FARHATAL QALB CHAPTER 24


 PG:24_



   Tana karasawa ta yi hamdala . Ta nufi wajen sink ta wanko hannunta da hand wash din da Maa ta nuna mata dazu. 


Dusters din da suka baci ta diba. Bayan ta mayar da komai mazaunin sa. Ta tattare kitchen din ta yi mopping. Sannan ta fita da moper din da bokitin zuwa famfon baya. Ta wanko su tas ta shanya.


Ta koma kitchen din. Wani spray ta gani na saka kamshin gidah na kamfanin da ta gani a rubuce na (yerwa incense and more) Faffesa shi tayi. Baki dayan kitchen din ya gauraye da kamshi.


Ta dakko food flask din abincin ta riqe a hannun ta. Maa ta shiryo cikin doguwar riga ta rufe jikinta da mayafin rigar. Tana hango Waheedah ta dashare hakora.


"Sakkowa ta kenan ni ma...Sannu da kokari."


"Na dauraye su duster din nayi mopping kitchen. Akwai wani abun da za'ayi?"


"Sannu da kokari yar albarka. A'a babu komai kin gama. Mungode kwaarai. Dan Allah kiyi wa Hadizan sannu. Yauwa ungo ki bata wannan maganin tasha. Har na tsawon sati daya. " 


Ta miqa mata wata leda mai dauke da magunguna. Ta cigaba da cewa,


"Na zana yadda zata sha kowanne."


"Tohm. Allah ya saka da alkhairi."


"Aamin. Amin. Nima fitar zanyi ai. Yaran duk suna wajen su Ummimi. "


Sai a sannan Waheedah ta daga kai ba kowa a parlorn da dinning area sai Haj Hameedan kawai. 


"Tohm sai da safe. "


"Yauwa Waheedah." 


A tare suka fita daga cikin sashen. Waheedah tayi hanyar gate don fita. Ita kuma Haj Hameedah ta nufi sashen abokiyar zamanta inda Ummimi suka sauka. 


     

××××


   Tanata sauri har ta kusa karasawa gidah taci karo da kawarta Basira.


"Kawata daga ina?"


"Daga gidan aikin Umman mu nake.. Kawalliya "


"Allah sarki Umma. Dazu naje dubuta ai ni da fannah. Awajen Najan Isubu naji."


"Eh wallahi zazzabi take "


"Allah ya bata lapia mai dorewa. Ciwon da zai sa Umma kwanciya ai babban ciwo ne."


"Wallahi kuwa ... Amin. Ya Innar ku?"


"Alhamdulillahi sunje dubiya unguwar yan Tasha"


"Okay Allah sarki..."


Jerawa sukayi suna tafiya suna hirar su ta kawaye .


Ta majalisar su Ibrahim suka ketare. Sun jeru samarin sunata hira. Wasu na danna waya. Wasu na cin masarar da suka tsayar da me masarar suna saya.


 Wasun su na shan shayin cikin wata yar karamar buta dake gaban su. Kamar ko da yaushe. Yayin da wasu daga ciki suke whot wasunsu kuma hira suke mafi yawan su kuma na danna waya. 


Matashi Ibrahim na cikin jerin samarin dake danna wayoyin hannun su. Sanye yake cikin yadi mara nauyi me layi layi. Kalar qasa. Ya kishingida yana mai duba wayar sa cikin nutsuwa. Kyakkyawa ne wankan tarwada mai matsakaicin idanuwa da dogon hanci. 


"Wohoho...." Wani daga cikin samarin ya furta. 


Dayan kuma ya shiga lakato tafun kafar Ibrahim . Cikin rada yake cewa,


'Ga takan, Ga takan...."


Ibrahim ya 'daga kansa a hankali ya sauke akan Waheedah dake tafiya ita da Basira. 


Tamkar an tsunkule shi haka ya miqe da sauri jikin sa tamkar mazari tsabar rawa. Yana mutuwar son Waheedah. Wani irin so yake mata wanda ba zaa iya fasalta shi ba. 


Ya tsallaka kwalabatin dake gaban sa. Abokan nata masa dariya. Yayi banza da su ya isa wajen su Waheedah dake tafiya.


"Waheedah... Waheedah .." Ya kira sunanta yadda zata iya jiyo sa.


Ja sukayi suka tsaya. Ya karasa yanata dashare baki yana murmushi.


"Ina wuni Ya Ibrahim?." 


"Lapia kalau Basira .."


"Ina yini...!" Waheedah ta gayshe shi cikin ladabi. 


"Alhamdulillah Waheedateey . Kaif? Ya komai.Tawan.." 


Basira ta yi yar dariya kafin tayi gaba ta tsaya daga can nesa. 


"Waheedateey....?!!" Ya sake jan karshen sunanta cikin wata siga ta soyayyah.


"Sauri na ke Ya Ibrahim ..." Ta bashi amsa cikin kosawa, Don sam batason kule kulen nan.


"Ance Umman ku batada lapia.... Ina ta son shiga na duba ta. Waheedateey, Kin ki bani chance.. Waheedateey inason naga mahaifin ki don ya bani dama na fara zuwa tadi wajen ki . So nake na aure ki Waheedateey kinsani tun ba yau ba ..."


"Ban gama makaranta ba. Kuma na gaya maka cewar inason na cigaba da karatu ko da na kare sakandire . A yanzu kuma gaskia ban kai shekarun da zan dinga zance ba. Kayi hakuri "


Ibrahim ya dafe kansa. Waheedah na gara rayuwar sa. Yan matan unguwar shura na macewa akan kaunar sa. Duk basa gabansa ita yake so. Amman kwata kwata ita din bata yin sa. Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace da ita 


"Zan bari ki karasa karatun sai muyi auren.  .... Sai ki cigaba da karatun a gidah na . Kinji ko?"


Waheedah ta sake gyara tsaiwarta da kular abincin da ke hannunta ahankali cikin nutsuwa tace da shi,


"Ya Ibrahim sai nayi istikhara naga alkhairi ne ko akasin haka? Sannan yanzu ba a aure gaba gadi Ya Ibrahim."


"Bangane gaba gadi ba Waheedateey. Ban isa auren ki bane ko kuwa ban kai matsayin auren ba?".


Waheedah ta girgiza kai kafin tace da shi,,


"Babu komai "


"No ban amince ba. Da magana a bakin ki Waheedateey.... Ni bansan me kike jira ba da ba zaki karbar kokon barar soyayya ta ba Waheedateey... Ga ni matashi mai jini a jika. Nayi karatu na har ya zuwa matakin NCE Waheedateey. Ni dan asali ne na fito daga dangi masu dattako da sanin ya kamata Waheedateey. Ina sana'a ta ba zaman banza nake ba. Zan iya riqe ki har karshen rayuwar mu Waheedateey... Ga Zainab yar uwar ki nan tana tadi da samarinta. Gidan ku daya. Yar uwar ki ce ta jini amman ni kinki bani chance ... Meyasa?? Uhm?" Ya fada cikin rada rada. Yayinda tururun numfashin sa ke dukan kofofin kunnenta.


"Kinyi shiru... Wace irin tsana kike mun ne.... Eh Waheedateey?"


"Ban tsane ka ba Ya Ibrahim. Komai lokaci ne ciki harda auren da kake fada. Idan Allah yayi ni mata ce agare ka . Wallahi dole sai na aure ka. Sannan rashin baka damar zuwa zance wannan raayi na ne na fuso na kammala karatu sannan. Don ba zan iya raba hankali na biyu ba... Ni da Zainab ba daya bane. Mu yan uwan juna ne amman masu bambamta halaye. Sai abu na karshe Ya Ibrahim kasan menene matsayin gene dinka? Ina nufin genotype ...Da sauran gwaje gwaje na lapia? Ba a tafiya kai tsaye ayi aure ba tare da gwaji ba."


Ibrahim ya furzar da iskar bakin sa. Cikin kufulewa yace,


"Waheedateey wannan maganar ta genotype yahudanci ce. Wani renin hankali ne yahudawa suka kawo shi don a hana musulmai raya sunnar manzo SAW. Renin hankali ne shiya sa ranar da ake gwajin nayi zamana a gidah ko kofar gida banje ba. Lapiyayye ne ni wallahi. Computer bata isa ta kawo mun karyar kanzar kurege ba.. "


Waheedah tayi murmushi kawai. Ta cigaba da tafiya. Ibrahim yabi bayanta da sauri yana cewa,


"Kinyi shiru .."


"To me zance? Ai ka gama magana. Ni kuwa ko lokacin aurena yayi bazan yi aure ba tare da gwaji ba. Domin cututtukan zamani sunyi yawa masu halakawa ko mutum yayita jinya har karshen rayuwar sa. Musanman ciwon sickle cell na amsosanin jini.... Tun yanzu nasan genotype di na. Don haka ba zan yi auren jelan asibiti ba da yardar Allah...."


"Abar maganar nan.... Yanzu dai yaushe zan zo na duba Umman ku?"


Waheedah ta girgiza kai kawai kafin tace dashi,


"Umma taji sauki... Mungode da kulawa." 


"Shikenan sai mun sake haduwa..."


Ya juya ya koma majalisar su . Ita kuma da Basira suka karasa layin su. Kowanne ya shiga gidan su ..


Umma Hadiza ta sake cika da mamakin abincin da Waheedah ta sake kawo mata. Tayita zuba addua tana yabawa Haj Hameedah da kokarin da bata gajiyawa.


Ta zubawa Marka aka mika mata. Dakyar Markan ta karba tana yamutsa fuska. 


Yayinda Umman ta rabawa su Kamal da Najan Isubu. 


Waheedah ta dauki food flasks din ta kai su waje ta wanke su sau 3 da omo ta dauraye su tas sai kyalli suke. Sannan ta mayar su cikin kwando ta lullube su. Kafin zuwa safiya ta mayar dasu gidan na The Adams family!!



❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links