saka ta rufe kanta amma kana iya hango duhun gashin kanta, fuskarta fayau duk da k'asan zuciyar ta babu dadi, bata lura dasu ba, tafiyar ta kawai take kai tsaye zuwa part din Yaya, idanun sa akanta Fauwaz na ankare dashi, mikewa yayi ya nufe ta, ya kira sunan ta, waigowa tayi sai ta saki fuskar ta


"Ya Fauwaz.."


"Na'am, kin daina buyan?"


"Dama ba buya nake ba fa."


"Me kike?" Yace yana mika mata hannu, ta bashi warmer din hannun ta, mika masa tayi suka jera tana masa bayanin dalilin ta, wanda jin ta kawai yake amma ba wai ya gamsu bane.


"Kinga Ya Tariq chan ya kafe mu da ido,kar ki juya just pretend kamar baki ganshi ba."


"Dama ban ganshi ba ai, me yasa zai kafe mu da ido?"


"Oho." Ya d'age kafada yana murmushi, share zancen tayi suka shige wajen Yayan yana kallon su, kamar ya tashi yaje ya kwankwashi kan Fauwaz haka yaji, ya rasa me yasa amma yadda yaga suna magana da murmushi yasa duk yaji haushi ya tik'e shi, cigaba da zama yayi a wajen har ranar da tayi saura ta karasa mamaye wajen, zafin ta ya bige shi. Mikewa yayi yana zura hannayen sa cikin aljihun wandon sa, yabi bayansu zuwa part din Yayan dan zuciyar sa ta gaza hakuri sai yaje yaga abinda yake faruwa.

   

Dariyar Yaya ya jiyo har da kyalkyalawa tun kafin ya ida shiga ciki, daidaita fuskar sa yayi zuwa yanayin da ya saba a ko da yaushe, ya shiga da sallama amma ciki - ciki,dakatawa Yaya tayi da dariyar dama video take kallo a wayar Fauwaz na abin dariya.


"Malam Badamasi an karaso?"


Tace tana dariya, dariya Fauwaz yayi Jidda kuma ta dauke kanta zuwa wani shashen falon,  zama yayi yana zaro hannun nasa yana kallon wajen da take zaune, kallon kallo Yaya sukayi wa juna ita da Fauwaz kafin su kwashe da dariya, dariyar da ta saka Tariq din tsarguwa.


"Ina kwana?" Yace 


"Lafiya lou wallahi, kamar yadda ka ganmu ni da mutanen amana ta."


"Ke bakya gaida mutane ne?"


"Wai Jidda, ai bata son yawan magana kasan, kuma dai idan jinin ta be hadu da na mutum ba, bata masa magana ko Jidda?"


"Haka ne kuwa." Fauwaz yace, 


"Ok yayi kyau ai, ni dai Yaya karki manta da alkawarin da mukayi."


"Ina zan manta? Ka jira lokacin dai."


"Shikenan." Yace yana maida kansa jikin kujerar , mikewa jiddah tayi, ta gyara yafen mayafin ta, ta ce


"Yaya zan dawo anjima."


Jan numfashi yayi ya sauke da sauri, yadda muryar ta, ta doki kunnen sa. Hada ido sukayi, tayi saurin janye nata tayi hanyar fita da dan saurin ta. Kundin tunani ya fada bayan fitar ta, sai ya mike kawai be ce uffan ba, ya fice daga shashen. Tafawa Yaya sukayi da Fauwaz, 


"Kaga mutumin ka ko?"


" Wallahi Yaya, ke ai legend ce kinsan ta kan tsiya, wallahi ya Tariq ya fara bani tausayin dan yadda yake jin kansa da miskilanci jiddah oga ce, kuma tana da gudun zuciya tunda taji da bakin sa yana furta wannan maganar zaa sha wuya kafin ta dawo daidai."


"Su karata chan, idan suka tare zasu daidaita kansu, mu dai muyi iya yinmu mu hora shi sosai, sauran mu barwa jiddaa su karata."


"Kin san ta kan tsiya Matar nan."


"Dani yake magana ai, kunno min kallon nan na cigaba."


"An gama ranki ya dade."


Kunna mata yayi yace zai je ya dawo yanzu, yana fita ta sa hannu ta jangwale kallon gashi bata iya ba, haka tayi ta tabe-tabe har tazo kan video da yayi mata a airport da za'a chanja ta daga mota zuwa jirgi, a cikin jirgin har zuwa gida. Salati ta rafka wayar saura kiris ta subuce daga hannun ta, sai gashi ya dawo yana shigowa ta damke masa hannun riga 


"Ni zaka yaudara? Wayyo Allah."


Sai ta fashe da kuka


"Menene Yaya? Me ya faru?"


"Ubanka ne, wallahi sai yazo da kansa ya raba ni da kai yau, sai da nace maka bana so, bana so, amma saboda ka raina ni..."


"Wai menene Yaya?" Ya yi dabara ya zame rikon da tayi masa ya karbi wayar sa,


"Waye ya saka ni a jirgi? Waye idan ba kai ba? Waye?"


"Auw wai magaanar jirgi ne Yaya? Yaushe kika shiga ni bansan zancen ba."


"Video din menene a wayarka? Ni zaka rainawa hankali?"


"Video ni? Yaushe akayi? Bansan maganar me kike ba fa Yaya."


"Idan yazo sai kayi masa bayani, ita Jiddan zTa shigo ne wato har da ita za'a hada baki a kassara min rayuata?"


"A ah fa, ba laifin jiddaa, tunda dai kin riga kin ga video din ba amfanin boye miki, maganin bacci na baki aka saka ki a jirgin."


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wayyo ni Hajara, ni kake so kaga baya ko? So kake ka kashe ni, na shiga uku na lalace Wayyo."


Gwalo yayi mata, ya fice da sauri tana kiran sa ya gudu yana dariya. Kuka ta shiga yi wiwi tace Usman yaje ya kira mata Anty, yaje zai gasu sun dawo tare da saurin ta, tana zuwa tace ta kira mata Baba yazo yanzu yanzu Fauwaz yana son ganin bayanta, duk yadda Aunty taso ta tsaya suyi magana ta fahimci me ke faruwa amma kemaimai taki sai kuka take tana fece hanci, Baba yadda Aunty ta iya dole ta kira Baba be dauka ba dan dama yace suna da meeting, hakuri ta dinga bawa Yayan har ta samu ta lafa da rikicin, ta lallaba ta, ta zauna taje ta kawo mata kunun ta tasha ta kunna mata kallo, sannan ta samu ta bar maganar kafin Baba ya dawo.


   Tana zuwa daki ta cire mayafin ta jefar akan gado ta kwanta rigingine, duk yadda taso ta danne abinda yake cin ranta ta kasa, gashi bata so Aunty ta sani dan zata shiga damuwa ne, kuka take so tayi amma ta kasa,sai ta dauko wayar ta, ta kira Safeera duk a kokarin ganin ta dauke hankalin ta baki daya, sun jima suna hira kafin suyi sallama, ta samu relief sosai duk da ba maganar sukayi ba, amma dai a kalla ta samu wadda zasuyi hira har ta fahimce ta.


***Tun bayan ya baro wajen Yayan ya fice daga gidan, dan yana da abubuwan da zai yi masu yawa kafin ya fara aiki sosai dan tuni yayi accepting din offer din Air Canada, one of the best airlines in Canada. Aikin pilot yana bukatar time and dedication, with alot of commitments duk da haka dai shine burin sa, yanzu haka zuwan nan da yayi jinsa yake a takure, ya saba ko yaushe suna sama kamar tsuntsaye. 

   Yana hanyar dawowa Mama ta kira shi, ya daga yace mata baya gidan dan baya son haduwar su a dan wannan lokacin, dan baya son matsala tsakanin ta da Baba, yafi so ta kwantar da hankalin ta, shi zai yi abinda ya kamata.

   Yana shigowa gidan suna kokarin komawa wajen Auntyn ita da Amira, a gaban su yayi parking bayan ya haske su da hasken fitilar motar, bud'e murfin yayi ya fito be ko kashe motar ba, Amira ta gaishe shi da sauri, ya amsa yana jiran yaji itama da gaishe shi, amma sai yaga ta share tana kokarin cigaba da tafiya dan barin wajen, ransa ne yaji ya baci, dama ga haushin abinda Yaya tace dazu wai idan jinin mutum be hadu da nata ba, bata magana, baya son raini sam me yasa ba  zata gaishe shi ba, me yasa ba zatayi masa magana ba. Ganin tana kokarin barin wajen dan har tayi taku kusan uku ya sakashi sa hannu ya damko nata hannun ta, kamar wanda aka jonawa shokin haka suka ji a lokaci daya, ya kafe ta da idanun sa dake sata diriricewa 


"Me..ne.. ne?" Tace a duburburce, 


"Rainin hankali." Yace a hankali, bata ma san me tayi ba?


"Dan... Allah ka cikani zafi." 


Ta nuna masa hannun nata da ido, dan sassauta mata rikon yayi,ya cigaba da kallon ta, shi sam yanayin da take zarya a cikin harabar gidan dake cike da ma'aikata da mutane mabanbanta shine be yi masa ba, ba kuma wai kishi yake ba, kawai dai be ga amfanin hakan ba tunda dai ai ko ba ya son auren dai amma akwai igiyar sa akanta, yanzu ma mayafi ne yalolo a iya saman kanta, duk da kayan jikin ta basu da aibu amma baya son hakan, ko su Fauwaz ne baya so suna mingling ta bari idan aka warware auren nasu sai tayi duk abinda ma taga dama be damu ba.

   Tuni Amira ta cikawa wandon ta iska, dan ta lura Ya Tariq din ma ya manta tare suke da Jiddan, sake maimaita ya cikata tayi tana kauda fuskar ta, dan ta rasa dalilin da yasa yake shigar mata rayuwa, tana iya kokarin ta na ganin tayi nesa dashi amma yana sake shigowa yana dagula mata lissafi


"Anki a cikakin."


 Yace yana hade rai, kokarin kwace hannun ta shiga yi, wanda ko zaa hada irin ta goma basu isa su kwace ba, dariya ma ta so bashi yadda take ta kicin-kicin kwace hannun nata, sai zuciyar sa ta raya masa wani abu, be yi dogon tunani akai ba, kawai ya bi umarnin zuciyar tasa, ya jata ya bud'e murfin motar ya tura ta a ciki, ya shiga ya juya ya sake ficewa daga gidan.

  Uffan bata ce masa ba, ya dinga gudu da ita akan titin, kanta na kallon window lokaci zuwa lokaci tana saka hannu ta share kwallar da take zubo mata. So yake ta bude baki tayi masa magana, ta roke shi ya tsaya ko tace ya maida ita gida amma kemaimai taki cewa komai, kamar zai yi hauka haka yake ji, be taba ganin miskilanci irin wannan ba, duk yadda ake fadan nasa ta taka shi ta shanye dan shi ya rage kusan kaso goma a ciki bayan tafiyar sa. Gajiya yayi da zagayen ya samu gefen wani restaurant yayi parking, suka zauna a motar kawai, zaman da ya haifar masa da wani yanayi me wahalarwa. Karkata zaman sa yayi ya juyo yana kallon wajen da take zaune, ita kuma tana kallon waje taki yarda ko sau daya ta kalli ciki dan zuciyar ta, tayi masifar yin weak.


"Jiddaa..." Ya samu kansa ta kiran sunan ta, wanda shi kansa be san dalilin kiran nata ba, kasa amsawa ba kuma wai dan tana sani ba, sai dan ba zata iya amsa masa ba, tana bud'e baki kuka ne zai fito, ita kuma bata so yaga gazawarta. 

  Dunkule hannun sa yayi, ya daki sitiyarin motar, sautin kukan ta ya shigar masa har cikin kwakwalwar sa, baya son kukan ko kad'an, kuma be ga wani babban dalili da zai sakata kuka ba, tunawa yayi ranar da ya ganta a kitchen tana kukan nan, tabbas akwai babban abinda yake damunta, toh ko bata son shi ne? Sai yaji gabansa ya fadi, tsoro ya shige shi. Cigaba da kukan tayi a hankali bata san yana jin ta ba. Ji yayi kamar ana fuzgarshi zuwa gareta, ya dinga matsawa har ya matso daf da ita, har tana jin hucin numfashin sa, hade da kamshin turaren sa da ya kara karfi saboda matsowar da yayi kusa, bata san haka ya zo daf ba, ta juyo da nufin ganin abinda yake yi, ba tare da tunanin komai ba, ya rungumeta yana zagaye ta da hannun sa zuwa cikin fafffadan kirjin sa.

[

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links