*7*
©®Hafsat Rano
****A tsakiyar falon ta tsaya ta shiga kwalawa Amiran kira, a tunanin ta, tana cikin wajen Antyn, bata san direct wajen Yaya ta gudu ba dan tasan haduwar su ba zatayi kyau ba, shiyasa ta salallaba ta gudu, ba kuma zata yarda su hadu ba sai gobe , dan duk bala'in Yaya sai dai ta barta amma a wajenta zata kwana ta san kuma Mama ba zata taba biyo ta wajen Yayan ba,gaisuwa safe ce kawai take hada su kuma shima kwana biyun nan da daminar ta dan ja baya zafi ya sako kai tsakar gida take fitowa tun sassafe ta basa baza tabarma.
Dakin ta, ta shige ta san duk daren dadewa zata zo ta sameta ne, bata amince ba babu in da zata bi Halima dan har yanzu bata gama yarda da ita ba, duk yaron da zaka dauke shi aiki karshe ya aure maka miji ba kuma zaka taba amince masa ba har duniya ta nade, duk da idan da zaa saka mata wuka ace ta fadi aibun ta ba zata ce gashi ba, amma ita sam bata amince da ita ba, ba kuma zata fara daga yanzu ba, ta bar yarta ta bita garin da bata san me zata tarar a chan ba.
Da la'asar fita ta kamata, ta shirya ta fice daga gidan ta manta shaf da batun Amiran, shagon ta ne aka kawo kaya, abinda ya fitar da ita kenan tare da Fauwaz, wanda basu suka shigo gidan ba sai dare. Kasancewar a gajiya ta dawo bata bi ta kan ta ba, ta kwanta dan da wuri zata sake fita washegari akan ragowar kayan da basu riga sun iso ba.
Shirin su suke hankali kwance, murna wajen Jidda da Amira baa magana, Maryam a kasan ranta tana son bin su Amma bata shiryawa fadan Mama ba, shiyasa kawai ta hakura tana kallon su. Kitso akayi ma Jiddan me kyau duk da tsananin santsin gashin kanta amma da ya hadu da bahijja me kitso sai gashi ta kama mata shi, yayi kyau sosai dan sai da taji kunya yadda su maryam suka dinga koda ta wai kamar kan larabawa.
Cikin dare ta kasa bacci saboda zumudin tafiyar ana kiran sallah ta mike kamar wadda aka tasa, ta hau shiryawa tana sake hade kayan da zata tafi dasu. Tun dare dama tayi shara saboda haka babu datti, sai yan kayan da ba zaa rasa ba suma ta tattare kowanne ta saka shi a in da ya dace. A haka Anty ta sameta, batayi mamaki ba dan idan da sabo ta saba da wannan, sam Jiddan bata da son jiki kuma duk abinda ta san ya kamata yi kawai take ba sai an ce ba, bare kuma yau da take da zumudin ganin baffanta.
"Sannu Jiddah, Allah dai yasa kin yi bacci?"
"Nayi." Tace sai kuma ta dan russuna tace
"Ina kwana Aunty?"
"Lafiya lou Jidda, bari na dora mana ruwan wanka dan da wuri zamu fita in sha Allah, idan kin gama kije ki ga Amira ko ta tashi."
"Toh..." Tace cike da zumudi ta karasa abinda take ta nufi wajen Yayan dan Amira ta fada mata anan zata kwana saboda Mama.
Ta tashi har tayi sallah ma,amma kuma yanayin ta be nuna wa Jiddah tana cikin walwala ba, kallon fuskar ta tayi, sai kuma ta zauna a gefenta tana mata kallo me dauke da alamar tambaya
"Na fasa zuwa." Tace a cikin yanayin da yake nuna kusa take da ta fashe da kuka
"Mama?" Ta tambaye ta
Daga mata kai tayi alamar eh
"Ok kiyi hakuri."
"Dan Allah mene dan na biku? Gaba daya Mama bata so taga muna harka daku bansan me yasa ba, yanzu ta turo Safiyya wai kar na soma bin ku."
"Bakin kishin ta na tsiya ai bazai barta ta hakurar wa zuciyar ta, ta karbi abinda Allah ya riga ya kaddara ba."
Yayah tayi maganar tana shigowa dakin rike da charbi a hannun ta, duk suka kalleta sai ta dora
"Nace dai duk ba akan kishi ake wannan abun ba? Idan akan shi ne yaci ace an ajiya ko? Shekarar Halima kusan takwas a gidan nan harda arzikin Usman, idan hakan be zama ishara ba sai yaushe?"
"Ba haka bane Yaya, tace wai bamu saba zuwa irin wajejen ba."
"Uwarki ce bazan hanaki kareta ai, me zai sameku a chan da ba zai same ku anan ba? Kin taba ganin an yi wa Allah wayo? Ba hujja bace bakin kishi ne kawai."
Mikewa Amiran tayi tana jin babu dadi, bata son maganganu irin haka akan Maman, musamman daga wajen Yayah, a kullum so take taga komai ya zama normal Mama ta yi hakuri ta bar komai ya wuce
"Idan kun gama shiryawa zan shigo."
Ta wuce kawai ta bar part din ranta duk babu dadi
"Yarinyar nan ba dai hankali ba dan tafi uwarta wallahi, dama uban yan girman kan chan da safiya sune suka yo uwarsu, amma sauran ba ruwan su."
"Uhum." Jidda tace itama ta mike, tafice ta bar Yaya na cigaba da mitar zancen.
A gurguje tayi ma Usman wanka tayi nata ta shirya cikin riga doguwa ta atamfa ta sallah da Baba yayi musu ita da Maryam da Amira. A shirye ta samu Aunty tana zaune tana waya a gefen gadon ta, yadda take wayar ya tabbatar mata da Baffa ne, zumudin ta ne ya karu sanda taji Antyn tana cewa sai sun zo. Bayan ta gama wayar ne ta dauko mata sarka da dankunne me kyau ta bata ta saka sannan tace ta jirata a falo. Fita tayi ita kuma ta yafa mayafin ta ta nufi sashen Baban, ta same shi ya shirya shima, da mamaki take kallon sa
"Ba dai fita zakayi?" Tace tun daga kofa, kafin ya bata amsa Mama ta turo kofar ta shigo, ya kalle ta sannan ya maida kallon sa wajen Auntyn yace
"Tare zamu, inaso zan ga Yaya."
"Yaran sun shirya?" Yace yana kallon Mama, dan dam tayi amma sai ta kame tace
"Sun kuma chanja shawara kasan abun yara."
Gid'a kansa yayi yace
"Taimaka min da hula ta akan bedside Halima."
"Toh." Tace ta wuce ciki, yana ganin ta shiga ya maida kallon sa kan Mama yace
"Minti goma sha biyar na basu su shirya, Muhammad ma yace min zaije dan haka kar abata min lokaci."
Wani kallo tayi masa, ya daga mata kai alamar haka yace, bata ce masa komai ba ta juya ta fice daga shashen. Dakin su Amiran ta wuce ta sameta a kwance a gado ta lulluba da bargo ranta babu dadi, a kanta ta tsaya fuskar ta a hade tace
"Sai ki tashi ki shirya yana jiranku, saura ki tsaya bata lokaci yace ni na hana kuma."
Da sauri ta mike zaune, tana kallon fuskar Maman cike da zumudin murna
"Ki shirya Muhammad ma, ki daukar masa sababbin kayan sa."
Daga haka ta juya ta bar dakin, da sauri Amira ta tashi ta hau ciro kayan ta a wardrobe da ta maida su, ta saka a trolley taje dakin Maman ta dauko na Muhammad ta hada, sannan ta shiga wanka ta watsa da mugun sauri sannan ta fito ta zura kayan ko shafa mai batayi ba,ta fita zata kira Muhammad Maryam tace mata ta masa wanka har ya tafi falon Baba, komawa tayi daki da sauri ta gyara fuskar ta, ta daura dankwali sannan ta dauko kayan nasu ta fito.
Babbar motar Baban ce da ake amfani da ita idan za'a je kauye ko wani waje tare, driver ne yake tukata sai Baban a gefen sa, kujerar baya jidda da amira suka zauna Anty kuma ta zauna a ta tsakiya ita da Muhammad da Usman, maryam kamar zatayi kuka da ta rakosu dan dai kawai bata son fushin Mama ne amma da itama sai taje, ita da Safiyya kawai suka rage a gidan dan Mama ta sake fita da Ya Fauwaz da Umaima tun dazu kuma kila sai yamma likis zasu dawo.
Hanya suka dauka sosai bayan an tsaya an yi siyayyar abubuwan da zasu tafi dashi. Tafiya sukayi a hankali har suka isa, hakan ya kara zumudin jidda ganin an dauku hanyar gidan, ta zura hannunta ta window tana feeling sanyayyiyar iskar dake kadawa. Parking Baba Driver yayi a kofar gidan dan ba wannan ne karon farko na zuwan sa da Baba ba. Baffa na jin tsayuwar mota ya fito da sauri suka yi kicibis a waje. Fuskar sa tamkar gonar auduga, idanun sa suka hango masa Jiddan sa, wadda ta sauya masa tayi haske ta dan yi kiba kadan, wajen Baba ya nufa kai tsaye duk da dokin ganin Jiddan, suka shiga gaisawa da tambayar bayan saduwa,cikin gidan suka dunguma suka shiga gaba daya, akayi sa'a Lami bata nan tayi tafiya zata kuma kwana biyu, gidan a share yake tas tas, sai katuwar tabarmar da Baffa ya shinfida a tsakar gidan, suka zauna dukkan su aka shiga gaishe gaishe. Duk da zumudi da son ganin baffan nata amma sai ta makale a gefe cike da kunya, takasa cewa komai. Dariya duk ta basu Baba ya tsokane ta akayi dariya kafin ta gaida Baffan ya amsa sannan Amira ma ta gaishe shi.
Wajen awa biyu Baba sukayi, suka sha fura da nono sannan suka ci dambu da Innar su Saude ta aiko musu, sannan suka shirya komawa shi da Baba driver, Kwan zabi Baffa ya basu masu yawa ya rakasu har mota Baba ya dauko kudi ya bawa Baffan ya karba da kyar yayi godiya. Ya bude masa kofar ya shiga ya sauke glass din yace
"Yaya zan shiga siyasa in sha Allah, a tayamu da addua."
"Kai Masha Allah, Alhaji ai dama irin ku ake so a siyasar kasar nan,ka chanchanta"
"Kayya, zamu dai gwada jarrabawa mu gani."
"Toh Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin."
Suka sake sallama suka tafi Shi kuma ya koma cikin gidan, ya samu Anty a zaune suka shiga hirar yaushe gamo, ya dinga yi mata godiya akan jidda sannan ya bata labarin zuwan da Baba yayi aka kaishi wajen likatan kashi tun daga lokacin ya samu saukin kafar dan har gona zuwa yake. Ita bata ma san anyi ba,dan be fada ba, kuma dama tasan ba fada din zai yi ba, haka yake ko yayi abu baya so a yaba masa yafi son kawai a yi shiru.
***Kwanan su biyu sosai Amira taji dadin garin, yanayin weather din yayi mata ga fura da nono abinda take matukar so kenan, gobe zasu tafi shima da kyar Baba ya kara musu kwana daya,dan be samu me zuwa dauko su bane ba ma shiyasa, kanya suke je tare da Saude suka samo suka zauna a tsakar gidan su Sauden suna sha tana basu labarin abun dariya, tashi Jidda tayi ta ce zata dauko abu a gida ta dawo. Gidan su ta shiga ta tarar da Anty zata fita hankalin ta a tashe, da sauri tace mata.
"Jidda Muhammad yana wajen ku ne?"
Da sauri ta girgiza kanta
"A ah, tare muka bar su da Usman suna zaune."
"Na shiga uku!"
Tace tana yin gaba, da sauri jidda tabi bayan ta, suka hau neman sa, abu kamar wasa sai gashi an neme sa an rasa, iya kar tashin hankali Anty ta shiga. Sauran makota ne suka fito aka bazama nema, Usman dai yace yabi su Yaya Amira da Yaya jidda da suka fita, lokacin Anty tana sallah, su kuma sun ce be biyo su ba, kuka wiwi Anty take tana jin kamr ta hadiyi zuciya ta mutu, wannan wanne irin tashin hankali ne, ina ya shiga? Me zai faru? Yaya Mama zata ji idan wani abu ya same shi bayan da kyar ta yarda suka biyo ta, zata taba fita idan wani abu ya same shi? Ba zata fita ba ko a wajen mutane balle mahaifiyar sa. Har duhun magriba ya soma babu shi babu labarin sa, dukkan su kuka suke har Jidda da Amira da ta cika da tsoron abinnda zai faru da Muhammad din.
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*