Page (8)
****Kasancewar karamin gari ya saka suke da yakinin ba zai bata a cikin sa ba, sai dai tabbas ana kyautata zaton ba lafiya ba, daga chan gaban gidan su Jiddan akwai wata babbar rijiya, da duk mazauna wajen suke amfani da ita. Kamar an tsikari Aunty haka ta mike da sauri duk suma suke mike
"A duba rijiyar nan, Allah ubangiji yasa ba fadawa yayi ba."
Ta fashe da kuka, jikinta na rawa sosai tamkar mazari, Baffa ne da Baffan su Saude da wasu maza biyu suka nufi rijiyar dan duk ciki babu wanda ya yi tunanin dubawar.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Kalmar da aunty ta iya ji kenan daga bakin Baffa sanda ya leka kansa cikin rijiyar, saboda tsabar kaduwa ta yanke jiki ta fadi cikin wani irin yanayi. Nan da nan wajen ya cika makil da mutane aka samo masu shiga rijiya mutum hudu biyu suka shiga suka dauko shi, cikin yanayin firgici.
***Wani irin kuka aunty take, duk rashin imanin ka sai ka tausaya mata, Jidda da Amira ma sun ci kuka sun gode Allah, suna nannade a zaune gefen Aunty Usman na jikin Amira yana kuka shima duk da kukan be san na menene ba, waya Baffa ya dauka ya kira Baba, ya koma gefe ya sanar dashi abinda yake faruwa cikin yanayin dauriya dan sai da yayi da gaske sannan ya iya kiran Baban shima saboda kiran ya zama dole ne.
"Kullu nafsin za'ikatul maut Yaya, ko da Muhammad a gaban mu yake ni da mahaifiyar sa dole sai ya mutu, bani da jahilci dan ni musulmi ne kuma na yarda da kaddara, Allah ya sa me ceton mu ne, kayi mishi dukkan abinda ya kamata a kaishi gidan gaskiya."
Jiki a sanyaye Baffa ya dawo ciki, akayi duk abinda za'a yi, a daren aka kaishi.
****Sanda Baffa ya kira Baba yana daf da shiga gida, sosai mutuwar ta dake shi duka me zafin gaske, kansa a kasa kirjinsa na masa wani iri, juriya da jarumta irin ta namiji a haka suka karasa gidan, yana tunanin yadda zai sanar da Mama.
Dakin ta ya wuce kai tsaye wanda ya dade rabon shi da shiga har cikin dakin nata, tana zaune tana lissafi gabanta tray ne na abinci tana so ta kammala taci duk da tana jin kamar an dauke appetite din bakin ta ne, wani irin yanayi take jin zuciya da gangar jikin ta tamkar zatayi zazzabi, daurewa kawai take tana karfafa jikinta dan bata so ta bar aikin da take bata kammala ba. Sauri take taga ta gama dukka dan tana son kiran Tariq taji ko lafiya yake? Dan sai take jin kamar ba lafiya ba, ajiye takarda da biron hannun ta, tayi ta jawo wayarta dake saman gado ta hau dialing number sa.
Yana zaune a gajiya yake tikis bayan ya dawo daga motsa jikin sa, so yake ya watsa ruwa kafin ya duba wasu papers da zai, amma kuma ya gaza tashi yana kishingid'e kansa na dan sara masa wanda ya san stress ne na karatu da baya ko hutawa dan a sati weekends ne kawai yake samu ya huta kamar na awa hudu amma sauran ranakun sam bashi da hutu. Wayar sa dake yashe a saman dan madaidacin table dake cike da manyan text books dinsa ce tayi kara, duk da baya expecting Kira daga kowa amma sai ya mike yana dora idon sa akan table din har ya karasa ya dauki wayar ganin sunan Mama ya sakashi dagawa ya zaune a kujerar dake gaban table din yace
"Hello..."
"Hello Assalamu alaikum."
"Wa alaikisalam." Ya amsa yana dan motsa kafarsa kafin ya gaishe ta, ta amsa sannan ta dora
"Lafiya kake ko?"
"Me faru mah? Lafiya ta kalou."
"Naji muryar ka haka-haka, hope dai babu wata matsala."
"No, stress ne kawai, da na dan samu na watsa ruwa zan warware ."
"Ok!" Tace a gajarce, shigowar Baba dakin ya sakata rike maganar da zatayi, ta zuba masa ido tana karantar yanayin da ya shigo mata, zama yayi a gefen ta, sai taga kamar idanun sa sun kada
"Rike wayar Tariq."
Tace tana zare ta daga kunnenta, tashi yayi shima bayan ya cire wayar daga kunnen sa ya nufi wajen kayan sa, ya shiga cire kayan jikinsa.
"Me ya faru?" Tace tana kallon sa
"Aisha!" Sai gabanta ya ce ras jin ya ambace ta da sunan ta kai tsaye, kamar wadda aka zare wa laka haka taji, ta saddakar babu lafiya amma kuma ta gaza hasaso komai akai
"Kinsan cewa rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Haka kinsan cewa bawa baya taba wuce kaddarar sa, kiyi hakuri, kiyi hakuri duk me rai mamaci ne."
"Dan Allah me ya faru?" Tace hannun ta na rawa
"Muhammad ne..."
Sai ta mike da sauri,
"Me ya same shi?"
"Zauna dan Allah." Yace yana riko hannun ta, kasa zama tayi ta hau girgiza masa kai
"Me ya same shi? Me ya sami d'ana."
"Ya fada a rijiya, Allah yayi masa rasuwa."
Kara ta kwalla da karfi,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shikenan an kashe min d'a."
Sai ta fashe da kuka me karfi, kukan da ya kai attention din Tariq kan wayar dake hannun sa yana kokarin zuba tea a cup,a kunne ya saka wayar da sauri yana sauraren abinda Maman take cewa
"Sai da na nuna bana so yaran nan su je, ka dage dole sai sun je, shikenan ta kashe min shi,an raba ni da d'ana, Wayyo Aallah na."
Riko ta Baba yayi, ta kwace tana matsawa baya, kamar zata zauce haka take ji, da sauri Tariq ya katse kiran sannan ya sake kira at the same time, Baba ne ya dauki wayar, ya daga
"Muhammad ne Allah yayi mishi rasuwa yanzu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, rashin lafiya yayi?"
" A'ah, tsautsayi ne ya gamu dashi,ka kwantar da hankalin ka zan kira ka."
Sai ya kashe wayar, yayi saurin fita ya bi bayan Mama da ta fice da gudu tana kwala ma yaran kira. Da sauri Safiyya, Maryam da Umaima suka fito a kusan tare, Yaya dake part dinta itama ta fito a gigice, Safiyya ce ta rungume Maman da take kuka tana kiran ta kashe mata shi, kamar wadda zata zauce haka ta koma, duk suma suka saka kuka ganin Maman na kuka sosai, daka musu tsawa Baba yayi ganin sam sun maki sauraren sa, yana kokarin yayi magana amma suna kuka Maryam hadda kururuwa, shiru sukayi duk suka koma kuka kasa-kasa, yace su wuce zuwa falo, sannan ya juya, suka bi bayan sa banda Mama da ta tsaya a wajen, sai da Safiyya ta rike ta sannan suka koma ciki, duk suka zauna suna fuskar su a cikin kafafunsu suna kuka kasa kasa , Yaya ce kawai a zaune a kujera, Mama na daga kofa taki zama, Baban ma a tsaye yake ba zaka iya tantance yanayin halin da yake ciki ba, Muhammad yaro ne me matukar shiga rai, shiyasa ya shiga ransu sosai duk da karancin shekarun sa,
"Dukkan mu zamu mutu babu Wanda zai zauna a duniyar nan sai dai in har lokacin mu be yi ba, amma idan yayi dole ne mu tafi, babu kuma wanda ya isa ya hana, kowanne bawa da yadda Allah ya kaddaro masa SANADIN mutuwar sa, Muhammad lokacin sa ne yayi,ko yana gaban mu ne bamu isa mu hana ba wallahi, kukan ku ba zai dawo dashi ba kuma ba zai chanja komai ba sai ma sabawa Allah da kuke kokarin yi ta hanyar kin yarda da kaddara."
"Allah ya gafarta masa yasa me ceto ne."
Yaya tace a sanyaye ita kanta mutuwar ta kad'a ta, dan hawaye take yi duk da bata bude murya ba,
"Kiyi hakuri Aisha, kiyi masa addu'a kawai, idan Allah ya kaimu da asubah zamu tafi in sha Allah."
Daga haka ya juya da sauri ya bar falon,zaman dirshen Mama tayi a wajen ta cigaba da kuka me cin rai, zuciyar ta taki amince mata ba an shirya cutar mata da yara bane dama tun farko shiyasa bata amince da tafiyar ba, waya Safiyya ta dauka ta kira gidan su Maaman, cikin kankanin lokaci sai gasu sisters da brothers din Mama har da Hajiya Babba, babu wadda ta yarda a cikin su cewa lokacin Muhammad ne yayi, dukkan su sun tafi akan shiri ne, wasu ma gani suke Aunty ce ta jefa shi a rijiyar dan sun yarda babu abinda kishiya ba zata iya aikatawa akan yayan kishiyar ta ba. A gidan duk suka kwana Hajiya Babba kawai aka mayar gida zaa dawo da ita gobe, kusan duk basu rintsa ba.
Bangaren Aunty kuwa sosai jikinta ya rikice da mugun zazzabi, tun bayan da aka kaishi aka dawo ta tabbatar da gaske ya rasu ba mafarki take ba, bata san wanne kalar tunani mutane zasuyi akan ta ba amma ta tabbatar ba zata taba fita ba, me zata cewa Mama ta yarda da ita ne wai? Me kuma zata ce wa Baba da saurin yaran su yarda babu sakacin ta?
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Ta furta da karfi sai kuma ta fashe da kuka, rike ta Innar su Saude tayi tana bata Baki
"Kiyi hakuri, haka Allah ya kaddara babu makawa sai ya faru."
"Me zan ce wa duniya? Me zan fadawa mutane su yarda bani da hannu a ciki? Su yarda ba sakaci na bane? Me yasa wai ma ba Usman bane ya mutun?"
Da sauri ta rufe mata baki tana bata fuskar ta sosai
"Karki yi sabo wallahi."
"Astagfirullah."
Ta hau fada da sauri da sauri, jidda da Amira dake kusa dasu suka kara tsananta kukan su, har wani jaja-jaj fuskar jidda tayi saboda kuka, fuskar su ta daga sosai, su ya bi, Usman yace su dawo shi sai ya tsaya yace zai jira su,ya akayi har ya je wajen rijiyar ya fada babu wanda ya lura shine abinda yafi damun Baffa.
Gidan baki daya babu wanda ya rintsa saboda zulumi da tashin hankali, da asuba, Baba, Safwan da abokin Safwan Jamil, neighbors suke sai abokan Baba su biyu Alhaji Adamu da Malam Nura sai driver Baban suka dauki hanya, suka isa wajen 7 lokacin su Baffa sun fita har an shinfida tabarmi suna zazzaune cike da zulumin tashin hankalin da ya same su, tunda Baffa ya hango motar su Baban gabansa ya fadi, haka ya daure ya taro su, suka hadu suka zazzauna, gefen Baban Baffa ya zauna jikin sa a sanyaye, lura da yanayin Baban ya sakashi yin shiru dan da so yake yayi masa bayani amma sam Baban ya nuna babu bukatar hakan. Sun dan jima a zaune har rana ta fito sosai, sannan suke ce zasu tafi. Baffa ne ya nemi Baban ya shigo ciki su yi magana da aunty dan sosai take cikin wani hali, tashi yayi yabi bayan Baffan zuwa cikin gidan, suna zazzaune a tsakar gida da sauri Amira ta tashi tayi wajen Baban tana fashewa da kuka, rike hannun ta yayi be ce komai ba, ya isa gefen tabarmar da aka shinfida masa ya zauna sannan ya amsa gaisuwar matan dake wajen tare da Aunty duk suka tashi suka shiga ciki ya rage daga shi sai Aunty, kukan ta ne ya tsananta har ta gaza furta kalma daya ,yana jin ta be ce komai ba, har sai da ta dauki lokaci dan kanta ta rage ta shiga jan hanci.
"Kin gama?" Yace yana kallon ta, girgiza masa kai tayi da sauri
"Toh ya ishe ni haka, kin isa ki hana abinda ya faru ya faru ne? Ko kuma zaki iya chanja abinda Allah ya riga ya kaddara?"
Girgiza kanta tayi da sauri, ya gid'a kansa sannan yace
"Bana son shiririta, abinda ya riga ya faru ya faru, Allah ya jikan sa yasa ya huta, kar ku bata mana lokaci tare nake da mutane, ku fito mu wuce."
Yana fadan haka ya mike, ya fice daga gidan, jikinta a sanyaye ta tashi itama, taje suka dauko kayan su, suka fito Jiddah dauke da Usman ,Amira ta rike musu kayan, Iya Lami da tayi dawowar safe na tsaye daga gefen bayan gida ta zuba musu ido,tana hasashen yadda zaa kwashe da uwar d'an idan an koma, zata so ace da ita zaa yi tafiyar dan kawai taga yadda Halima zata wulakanta dan ta tabbatar ba za'a kwashe kalou ba dan ma mijin nasu babban mutum ne me dattako.
Sallama sukayi mata,ita da Innar su Saude da sauran matan, ta amsa kamar ta damu da abinda ya faru, ta rakasu har zaure tana bawa Auntyn baki, babu wanda ya kulata suka fice dan kowa ya riga ya san karya take kawai dai dan kar ace bata yi bane. Motar da Fauwaz da Jamil da Driver suka shigo ita su Auntyn suka shiga sai Jamil ya koma wajen su Baba ya zauna a gaba. Baffa na tsaye da sauran mutanen unguwar, sai matan dake mammakale a katanga, daga musu hannu su Baffa sukayi sanda aka tada motar, idanun sa akan Jiddah da itama shi take kallo, har suka bar unguwar tasu. Ajiyar zuciya Baffa ya sauke yana fatan komai yazo wa Haliman da sauki dan ya hangi tashin hankali shinfide acikin kwayar idanun ta, ya kuma san abinda take gudu da tsoro wanda har ya haifar mata da zazzafan zazzabi wanda baya raba daya biyu daga jiya zuwa yau Jinin ta yayi mugun hawa.