SANADIN LABARINA 28


 Page (28)




_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._


_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_


_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_


_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_


_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_


_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ 


_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_


_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_


_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_


_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._


_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_


_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_


_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_



_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_



***Kamar wanda aka dasa a wajen haka ya tsaya k'yem, tun da yake, tunda yake a rayuwar sa be taba ganin gashi irin wannan ba, yana yawan imagining mace da long hair amma not this long, daga ganin shi zai yi dadin tabawa. Sam bashi da cika bare yawa, sai tsayi da tsantsi da baki. Yana tsaye yana shawarar abinda ya kamata yayi, duk da ya gaza gasgata zuciyar shi cewa ita ce, that slim girl da yake ganin ko motsi tayi da yawa zata iya ballewa, duk da hr yanzu she's slim amma kuma she's curvy, irin yadda yake so da muradin matar da yake so, amma kuma ba wai son ita Jiddan yake ba, kawai dai she possess some qualities da yake so a wajen mace. Tunawa yayi da bata ko gaishe shi ba, bare ta bude baki tayi masa magana sai ma wuce shi da tayi kamar bata lura da existence dinsa ba, ransa ne yaji ya baci, ya bar kofar ya nufi hanyar da tabi ya tarar da daki daya a wajen, ya tabbatar nan ta shiga, knocking yayi a kofar jidda dake durkushe a wajen tayi saurin kallon kofar, tunanin ta Aunty ce, tayi saurin saka bayan hannun ta, ta goge fuskarta sannan ta bud'e kofar tana sauke kanta k'asa kar Aunty ta gano wani abu.


"Baki iya gaisuwa ba?" Yace bayan ya sake kare mata kallo, da sauri ta dago ta kalle shi, taga ya zura mata ido, saurin dauke kanta tayi bata ce masa uffan ba


"Kina kallo na, amma ko ki gaishe ni, ko ba'a koya miki gaisuwa bane?"


Nan ma dai shiru tayi masa, hakan ya sake kular dashi, ya fizgo hannun ta, tayi saurin janye wa tayi baya da sauri, ya samu damar shigowa dakin yana kallon ko ina a cikin dakin, idon sa ne ya sauka akan abincin dake saman bedside drawer, ya nufi wajen ya dauki tray din, ya samu waje daga gefen gadon ya zauna ya shiga cin abincin yana kurbar lemon kwakwan yana satar kallon ta, tana tsaye a wajen da take bata motsa ba, bata kuma ce masa ci kanka ba, yaci abincin sa ya koshi yana ci yana more kallon ta, ba tare da ta sani ba, haka shima ba tare da ya san abinda yake ba. Tunanin sa ne ya kawo masa, ya tuna me ma yake a cikin dakin ta, baya son raini kwata-kwata, sai gashi yana kokarin siya ma kansa raini da kudin sa, ficewa yayi be sake ce mata komai ba, tayi saurin rufo kofar yana fita, yaja dan siririn tsaki ya fice daga part din.


*** A zaune ya samu Fauwaz yana waya, ya watsa masa wani kallo yayi wucewar sa bedroom din sa, saurin katse kiran Fauwaz yayi, ya tashi yabi bayan sa, ya tarar dashi yana cire kayan jikin sa


"Ina ka shiga ne? Tun dazu nake jiran ka gashi wayar ka, ka barta a nan."


"Ina ruwan ka da in da naje? Yace yana rataye rigar sa a jikin hanger ya rage saura singlet kawai da dogon wandon


"Na zata wallahi ba zaka dawo yau ba, ina ta tunani gashi Mama tana ta jiran ka."


A gabansa ya tsaya bayan ya jawo towel sabo daga cikin closet dinsa, ya rataya a kafadar sa


"Yanzu ace har da kai, za'a yi min irin wannan auren a rasa wanda zai fada min."


"I'm very sorry, amma kaima kasan babu wanda yake going against maganar Baba, kuma kai ba kowa ma kake kulawa ba ko da a family din su Mama ne, da nasan definitely wani sai ya fada ma, mu kuwa ba zamu ketare maganar Baba ba, har Mama da taso nuna bata so sai da suka samu matsala akan haka."


"Akan auren?" 


"Yes, akan auren wallahi."


"This is serious."


"Shiyasa nake so ka tsaya muyi magana, duk da naga dazu ranka ya baci sosai, amma nasan ba zai yi lasting ba, just hear me out."


"There is no need ai, Baba ya fada min komai, so ka barshi kawai."


Sai ya juya yayi shigewar sa toilet, dan ji yake kamar ya shekara be wanka ba. Yana wankan yana tunanin fuskar ta, wadda ta tsaya masa a ko ina, mamakin kansa yake yi, har ya gama wankan ya dauro alwala ya fito, ya shirya cikin kayan baccin sa, ya feshe jikin sa da turaren Versace collection, ya fito falon ya dauki wayar sa ya sake komawa ciki ya rufe kofar ya rage hasken dakin zuwa me duhu, yayi relaxing akan couch ya kunna datar wayar sa yana so ya duba Ishaq. Ya dan dau lokaci akan wayar yana kallon messages din Yasmin na popping a saman wayar ya share be duba ba, ya saka wayar a flight mood ya kwanta bayan ya karo karfin A C din dakin saboda yadda yake da jin zafin gaske, gashi ya saba sosai da yanayin sanyin kasar da ya baro. A tunanin sa yadda ya dauko gajiya yana rufe idon sa bacci zai dauke shi, amma sai ya samu kansa da kasa baccin kwata-kwata, ya runtse idon sa ya bude amma still baccin yaaki zuwa kemaimai. Mikewa yayi ya kunna hasken dakin ya fito da system dinsa domin ya samu ya mantar da kwakwalwar sa tunanin da take ta kokarin turo masa, ya dade nan ma amma babu wani progress, tunanin ta ne yake neman damun sa, dan ko dan runtse ido yayi sai ya hango ta, a tsaye a kitchen din nan tana jan ajiyar zuciya, duk da be san dalilin kukan nata ba, amma ya taba shi sosai, wanda har yake jin da ya sani ya tambaye ta dalilin kukan nata, duk da baya jin akwai wani abu da zai iya mata bayan tambayar.

   Tunawa da yayi be yi shafa'i da wutri ba, yasa shi kashe system din da saka ran kila dan be yi bane yasa ya kasa bacci amma yanzu tunda ya tuna yana idarwa yasan zai kwashe shi baccin. Da wannan tunanin yayi sallar ya sake kwantawa amma dai still ba wani progress, tsaki yaja ya zura slippers dinsa ya fito, ya wuce Fauwaz a falon yana wani aikin cike cike a system, ya bishi da ido har ya fice.

   Harabar gidan tana nan kamar rana saboda hasken da ya mamaye ilahirin gidan, be san dalilin da ya fito dashi ba, be kuma san wajen wa zai je ba, ya samu kansa kawai da hakan ya dinga zagaye compound din kamar me gadi, idanun sa na kan part din zuciyar sa na fizgar sa akan ya je, ya shiga amma ya daure, sai da ya gaji da zagayen sannan ya koma ciki ya sake dukunkunewa a cikin blanket, ya samu da k'yar baccin ya dauke shi bayan ya cika kansa da tunanin ranar da duk wani abu da ya wakana a ranar.

    


***A makare ya tashi dan saura kiris ya rasa sallah a masallaci, dan sau biyu Fauwaz na tashin sa amma ya kasa tashi sai da yaji da gaske idan be tashi ba zai rasa sallar sannan ya taso yayi alwawar a gurguje yafita zuwa masallaci, ana sallar ya dawo daki saboda wani irin bacci da yake ji. Yana kwanciya ya koma baccin wanda har sai da rana ta daga sosai sannan ya tashi, shi din ma aiken Mama ne ya sashi tashi dole dan ta matsu yazo taji yadda aka kare duk da bata taba tunanin akwai wanda zai masa maganar nan a jiyan ba ganin ya dawo kuma ya gaji, ta san kuma basu hadu da Baba ba dan late Baban ya dawo.

    Wanka yayi a gurguje, ya nufi part din Maman, ya tarar da abincin sa achan ya dan yi breakfast din sama-sama sannan suka zauna da Maman ta dan bugo cikin sa dan taji yadda ake ciki


"Akwai wata magana da kukayi da wani bayan dawowar ka ne?"


"Magana?" Yace kamar me nazari, 


"Eh kamar maganar aure haka ko wani abu."


"Oh eh, Baba yayi min magana."


"Yace maka me? Yaushe ma kuka hadu dashi?"


"Jiya very late, yayi mun maganar."


"Ina fatan baka amince masa ba, dan nasan babu abinda zakayi da wannan yarinyar me kama da sadakar yalla, kafi karfin ta nesa ba kusa ba, saboda haka bana so, ban amince zaman ku a karkashin inuwa daya ba."


"Mama?" 


"Kwarai da gaske bana son auren, karfi na kawai akafi dan an hada ni da mahaifin ku,dan haka tunda kai na isa da kai, inaso ka sakar musu 'ya, dan bana kaunar ta ko miskila zarratin wallahi,idan yaso koma wace sai ka samo kuyi auren ku".


"Tunda ba kya son ta sai ki hanata numfashi Aisha."


Mikewa tayi Tariq din ma ya mike da sauri suka kalli kofar da Baban ya shigo, kofar baya da ya saba shigowa part din. Da safe Mama taji fitar sa dan da wuri ya fice daga gidan bata kuma zata ya dawo ba, kunya ce ta lullube ta, ta rasa in da zata saka kanta dan ba haka taso ayi ba, ya akayi ma bata ji bud'e kofar ba sai shigowar sa kawai


"Nace tunda bakya son ta, sai ki katse mata numfashi."


Hanyar ficewa Tariq ya nema, Baba ya buga masa tsawar da tasa shi kasa kara ko step daya


"Wallahi wallahi wallahi, kaji rantsuwar dan musulmi ko? Wallahi ka kuskura, ka saki Hauwa'u wallahi babu ni babu kai, kaji na fada maka."


"Ayi hakuri Baba."

 

Ya russunar da kansa k'asa


"Ke kuma, ko ciwon kai Hauwa'u tayi sai na tuhume ki, dan bazan kara yarda dake ba, ni ne ubanta dan haka zan yi duk yadda zan yi na kare ta daga sharrin ki, mutuniyar banza."


K'ala Mama bata ce ba, ya juya ya fice Tariq ya bi bayan sa da sauri

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links