🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌹🤱🏻WATA UWAH 🤱🏻🌹
🙆🏻♂️(RAYUWAR ABDUL) 🙆🏻♂️
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by
mommyn fareesa
wannan shafin nakine halak malak kiyi yadda kikeso dashi zqinab hamisu wada💓🥰
free 🅿️ 3&4
.......cikin wani yanayi meenah tace"haba goggo! alwalah d'in ma hanashi zakiyi yayi dan Allah? meyasa bakya yiwa yaya Abdul adalci?" fad'amun yadda zanyi dan ubanki"cewar goggo afusace tana tunkaro meenah dake tsaye"yah Abdul yamik'e tsaye zuciyarsa na wani irin zafi ya k'ak'aro murmushin yak'e yana fad'in meenah jeki Ida aikinki"goggo kiyi hak'uri zanje masjeed nayi alwalah d'in acan"yafad'a cike da ladabi"goggo taja tsaki had'e da cewa"ina ruwana ma da Inda zakayi?"ke kuma kutsugagga ki fita dg idona na rufe"zaki tafi ki bani waje ki idamun girkina ko kuwa?"hawaye na tausayin yah Abdul suka wankema meenah fuska"tana girgiza kanta tace"goggo Inda badan inada tabbas kece mahaifiyar muba danace ba kece kika haifi yaya Abdul ba.... ji kikeyi tass! goggo ta d'auke meenah da mari mai rai da lafiya tana mara dakk'uwa"yah Abdul ya girgiza kansa bece komaiba ya juya yafita"goggo ta dinga masifa da bala'i"meenah batace komaiba ta zuba ruwan tayi alwalah d'in tana kuka"kafin ta koma kitchen d'in ta duba girkin sannan ta wuce parlourn.....
bayan sallar magrib yaya Abdul yashigo cikin parlourn goggo"tana zaune kan kujera tana kallon tv kamar tasan me suke fad'a"sau 3 yanayin sallama Amma ta masa banza"k'asa kan carpet yazauna ya sunku yadda kansa ak'asa Ahankali yace"goggo sannu da gida!"kaga dan Allah bana son takura"akanme zakazo kamun zaune?"yah Abdul na k'ok'arin mgn meenah tashigo parlourn da plate d'in abinci a hannunta na shinkafa da miya da nama" ta ajiye gaban yah Abdul"wlh meenah idan bakiyi hankali daniba saina miki baki"dan ubanki dani dashi wa kikafi so?"haba goggo menayi kuma?"oh bakisan me kikayi ba kenan?meenah na k'ok'arin mgn sukaji sallamar yara suna fad'in ance gashi"washe baki goggo tayi tana mik'ewa tsaye" kamar zatayi tuntub'e ta fita tana fad'in da alama d'an albarkane yabayyanah"meenah ta girgiza kanta tana bin yah Abdul da yayi tagumi"da kallon tausayi yad'ago kansa suka had'a ido"d'aure fuska yayi yace"dg yanzun komai goggo zatamun ko zata fad'a akaina bance kisa mata baki ba"ki d'auki abincin ki mayar banaci"yafad'a murya adake"dukda yana jin yunwar amma bazai iya ciba"meenah na k'ok'arin mgn goggo ta shigo d'akin da kaya nik'i nik'i a hannunta tana fad'in wayyo Allah haihuwar mai arzik'i tayi arayuwa"dana haifi talaka gara na haifi mai arzik'i"yo miye ribar haihuwar fatararre Allah natuba?"ke meenah maza kwasomun sauran kayan can dake acikin baranda"meenah batayi mgn ba ta fita"yah Abdul yayi k'asa da kansa yana mamakin sbd bedashi kawai mahaifiyarsa ta tsanesa?"Assalamu Alaikum! cewar kabeer yana shigowa cikin parlourn"da kallo nabi d'an lelen na goggo wanda bbu alamar tarbiyya atare dashi"yana sanye da k'ananun kaya"jeans d'in yayi k'asa har boxer nashi ana gani"yabar uwar suma cike da kai"ya zauna gefen goggo yana fad'in my mom na sameku lafiya?"lafiya qlau kabeer ya habujan ?"sannufa da hanya d'an albarka"yauwa mom(haka yake kiranta sbd yafi k'arfin yace"goggo)kallonsa ya maida kan yaya Abdul yace"yaya sannu gida nasameku lafiya?"lafiya qlau kabeeru"ah ah dakata ! bana son rashin tsoron Allah akanme zaka b'atama d'ana suna??yazo baka masa mgn ba"sbd kana masa hassadar yafika"saidai shine yafara maka mgn"idan baza kace kabeer ba ka bari"basar kawai mom"cewar kabeer yana d'aga wa goggo hannu"hakan yayi daidai da shigowar meenah parlourn"yah Abdul beyi mgn ba sbd beson raini amma yaji haushin kalaman kabeer""itadai ta masa cin fuskar data keso zai hak'ura tunda mahaifiyar sa ce" amma bazai d'auki raini agun na k'asa dashi ba"ya mik'e tsaye yafita"goggo ta tab'e baki "meenah na dg tsaye tace"yaya kabeer sannu da hanya"yauwa sis"tayi d'an murmushi tana jawo plate d'in abincin da yah Abdul be tab'a ba zata ajiye agabansa"goggo tayi saurin dakatar da ita gun cewa"kinga ki canzo masa wani"tunda shi wannan zalamammen beciba"kabeer yyi saurin cewa" mom ta barsa gsky dan bazan iya cin girkin taba dan is local"ba girmana baneba ,wannan villager girl d'in tayi girki naci "abarshi naje restorent naci kawai"hmm yaya kabeer kenan! rayuwa batada tabbas"ada kafin kayi kud'in ince irin wannan abincin kakeci koma wanda bai kaisaba ko?"wata uwar tsawa goggo ta dako mata"bbu shiri tabar parlourn tana mamakin halin mahaifiyar tasu....goggo kuwa firan yaushe gamo sukayi tayi da kabeer kafin ana kiran isha'i yasanar mata zai tafi masaukinsa yahuta da safe zai dawo"dan baya kwana agidan Idan yazo sai hotel duk time d'in daya zo.....
bayan fitarsa ,meena dake zaune atsakar gidan ta share hawayen ta"ta shigo parlourn ta zauna ta dubi goggo daketa duba uban kayan shopping da kabeer yamata tace" wlh koda kasheni za'a yi bazan dena fad'in gsky ba "domin ana nuna banbanci sosai agidan nan k'arara"sannan na yarda da ake cewa" duk wanda yake da kud'i agdnsu to shine Alh komin k'arantarsa "gashi nagani anan gidan"kwata kwata yah Abdul ne babba agdn nan amma sbd bashida kud'i an maidasa k'arami! komai sai yah kabir shine na kirki me kyan hali mu duk b.....cikin tsawa goggo tace" wlh ko kimun shiru ko namiki shegen duka "ai dukiyar kabeer ta miki rana dan ubanki"tunda da ita kike ci dasha da hidimar karatunki"fita ki bani guri shashar banza kawai....
yah Abdul kuwa yana fita shagonsa na d'inki yanufa"gaba d'aya duniyar ta masa zafi"amma dukda haka ya fawwalawa Allah komai"shagon abud'e yake sbd wanda suke atare ashagon suna d'inki yafito"kasancewar akwai nefa shagon da haske"yana shigowa wayarsa nayin y'ar k'ara alamar shigowar message"musa abokinsa na zaune kan kujerar da yah Abdul ke zama"kallo d'aya yayiwa abokin nasa yasan yanada damuwa"d'an murmushi yah Abdul yasaki yana fad'in na hak'ura my jiddo nah"yafad'a yana koma karanta message d'in da jidda ta turo masa naban hak'uri da nuna kulawa"tab'e baki musa yayi sbd yaji abinda Abdul yafad'a"shifa harga Allah aransa" be son soyayyar Abdul da jidda sbd wasu miyagun halaye na jidda"saidai yanayin shurune dan yafahimci Abdul d'in na yiwa jidda wani irin zazzafan SO"wanda da wuya ya iya rabuwa da ita"
kallon tausayi musa yyi masa" dan kaf yasan halin da yah Abdul yake ciki da kuntatawar UWA! dan bayada wani amini sama dashi, sun yarda d junansu ,su kashe su rufe a tare.....
Ango Ango!! cewar yah Abdul yanajan sit ya zauna"musa na murmushi yace"bakada kirki abokina 3 days kenan rabona dakai"nadubaka ta online naga kajima baka hauba"hakane abokina"amma kana Ango miye ya fiddoka awaje?"gunka nazone ai"muje dg waje"okay yah Abdul yafad'a suna mik'ewa tsaye suka fita"nura dake d'inkinsa yatab'e baki"dan yatsani yaya Abdul dukda bai masa komai ba"hakanan yakejin zafinsa"bayan kuma yah Abdul d'in shine yanemi alfarma wa nura daya dinga d'inki ashagon bazai biya kud'in haya ba.....
suna fitowa musa yace"mutumin girkin amarya nazo muje kaci"bakada kirki Abdul"kaine babban abokina amma tun ranar daka rakani d'akin my hafsy baka koma zuwa ba"d'an murmushi yah Abdul yayi yace"kaidai ka godema Allah tunda kasamu Inda zaka huta"inama ace nine nasamu nayi auren nan abokina"in sha Allah kaima zakayi"ina jin tausayin duk yarinyar data fad'o hannunka idan kukayi aure mutumina"hmm! jiddah na kake tausayi ko?"shiru musa yayi sbd haushin jiddan yakeji ko yau yaganta tsaye da babawo"yaran dabaida tarbiyya sai shaye shaye dabin mata shine aikinsa"kayi shiru"wani abu na tuna"amma zan tambayeka"yafad'a suna tafiya anutse"musa yaci gaba da cewa"wai katab'a yiwa jidda zancen zaka turo magabatanka agidansu ?"Eh ina mata ko yau munyi maganar"metace maka?"yawo da hankali takemun amma yau dana mata mgn na nuna mata muddin bata sona tasanar mun kawai"sanin kankane musa bayan jidda ban tab'a kula wata y'a mace da sunan soyayya ba"akan jidda nasan meye so"sannan tanada abubuwan danakeso matar aurena takasance dasu"bana so naso jidda sbd kyawunta ko wani abu"inaso na aureta dan Allah"dukda kasan ita zuciya batada kashi"amma komai nata yamun"Allah yashige mana gaba to"cewar musa.....ahaka suna fira jefi jefi har suka iso gidan musa"da key yasaka yabud'e k'ofar dake cikin soro d'in"yah Abdul yatsaya abaya yana fad'in kaje kasanarwa da madam zan shigo ko?"abokina kai bak'ontane?"kadai je haka yadace amusulunce"to uztax"yafad'a yana dariya yayi cikin gidan"bbu jumawa musa yamasa flashing"Ahankali yah Abdul yanufi cikin gidan yanayin sallama anutse"musa ya amsa"yashiga cikin parlourn"musa na zaune agefen hafsat matarsa"hannayensu sark'e da juna"tanata jin kunya amma musan ko ajikinsa"dukda dare yafara amma tasha gayunta"ran amarya yadad'e"yafad'a yana k'ok'arin zama kan kujera"kanta ak'asa tana murmushi ta gaishesa"musa na mata rad'a suna dariya"yakama hannun ta suka wuce ciki"yah Abdul yasaki ajiyar zuciya sbd ba k'aramin burgesa sukayiba"atake shima yafara hasaso su ahaka shida jidda"wai tana zaune samqn cinyoyin sa tana masa shagwab'a....abokina mun barka kai d'aya ko?"bbu damuwa Ango"dariyar shakkiyanci musa yasaki yana zama kan carpet yajawo warmers d'in abincin"yazuba musu komai"friend rice dataji kayan had'i tanata k'amshin curry da spices"ga soyayyan naman rago asama....cikin y'an mintina sukayi k'at"atare suka fita sbd su tafi masjeed yin sallar isha'i....
Da dare misalin k'arfe 10:30 pm"yah Abdul ne kwance rub da ciki"akan katifarsa ad'akin sa "dg shi sai boxer yarufe jikinsa da bed sheet"sai matse k'afafuwansa yakeyi sbd ciwon mara dake addabarsa"sai juyi yakeyi yana rintse idanuwansa gwanin ban tausayi"dama yasan muddin tunda yaje wajen jidda comform ne zatayi masa shagwab'arta dake hadda masa sha'awa"gaba d'aya yana son kasancewa da y'a mace akusa dashi"dan yakasance mutum mai yawan buk'ata"amma Allah besa yyi aureba"taya samu aikin yi yakeyi ba aureba"amma wannan matsalar tasaka shi tunanin yyi auren anan kusa..yajima yanata juye juye sai wajen 1am bacci yyi awon gaba dashi"cikin ikon Allah yayi mafarki....koda yafarka da asuba jikinsa duk yab'aci"sosai yaji dad'in jikinsa"amma far gabansa guda yadda zai shiga cikin gidan yayi wankan wajibi"dan yasan goggo natashi sallar asuba"duba time yyi a phone nasa"da sauri yatashi sbd gudun kar yamakara"jallabiya yasaka yafito da babbar butarsa rike ahannunsa dake cike da ruwa"Ahankali yatura k'ofar yana sand'a yashiga"bbu kowa atsakar gidan"dan akwai nefa"Ahankali yanufi toilet"agaggauce yayi wankansa da alwalah yafito"Ahankali yanufi k'ofa yana hamdalar goggo bata ganshiba.....bekai bakin k'ofar ba yaji ance kai!!......✍️
zazzafan labarine mai saka mai karatu shauk'i"ba'a Fara komaiba zak'in labarin na agaba yi k'ok'ari ki biya ta wannan hanyar dan adama dake👇
wannan book d'in nakudine
Normal grp 300
Vip grp 1000
Special people 2k wato 3pages in a day
zaku biya kud'in ku ta wannan acc number👉2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK
Kituro shaidar biyanki what's app number d'ina 08100084251
300 kawai ake turo Kati idan bakida acc amma sauran payment d'in ta acc ne
banason transfer d'in Kati ko vtu photo d'in katin MTN zaki d'auka saiki turo dan Allah banda kira❌
Y'an nijar kutuntub'i wannan n👉 +227 88 01 90 50
Normal grp 500f
Vip grp 1000f
Special people 2000f
dan girman Allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba