SANADIN LABARINA 26


  Page (26)




Tana tsaye a gaban mirror taji shigowar motocin alamun sun dawo, gaban ta ne ya fadi cikin ta yayi wata irin murdawa, ji tayi kamar tana bukatar shiga toilet amma tasan irin wannan yanayin ne da mutum yake tsintar kansa when he's nervous. Tafin hannun ta ne taji yana mata wani iri sai kuma tafi kafarta, samun waje tayi ta zauna da sauri tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, ta dan dan mintuna a haka kafin ta tashi ta karasa shiryawa cikin sabon kayan ta riga da skirt, ta yafa madaidacin chantilly akan kayan nata, ta feshe jikin ta da turare me sanyin kamshi, wanda baya hawa ka.


***Kafafunsa ya zuro sanda suka iso cikin gidan nasu, idanun sa na kan gidan da yanayin tsarin gine-gine wanda yayi saurin banbance kowanne,.


"Ina wajen Mama?" 


Yace bayan ya fito daga motar, da hannu Fauwaz ya nuna masa, yana kokarin bawa yaran dake harabar gidan masu kula da gyaran compound din da duk aiken gidan jakunkunan Tariq din dan kai mishi su part dinsu.


Takawa ya shiga yi zuwa part din Maman wanda tuni su Maryam sun isar mata da labarin isowar sa, tana tsaye a tsakiyar falon ya turo kofar ya shigo, ta saki baki ganin wani irin chanjawa da Tariq din yayi. Murmushi ya sakar mata yana karasa ciki da dan saurin sa, ya russuna ya gaida Maman bata san lokacin da ta rungume shi ba.

  

"Welcome home son, sannu da hanya."


Ta sake shi tana fada, sai kuma tace ya zauna, ya zauna bayan ya dan kalli falon. Gaishe ta ya sakeyi sannan sukayi maganar bayan rabuwa, ta saka aka kawo masa ruwa da juice yasha ruwan kawai tace sauran abincin suna chan a part dinsu aka jera masa, mikewa yayi yana zuwa hannun sa a cikin dogon wandon sa yace zai je ya huta zai shigo anjima. Har kofa ta raka shi cike da jin dadin ganin sa.

  Yana fita suka hadu da Fauwaz ya gama shigar masa da kayan, ratayo kafadar sa yayi ya yi maganar a hankali


"Rakani na gaida Aunty, sai Yaya daga nan ina so na huta dan wani banzan transit mukayi a Ethiopia wanda yayi draining baki daya energy dina."


"Wai, matsalar kenan dama, ina zamu fara zuwa?"


"Wajen aunty, dan Yaya idan naje surutun ta nasan zai kara min ciwon kai, kaga ina fitowa sai naje na huta gaba daya."


"Allah ya dawo damu ai, kai da Yaya ai kamar Tom and Jerry, Jidda ce kawai daidai da ita ta iya lallaba ta wallahi."


"Jidda?" Ya kira sunan kamar me tunani, sai kuma yace


"Ohh, that slim girl?"


Dariya ya bawa Fauwaz,be bashi amsa ba saboda karasowa part din Auntyn da sukayi, suka shiga Fauwaz na gaba yana bin sa a baya yana nazarin part din shima, kamshin abinci ne ya daki hancin sa, irin kamshin da be taba jin irin sa ba, lumshe idon sa yayi ya bude sanda Auntyn ta fito fuskar ta cike da fara'a tana masa maraba, murmushi yayi ya amsa sannan suka dan taba hira, yace zai dawo ya mike sai kuma ya tsaya


"Aunty wannan kamshin abincin, inason naci"


"Naka ne ai, tunda dan kai Jidda tayi."


Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, sai kuma ya kada kansa alamun ok, sannan yace 


"Zamu ci dadi."


"Sosai, jiddah expect ce in dai girki ne."


Ya Fauwaz ya kara dan duk ya sake samun hanyar convincing dinsa. Gid'a kansa yayi, yace suje suka fita sai part din Yaya, wadda ta cika tayi fam dan tunda tasan sun shigo take zurara ido a hanya amma dan wulakanci sai yaje ya gaida uwarsa sannn zai zo wajen ta. Suna shigowa ta tsuke fuska kamar ba jiran shi take ba, kallon fuskar ta yayi sai ta bashi dariya ganin yadda tayi kicin kicin da fuska ita a dole tayi fushi, fushin da be san na menene ba.


"Ai da ma baka zo ba, tunda sai ka gama gaida iyayen ka zaka zo waje na."


"This woman and her wahala." 


Yayi maganar a kasan makoshin sa, ya zauna a gefen kafarta yace


"Yi hakuri bazan kara ba."


"Dama ba laifi kayi ba..." Tace kunya kuma sai ta kama ta yadda tayi masa bayan dawowar sa kenan


"Mun same ku lafiya?"


"Alhamdulillah, Allah ya kaddara saduwar mu, na zata fa da sai mun mutu zaka zo taaziyya."


"A ah, ban isa ba." Yace yana murmushi


"Ikon Allah, ashe dama kana murmushi, dama dan uwanka yana murmushi kai." Ta kalli Fauwaz tana rike haba


"Dariya ma har da kyalkyalawa."


"Ah lallai magani yayi aiki, dole na kira Malam na sake godiya, ya kuma sake aiko maka da wani rubutun."


"Ai naji dadin maganin nan Yaya, nagode sosai."


Yace yana biye mata dan ya gano da dadewa wahalar da kansa kawai yayi da ya kasa fuskantar halin Yayan


"Ba komai ai yiwa kai ne, ka dai samu daddad'an labarin bikin ka wajen ita uwar taku ko?"


"Biki? Wanne biki Yaya?"


"Bari Yaya zan masa bayani kinji?"


"Wanne biki ake magana Fauwaz?"


"Muje part din mu, muyi magana."


"Ok." Yace a sanyaye, ya tashi suka fita, ita dai Yaya ko a jikinta, murnar ta kawai take tasan kuma duk tsiyar Tariq din ba zai taba kin jiddaa ba.

   

  Suna shiga part din nasu Fauwaz yayi wa Jidda text wadda take rufe a daki tun shigowar su wajen Auntyn har suka fita, tana jiyo echo din muryoyin su amma ta kasa fitowa


"Kawo ruwa part dinmu jiddah." Ta karanta text din, sai ta mike tana sake kallon kanta a mudubi, kafin ta fito ta shiga kitchen ta dora ruwa akan tray tare da cup ta fita zuwa part din su Fauwaz din.


    Ransa ne yayi kololowar tun kafin ma Fauwaz ya gama maganar, ya dakatar dashi ba tare da ya gama fahimtar abinda ma yake nufi ba, abu daya kawai ya tsaya ya fuskanta shine ana so a hada shi aure da figaggiiyar yarinyar nan jidda, be ma ji karshen bayanin ba, bare yaji har ma an daura musu auren shekara daya kenan. Hannu yasa ya dakatar da Fauwaz din ta hanyar cewa


"Ya isa!!!"



“Ya Tariq amma…” Fauwaz yace zai cigaba da bayanin


“Look fauwaz, ba zan iya auran yarinyar nan ba, tayi min kankanta da yawa, plus bata cikin spec dina gaskiya. Bana so mace ta cika siranta da yawa, plus she’s young. Very very young da rainon ta zanji ko da aiki na!?”


“I know, amma when last kaga Jidda? When last ka ganta face-to-face?”


“Ba zan iya tunawa ba, infact na manta kamar ta ma baki daya ni. So it’s better kaje ka sanar da Yayah, ba zan iya ba gaskiya, gobe goben nan zan koma in da na fito, daga dawowata? Haba!”


“Calm down and give it a second thought, karka yanke shawara base on abinda ka sani a baya, jiddan da ka sani shekara biyar baya ba itace wannan Jiddan ba! Ka daure ka ganta.”


“Fauwaz!”


Sai ya mike tsaye


“Kana bata bakin kane kawai, ba zan iya ba gaskiya, ba zan daukar ma kaina abinda na san ba zan taba iyawa ba.”


Mikewa shima yayi, yana girgiza masa kai, zai yi magana ya daga masa hannu


“Bana son sake jin komai. Ya isa haka nan, ba zan taba iya soyayya da ita ba, bare har ta kai ga maganar aure! Never!!!



****Tray din ruwan da yake hannun ta ne yake neman subucewa, tayi saurin rike shi hawaye na saukowa a kuncin ta, ya zatayi da auren sa da yake kanta? Ya zatayi da rayuwar ta yanzu kenan? Innalillah wa inna ilaihi raji’un. Ta shiga maimaitawa. Takun takalmin sa ne ya iske ta, tayi saurin matsawa jikin dan corridor din dake jikin dakin ta makale, fuskar sa a hade take tsaf, yana cikin shigar farar tshirt wuyan sa sakale da necktie navy blue sai dogon wandon chinos dake sanya a jikin sa. Dogo ne sambal, kuma giant na ajin karshe, zuwa yayi ya wuce ta, ba tare da ya lura da ita ba, tana jin kiran da Ya Fauwaz yake kwala masa amma yayi biris kamar be ji ba. Ya wuce kansa a gaba cikin yanayin da ta kasa hange ko hasashen sa. Ji tayi tamkar kafarta ba zata iya daukar ta ba, duniyar na juya mata, shekara guda kenan tana dauke da igiyar auren sa, igiyar da ta raba ta isma’il me tsananin son ta da kaunar ta, ta zabi zaman dakon jiran shi, duk da bata da yakinin abinda zata tarar daga gareshi. Zuciyarta tayi nisa a kaunar sa wanda har take jin bata da wani katabus idan har babu shi. Me yasa zuciyar ta, ta zalunce ta? Me yasa ta sakata kaunar wanda baya son ko ganin ta? Lallai zuciyar ta, ta zalunce ta zalunce mafi girma.


Zaman dirshan tayi a wajen, cup din da ruwan kowanne yayi nasa wajen, Fauwaz ne ya fito, ya ganta a wajen, yanayin da take ciki ya tabbatar masa da lallai taji maganganun su, durkusawa yayi a gabanta cikin yanayin tausayinta, dan yasan yadda take son Ya Tariq, kuma yasan sune ummul abaisin gina mata soyayyar shi a cikin zuciyar ta, shi da Amira sune suka bata hope, suka dora ta akan turbar da a yanzu shi kansa be san da wanne irin baki zaiyi amfani wajen gyara matsalar ba.


“Jiddah.”


Ya kira sunan ta cikin yanayin da shi kansa yasan abinda zai fada bashi da wata maana, dago manyan dara-daran idanun ta tayi, wanda a kullum suke cike da wani haske me kyawun gaske, sai dai a yanzu sun rine sun koma wasu iri na daban, tamkar ba su.


“Nasan kinji komai da muka ce, bansan me kuma zan ce miki da zai karfafa miki guiwa ba, amma na miki alkawari sai Ya Tariq ya kawo kansa wajenki, begging you on his two knees akan ki taimaka masa. Nayi miki wannan alkawarin, sai ya sauke duk wata izza da yake ji, sai ya ajiye duk wani self respect nasa, ya nemi soyayyar ki.”


Girgiza masa kai tayi, ta mike tana karkade jikinta, ya taimaka mata ya dauki tray din yana leka fuskar ta da ya kasa gane ainihin abinda yake faruwa a cikin zuciyar ta


“I’m so sorry Jidda.”


Murmurshi ta sakar masa wanda yake dauke da abubuwa masu yawan gaske, ta shiga takawa zuwa cikin gidan, gefen ta ya tsaya suke jera yana rike da tray din, suka shiga cikin gidan zuwa part din antyn, a saman madaidacin fridge din dake falon ya ajiye tray din ita kuma tayi saurin shigewa dakin ta, tana shiga ta kulle kofar ta jingina da bayan kofar zuciyar ta na bugawa da karfi da karfi


“Ina son ki Jiddah, ina son ki fiye da yadda nake son kai na, dan Allah ki ceci rayuwata ki so ni ko da kwatan son da nake miki ne.”


“Kayi hakuri isma’il, ba zan iya ba, ba zan iya ba.”


“Shikenan Jidda, shikenan sai watarana!”



Kalaman Isma’il na karshe kenan, anya ba alhakin sa bane zai fara bibiyarta? Anya? Ashe haka kake ji idan wanda kake so ya furta maka kalmar baya son ka? Haka isma’il ya ji? Mutumin da ya so ta tun tana yar kauyen ta? Ya so ta tsakani da Allah ba dan wani abu da ta mallaka a jikin ta ba, anya bata cuci kanta da rayuwar ta ba?


Dafe kanta ta yi da yake barazanar tsinkewa, ta lallaba zuwa gaban mudibi ta tsaya tana sake kallon kanta da kanta! Duk in da ake so mace ta kai a haduwa da cika ta san ta kai, amma sai dai kash!


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links