SANADIN LABARINA 9

 

 Page (9)


***Dukkannin su suna zaune a falon, Mama na daga side din part dinta a kasa sai wata kanwar ta Anty Mimi da take ta fama da ita akan tasha ko tea ne, dan tun jiyan bata saka komai a cikin ta ba. Motar su ce tayi parking a kofar gidan da ke dauke da yan tsiraren yan uwan Baba a zaune a kasan rumfa, wajen su, su Baba suka nufa Safwan kuma da su Aunty suka shiga cikin gidan. Dukan uku uku kirjin Anty yake har suka dangana da kofar da zata sadaka da falon nasu, takalman mutanen da ta gani ne ya sakata sauya akalar ta zuwa shashen Yaya, duk nan din ma bata da yakinin abinda zata tarar, kanta a kasa hannun ta kunshe a cikin Hijab dinta ta shiga da sallamar ta wadda sai kayi da gaske zaka ji muryar ta da take a dashe sosai. Da ido Yaya ta bita bayan ta amsa sallamar har ta durkusa a gabanta, kanta a kasa tana kokarin tattaro ragowar kalaman da suka rage akan harshen ta


" Karki ce komai, idan har kikayi magana akan abun da ya faru toh lallai baki san kaddara ba, ba kuma zaki ci jarrabawar ki ba, Allah ya kan jarrabi bawa ta hanyar da be yi tunani ko zato ba dan ya gwada imanin sa, ki daure ki ci wannan jarrabawar."


"Nagode Yaya, nagode nagode da kika fahimce ni."


"Jahili ne kadai mara tauhidi zai zarge ki, ki tsarkake zuciyar ki, karki kula kowa da maganganun mutane ki tsaya akan gaskiyarki."


Shiru tayi tana jin nutsuwa na saukar mata, a kalla mutane biyu masu kusanci da Muhammad bayan mahaifiyar sa sun fuskance ta, sun kuma gamsu cewa ba zata cutar dashi ba. Sai da ta tabbatar da samun nutsuwar ta wajen kashi hamsin sannan ta bar shashen Yayan ta nufi nasu. Ta shiga duk suka bita da kallo, kallo me dauke da tarin manufofi, gaban Maman ta karasa, ta durkusa cikin yanayin da yake nuna tsantsar yanayin da take ciki, zatayi magana ta daga mata hannu dan dama tunda ta shigo bata kalle ta ba, 


"Bana son jin komai,cuta dai kin riga kin cutar dani, ba zan kuma taba yafe miki ba idan har cutar da Muhammad kikayi da gayya, ki fita daga harkar yayana da komai naki, bana son ko bude ido na ganki."


"Allah baya barin wani dan wani yaji dadi Maman Fauwaz, kuma Allah shine shaida ta, da shi da Usman duk daya suke a wajena, ba zan taba yin abinda zai cutar dashi ba, Allah ne shaida ta, wallahi wallahi ban san ya fita ba, ina sallah a lokacin, ban kuma san baya tare da su Amira ba."


"Babu abinda zaki ce fa malama, dan Allah ki tashi ki bamu waje, zaman ki anan ma matsala ce babba."


Anty Nafi tace tana jan dogon tsaki


"Maman Usman kije part dinki, ba komai.". Anty Mimi tace a kasan ranta tana jin babu dadi, tana kuma tausayin Haliman dan tasan ba zata taba aikata abinda yan uwanta suke zargin ta dashi, rabon ayi hakan ne ya saka har yace zai bisu, ajali ne yake kiran sa Allah ya kaddaro a chan kasar sa take. Jiki a sanyaye ta mike, ta wuce su tana jin wasu na maganganu kasa kasa, ta wuce part dinta ta shiga ta samu Jidda da Usman a zaune sunyi jigum tamkar wadanda sukayi jinyar satittika, kar ma Jidda da ramar ta sake fitowa sosai ta dashe tamkar wadda bata da jini. Karfafa kanta tayi ganin halin da yaran suke ciki, ta shiga da karfin ta tana kokarin aro jarumta ta dora a saman fuskarta wadda ta boye ainihin abinda take ciki.

   Zama tayi itama a gefen Jiddan, wadda take jin su kadai suka ragewa juna a duniya, sun dan jima a haka kafin Auntyn ta mike ta nufi dakin ta, sai a lokacin wayarta da take cikin jaka ta sake daukar kara a karo na kusan hudu kenan, tun bata shigo ba aka kira Jiddan na tsoron ta fita ta kai mata taga ana ma Auntyn wani abu sai ta hakura kawai, ganin an sake kira yanzu ya sakata ciro wayar ta tashi zata kaiwa Auntyn daga cikin dakin Auntyn tace


"Daga Jiddah kice bana kusa."


Tsayawa tayi ta daga wayar, ta kara a kunnenta, muryarsa ta shiga chan cikin kunnenta, wani irin dum taji saboda yadda karfi da amon muryar sa ta doki kunnenta, sake maimaita Hello Aunty yayi jin ba'a yi magana ba, zare wayar tayi da sauri daga kunnen ta, sannan ta sake mayarwa a hankali cikin siririyar muryarta tace


"Bata kusa." 


Shiru ne ya biyo bayan har ta zata ko an katse kiran ne, dubawa tayi taga yana kan layi sai ta sake maimaita wa


"Bata kusa Auntyn."


Samun kansa yayi da kwaikwayon muryar ta a chan kasan makoshin sa da ta tuna masa da sirantar ta, 


"Ina Auntyn?" Ya tambaya


"Ta shiga ciki, idan ta fito zan fada ?mata."


"Ok, an kaiki asibiti?" Ya tambaya yana son ji


"Asibiti?" Tace sai kuma ta hau girgiza kai


"A ah, ai ni lafiya ta kalou."


"Ok!"


Yace a gajarce sannan ya katse kiran. Dama kira yayi su yi magana da Auntyn akan abinda ya faru, yayi magana da Mama dazu, ya kuma san itama tana cikin zulumi dan kai tsaye Maman ta nuna masa Auntyn ce ma ta kashe Muhammad din, shine ya hanata yin komai, ya kuma roke ta akan kar ta tashi hankalin ta, ta kuma tashi na kowa ya nuna mata haka Allah ya tsara dama chan, dan dole ta hakura ta kuma yiwa su Aunty Nafi magana suka hakura dan da sun shirya ciwa Auntyn mutunci sosai.

    Tunanin sa ne ya tsaya akan yar ficikar yarinyar, wadda be taba gani ko jin mutum me ramar ta ba, shi mamaki yake da yaji har tana magana radau haka kamar ba ita ba, a fili idan batayi magana ba zaka rantse ko kwakkwaran motsi idan tayi zata iya faduwa. Shafa sumar kansa yayi da ta soma taruwa dan ya kwana biyu be rage ta ba, ya shaki iska ya fezar yana tattare dukkan tunanin sa a waje daya, sannan ya mike daga gaban reading table dinsa ya tashi zuwa wajen system dinsa ya dauko ta ya jona a jikin socket ya kunna sannan ya shiga duba wasu publication yana kokarin dauke hankalin sa da abinda ya faru, duk da a chan kasan zuciyar sa yana tare da tausayin yaron, wanda ba zai dorar da wani abu ba game da rayuwar sa, duk rashin sakewar sa da mutane yana da matukar son yara, shiyasa yayi sabo da shi da Usman idan yana nan suna yawan zuwa dakin sa su manne masa, basu da rashin ji da hayaniya irin ta yara dai dan abinda ba zaa rasa shiyasa suke dadewa a wajen sa basu gundire shi ba, da zarar yaji zasu fara damun sa sai ya kunna musu kallo ya shige daki ya barsu wani lokacin har sai sun yi bacci sannan ya saka Safwan ko Safiyya su dauke su.

   Tattare aikin yayi ya ajiye dan baya jin zai iya, ya zaro socks me kauri sosai saboda sanyin da ake zugawa ya saka a kafarsa ya rufe ta da katoton takalmi ya dora rigar sanyi me kauri sosai ya fice daga gidan.


****

Kasancewar karamin yaro ne ba a zauna wani zaman makoki ba Baba yace babu bukatar hakan, idan kaga Mama zaka dauka jinya tayi saboda yadda ta zabge lokaci daya haka ma Aunty, dukkan su basu da lafiya dan sai da Baba ya kira Dr Bashir yazo har gida ya duba su ya basu magani.

   Sati kusan biyu da faruwa abun amma babu wani sauyi a yanayin gidan, idan ka shigo gidan zaka rantse babu mutane dan ko su Amira da suke ziryar shiga part din Auntyn yanzu basa yi saboda maman, sai dai su hadu idan zasu tafi islamiyya amma ko zaman falon wajen duk sun daina, tafiya ta kama Baba satin sa guda kenan bayanan shiyasa ko zaman cin abincin ma sun daina dama shi yake assasawa shima kwana biyu kafin ya tafi ya rabu dasu dan baya son tashin hankali kuma zaman su waje daya sai iya haddasa abinda yake ta gudu.


*** Tsaki Yaya taja a karo na ba adadi, lalle take kwabawa zatayi kunshi, duk gidan ya isheta so take ta yi tafiya amma tasan Baba ba zai barta ba, gashi yan hirar tata sun daina zuwa dama Jiddah ce take kawo su amma yanzu gidan kamar an yi ruwa an dauke shiru kake ji, bakin ta kaikayi yake mata kusan kwana uku kenan tana neman wanda zasu yi hira dashi amma ta rasa, Abu da take shigowa tayi mata wasu ayyukan kwana biyu taje ganin gida sai ya zama sai ita kadai. Kunshe kafarta tayi bayan ta shafa lallen a dukka kafar abinda ake kira da dungulmi ko tsohuwa ta fada kwata, ta saka leda da tsumma irin yadda tsofaffi suke, sai ga Safwan ya shigo. Sakin baki tayi tana kallon sa kafin tace


"Kai nifa na zata baka duniyar nan."


"Kai Yaya, ina zanje? Ina nan."


"Amma ko gaisuwa? Saboda ba uwar ku bace ace babu me leko ni."


"Kiyi hakuri sarauniya, kinsan yanayin da ake ciki, shiyasa amma ki basu yan kwanaki zasu ware, ni bana zama ne kwata-kwata ga kula da shop din Mama ga zuwa school?"


"Menene shup?"


"Shop ba shup ba Hajjaju."


"Ko ma uwar menene dai."


"Shago ake nufi, shine shop da turanci."


"Yanzu shagon ne kuka maida shi shap saboda tsabar iyayi da kinibibi ni Hajara?"


"Haka yake ai, yawanci fa kalmomin turanci ne bahaushe ya sata."


"Ummm, karyar banza."


"Allah Yaya, yawanci kalmomin na turanci ne."


"Kaga idan kana da kati a wayar ka, kira min yayanka inaso nayi magana dashi."


"Wai Ya Tariq?"


"Shi, kira min shi."


"Missing dinsa kike Hala?"


"Musi?" Tace tana bata fuska


Dariya ya kwashe da yace


"Eh mana..."


"Kai ka sani, idan ma zagi na kayi ruwanka,kira shi tambayar sa zan ko yana shan maganin sa, dan jiya nayi mafarkin sa wallahi."


"Magani? Wait wai bashi da lafiya ne?"


"Baka sani ba? Ai ba kalou kansa yake ba, shiyasa nayi yadda nayi na tabbatar ya karbi rubutu ya soma sha, kar abun yayi tsamari azo a aura masa yarinyar mutane ya bada wahala kamar yadda kakanku ya wahalar da rayuwa ta, kai gayen nan yaci ubana daidai gwargwado,me zaa yi da miskilin mutum ne wai?"


Dariya sosai ta bawa Safwan, ya shiga kyakyatawa har da kusan zamowa daga kujera, tsaye tayi hannun ta nannade da leda da tsumma tana kallon shi, bata cika son dariya ba nan da nan tayi kicin kicin da fuska, da kyar ya samu dariyar ta tsaya, ya rike bakin sa ganin ta bata fuska,


"Ya hakuri Hajiyata, afwan wallahi kece kika bani dariya, wato kema kinsan gaye?"


"Ban sani ba, tashi kayi gaba, idan ba zaka kira min shi ba, bari ubanku yazo ai shi na isa dashi sai yakira min Shi."


"Maida wukar your excellency, ni ban isa ba wallahi, bari na kirashi amma ba lallai ya daga ba, kinsan da banbancin lokaci tsakanin mu."


Shiru tayi masa banza kamar ba da ita yake ba, ciro wayar sa yayi, ya shiga WhatsApp yayi dialing video call dan hakan ne kadai zai wanke shi a wajen Yayan. Jidda ce ta shigo sashen daure da food flask me dauke da alala da Auntyn tayi wa Yaya, da sauri Safwan ya mike ya karbi flask din yana mata murmushi

[

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links