SANADIN LABARINA 6


 


                  Page (6)



****Fauwaz ne yayi mata duk cike-ciken da ya kamata yayi mata, ya biya kudin da komai sannan akayi mata interview, yanayin karatun ta ba irin nasu bane dan haka abubuwa da yawa bata gane ba, a jss 2 head teacher din yace a sakata Fauwaz ya roki a sata 3 tunda yanzu aka juya session din, hoping zatayi coping kafin time din, haka akayi aka sata ya rakata har kofar class din su da yake kusa da na su Amira ss1, tsayawa tayi tana kallon sa, a hankali tace


"Nagode Ya Fauwaz." 


Murmushi yayi mata sannan ya tafi, ita kuma ta shiga cikin ajin. Duk suka zuba mata ido suna kallon ta, tsayawa tayi daga jikin kofar ta sunkuyar da kanta kasa, Safeera ce ta taso daga seat dinta tazo ta sameta a tsaye tace


"Taho ki zauna."


Bin ta tayi zuwa seat din dake kusa da na Safeeran ta zauna sannan tayi mata godiya.


"Nagode."


"Ba komai, ya sunan ki?"


"Jidda..."


"Nice name, ni kuma sunana Safeera, ki saki jikinki, duk wadda ta raina miki hankali ki fada min."


Murmushi tayi mata bata ce komai ba, uncle ya shigo suka maida hankalin su zuwa kansa, kowa ya mike aka gaishe shi sannan yace new comer ta tashi tayi introducing kanta, bata motsa ba dan da turanci yayi maganar sai da Safeerah ta rada mata, ta tashi da sauri a kunyace ta tsaya,ya sake maimaitawa


"What is your name?"


Tace


"Jidda."


"Hauwa'u right?" Ta daga kanta


"Ki fada har da sunan Baba." Safeera ta sake whispering mata 


"Hauwa'u Ibrahim."


"Ok welcome to Jss 3 Hauwa'u, seat down."


Zama tayi jikinta a sanyaye, turancin shine babbar matsalar ta a yanzu, dan su a chan da Hausa ake koya musu yawancin subjects din. Introducing new topic yayi ya shiga bayani wanda kusan rabi babu abinda ta fuskanta, Safeera na lura da ita, har ya gama ya fita, ta kalleta bayan malamin ya fita tace


"Baki gane ba ko?"


Daga mata kai tayi alamar eh


"Zan miki bayani idan an fita break, sannan karki ji tsoro, turancin ma bashi da wahala, da kin gane shikenan."


"Nagode." Tace tana mata murmushi 


"Can we be friends?" Tace tana mika mata hannu, hannun ta kalla hakan ya saka Safeera yin dariya


"Zamu zama kawaye?" Ta fada mata da hausa, gid'a mata kai tayi ta mika mata hannun itama, suka gaisa


"Friends for ever." Tace tana sake matsar da chair din ta kusa da ta Jiddan.


"Duk abinda baki gane da turanci ba ki fada min, sannan akwai dictionary ma, duk kalmar da kika ji baki gane ba, ki duba zaki ganta da meaning da komai, zakiyi mamaki yadda zaki improving sosai."


*Shikenan, nagode sosai."


Hannu ta mika mata


"Taso muje muyi break kafin a dawo class."


Mika mata hannun tayi suka fito compound din makarantar, Amira da ke zaune tare da friends dinta ta taso da sauri


"Jidda."


"Kin santa?" Safeera ta tambaya


"Gidanmu daya." Amira tace sannan taja hannun ta


"Muje kafin a koma class."


Bin ta tayi safeera tayi tsaye tana kallon su, Asiya ce tazo kusa da ita tayi dariya tace


"Daga ganin yarinya kin makale mata, gashi nan ai."


"Ina ruwan ki?" Tace tana barin wajen, taje ta siya egg rolls guda biyu da lemon cway ta ci daya ta dauki daya ta je wajen da suke zaune da amira da kawayenta, ta mika mata


"Kawata gashi."


"Ta gode taci meat pie."


Amira tace tun kafin ma Jiddan tayi magana, ran safeera be yi mata dadi ba, ta juya zata bar wajen Jiddan ta mike da sauri ta ce


"Amira bari muje aji zan karasa rubutu."


"Tsayani." Tace da sauri tabi bayan ta, hakan ya sakata sakin fuskar ta suka koma ajin suka zauna, ta karbi eggroll din taci kadan, ta ajiye sauran.


Tun daga ranar Safeera ta zama kawarta, duk da da farko bata sake da ita ba, sai da ta fara fuskantar ta da halin ta, she's very simple ba kamar sauran yan ajin nasu ba, dan ba kasafai suke mata magana ba ma musamman tunda suka gano bata iya turanci ba. Dan ma suna shakkar Safeeran ne da wani abun ba haka ba, ita take koya mata duk wani abu da tasan zai saka yan ajin su kalli Jiddan a matsayin koma baya ko kuma ba level din su bace ita

    Sosai ta bada himma akan karatun ta, duk kuwa da tana shan bakar wahala amma haka ta dage, ko yaushe ta zauna tana rike da littafi, babu maraya sai rago, kuma babu abinda ba zaka iya ba in dai ka saka ranka. 

   Rabin rayuwar ta a bangaren Yaya take yin ta, hakan yasa Amira da Maryam suma ko da yaushe suna shashen, bata bin su wajen su saboda ko taje ma bata samun fuska a wajen Maman dan kiri-kiri take nuna mata bata son ta tare da yaranta, sanin haka yasa itama ta tsaya iyakar matsayin ta, bata zak'e ba bare a samu matsala.

   Tsakanin ta da yaran gidan musamman Fauwaz,amira da Maryam ba zata ce akwai wani banbanci da suke nuna mata ba, zuwan ta ma ya kara musu shakuwa da Anty tunda ko yaushe suna manne da ita idan basa wajen Yaya toh suna part din Antyn. 

    Bangaren islamiyya ma alhamdulillah, da naci da dagiya tana gane komai a hankali a hankali kan nata yake sake budewa, tun bata ganewa har ya zamana ta soma dauka sosai fiye da yadda tayi tunani. Hakan yake karawa Anty Jin dadi dan tana kyautata zaton ilmin shine gatan Jiddan ba komai ba. Aikin gida duk ta hanata komai girki kawai take tayata shima saboda bata so a samu matsala ko gaba idan tayi aure.

   Sau kusan uku Tariq na kiranta bayan tafiyar sa, idan suka gaisa sai yayi mata maganar Jiddan duk da baya fadin sunan ta sai dai yayi alamar yadda zata gane, dariya kawai takeyi tace toh zaa yi, sau daya ta bawa Jiddan labari da ta ga bata nuna interest dinta akan maganar ba sai kawai ta share itama.

   

***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin ikon Allah Jidda ta kammala jss 3 zata tafi ss1, Amira Ss2, Maryam ss3 ita da Umaima. Hutu Anty ta shirya musu zuwa chan garin su, ta fadawa Baba yace idan sun shirya zai saka driver ya kaisu amma kwana uku kawai zasuyi su dawo. Shiru tayi dan taso ace ko sati ne su yi, kallon ta yayi yaga kamar tana tunani yace


"Akwai wani abun ne?"


"Eh wai da ko sati ne."


"Kwana uku nace, ba kari kuma."


"Toh Jiddah ko zaa barta ita tayi satin saboda Yaya."


Da sauri ya waigo dan da har yayi shirin shigewa dakin sa


"Ban gane ba, an yi hutun islamiyya ne?"


" A'ah."


"Toh kwana uku zakuyi ku juya, ni ne uban Jidda ni nake da iko da ita a yanzu ba Yaya ba, idan kuma iyakata zaa nuna min toh."


"Allah ya baka hakuri."  Tace tana sauke kanta a kasa, daki ya shige be sake magana ba, Mama dake tsaye tun dazu a kofa tayi tsaki ta shigo fuskarta a hade, ta kalle ta itama ta kalle ta, ta sake jan wani tsakin sannan tace


"Ki gama munafuncin ki da shishigin ki da son lallai sai kin nana masa yar da ba tasa ba, zaki wani fake da munafunci da iyayi."


Tashi tayi kawai tayi hanyar fita ta bar mata dakin, dan dama basa taba hada zama waje daya dan in dai tana wajen Baba baya ko kallon Antyn sai itace ma zata dinga kokarin sako ta a hirar su irin na kissar nan,shiyasa ta shafawa kanta lafiya take iyakar kokari wajen gujewa abinda zai dagula mata sukuni.


***A falon ta, ta same su Amira na karanta musu wani story book, Adil ne akan kafar Jiddan, Maryam kuma na ta saman kujerar tana mata tsifa, wajen kwana biyu kenan Aunty tana fama da ita akan tsifa dan da gaske ta tsani abinda zai sata taba gashin ta, shiyasa tsifa ke mata wuya sosai. Su kuma tsawon gashin nata ne yake birgesu dan ranar da ta fara bude kanta Amira da Maryam tamkar zasu lashe ta, suka dinga tabawa suna dama sune da an ga gayu, ita dai murmushi kawai takeyi dan ita be wani dadata da kasa ba. Duk sati ake basu hairstyle a school shiyasa ma take yin kitson amma shima dan ba yadda zatayi ne seniors din nan ba mutunci ne dasu ba. Satin da aka soma exams kuwa ba'a basu hairstyle din ba shiyasa ta barshi har sai da Anty tayi magana.

   

"Tsifar kike tayata Maryam?" 


Anty tace tana zama daga kujerar dake daura da kofar shigowa part din nata dan fita zata kuma yi, 


"Wai bata son tabashi, shine nace ta kawo nayi mata. Nice nake da gashin Jiddah tab, Ai da an ga gayu wallahi, bama fa shi da wahalar tsifar saboda laushin sa"


"Lallai kam, kin taimaka mata. Idan kun gama Jiddah ki hada kayanki wanda zamu tafi dasu, na fadawa Baba yace kwana uku kawai zamuyi amma."


Tashi tayi tsaye da sauri cikin tsananin jin dadi tace


"Wayyo zan je naga baffanah, yaushe zamu tafi?"


"Gobe da safe in sha Allah, ki duba abinda bashi da wanki ki wanke."


Murna ta hau yi, fuskarta ta gaza boye farin cikin da take ciki, dariya suka dinga mata, Amira ta kalli Anty tace


"Anty dan Allah zan rakaku."


"Na'am?" Sai kuma tayi shiru dan tasan ba lallai uwarta ta barta ba, ba kuma dadi tace wa yarinyar a ah, shirun ta ya saka Amiran ta zata ko ba zata da ita bane


"Dan Allah Anty."


"Ba k'i nayi ba Amira, amma ki tambayi Mama idan ta barki shikenan sai mu tafi."


"Nima zan je."


Muhammad yace ashe suna jin abinda ake cewa,


"Nima." 


Usman ya fada yana mikewa yazo wajen Antyn, sai Muhammad din ma ya tashi suka tsaya mata a gaba


"Shikenan toh duk zani daku."


"Yeeeh yeeeh." 


Suka hau tsallen murna, murmushi kawai Anty take cike da jin dadi, a kalla zuwan Jidda ya kara mata shakuwa da yaran sosai. Duk da tasan ba lallai Maman ta bar su ba, amma ko a hakan ita taji dadi sosai ba kadan ba.

   Tunanin yadda Amira zata fadawa Mama takeyi gashi har ga Allah tana son zuwa taga yadda garin yake da labarin da Jiddah take basu.


"Idan na fadawa Mama zata yarda?"


Ta tambayi Maryam, dage kafada tayi alamar oho sannan tace


"Kema kinsan wace Mama, da hakura kawai kikayi."


"Ba zan hakura ba, i will try my luck."


"Allah ya bada sa'a toh." Tace tana mikewa


"Bari kiga naje na aro wayar Ya Safiyya nayi game."


"Tab! Allah sa ta baki."


"Zata bani ai tasan nima an kusa siya min tawa."


"Sai dai haka, moha taso ka rakani wajen Mama kaji, Allah yasa ta bar mu."


Rike hannun sa tayi suka nufi bangaren Baba da suka san zasu samu Maman achan, kuma tasan in dai Baba yace yes Mama ba zata hana ba sai dai zata sha rakwashi da kallon banza, duk wannan daga baya ne in dai har sun tafi. 


Sallama tayi daga kofar Muhammad ya kwace hannun sa ya shige ciki ita kuma ta tsaya tana jira a bata izinin shiga.


"Uwata shigo mana."


Baba yace yana gishingid'e yana duba wayar sa, shiga tayi kanta a kasa gabanta na dukan uku uku, ta ki yarda ta hada ido da Mama kwata-kwata, ta zauna a gaban Baban sannan tace


"Em em dama."


"Dama me? Ina jinki."


"In dai kaga Amira na haka ai akwai abinda zata tambaya."


"Ina jin ki toh."


"Dama Baba, so nake na bi Anty nima."


Da sauri Mama ta ajiye abun hannun ta, ta kalli Amiran da kanta yake kasa, ranta yayi masifar baci, ta kalli fuskar Baban ta karanci yanayin sa, fuskar sa a sake yana shirin yin magana ta rigashi


"Kin manta da bikin ummul? Ko ba zaki ba?"


"Wannan satin ne bikin?"


Baba ya tambaya yana kallon Maman


"Eh wannan ne, har sun yi anko ma fa, inaga dai ta manta,ummul ba zata ji dadi ba idan baki je ba."


"Ummul ba sa'ar Maryam bace ba? Ko Safiyya ma, ba komai sun wakilci uwata, ki shirya ki bisu kinji."


"Nagode Baba, Allah ya saka da alkhairi."


Sai ta tashi da sauri ta fita, ba tare da ta hada ido da Maman ba, tana fita Muhammad ma yace zai je, shima Baban yace toh. Kasa karasa abinda Maman take tayi a dakin, ta fice da sauri dan idan ta zauna ba zata iya rike bacin ranta ba.

[11/25, 3:54 PM] Rano2:             SL


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links