Free Page ( 3)
©®Hafsat Rano
***
***Kiran farko akan kunnen ta, saboda yadda jikinta ya saba da tashin wuri, dan tun bata iya tashi ba har ya zame mata jiki, ko bata ji kira ba zata mike, wataran ko sallah Lami bata barin ta tayi zata fara sakata aiki, itace dauko itace, itace debo ruwa da sharar gidan baki daya dan duk sai tayi su kafin ta tafi makaranta wadda take da yar tafiya tsakanin su, haka ta saba ta goge tun shekarun ta basu kai haka ba, babu wani aiki da yake bata wahala sai dai idan ba sunan sa aiki ba. Zama tayi jugum tana kallon yanayin dakin, ta kalli Usman da yake bacci a gefenta, tana matukar son yara, haka take ko a gida bata da aiki sai jajibo yaran makota kafin Lami ta hanata. Turo kofar akayi, Anty ta shigo sanye da Hijabi, ganin ta a zaune ya bata maki
"Har kin tashi Jiddah?" Tace tana karasowa cikin dakin
"Tun dazu na tashi."
"Toh maza tashi kije kiyi alwala muyi sallah, Usman be yi kuka ba ko?"
"A ah be yi ba."
"Toh yi alwalar maza kizo muyi sallah."
"Toh." Tace ta sakko, taje tayo alwala suka fara yin raka'atanil fajr sannan sukayi subh. Al'kurani ta dauko suka fara daga Falak da Nasi, zuwa in da Jiddan ta tsaya a karatun, ta yaba sosai da yadda take karatun dan batayi tunanin hakan ba duk da baffa ba daga nan ba wajen riko da addini. Suna zaune tare har garin yayi sha, tace mata ta koma ta kwanta, ita kuma ta fita zuwa shashen Baban dan tasan zuwa lokacin ya dawo daga masallaci. Tana fita ta fito itama ta je kitchen ta dauko tsintsiya da faka dan ko ta kwanta ba wai iya baccin zatayi ba, bata saba ba, ta share falon tas ta gyara kitchen ta wanke kwanukan da suka bata jiya da daddare sannan ta wanke toilet, bayan ta gama usman ya tashi, ta rakashi bandakin tayi masa alwala da brush sannan tace yayi sallah, be iya ba tunda karami ne haka yayi tana kallon sa.
Wajen takwas Antyn ta dawo shashen sai dai tsananin mamaki ya kamata, ganin yadda ta gyara ko ina kamar ba ita ba, murmushi kawai ta dinga yi tana wa Allah godiya da ya duba ta ya bata 'ya me taimaka mata. Kunun da Abu ta dama tazo kawo wa kawai taga yadda ta gyara ko ina, albarka ta dinga saka mata sannan tace taje tayi wanka zata je ta gaida Baba idan sun gama karyawa.
A babban falon suke karyawa gaba dayan su, har Baban dan yace cin abinci a tare yana kara shakuwa, shiyasa suke zama kowa yaci da dan uwansa musamman weekend da baya fita da wuri sai rana ta daga. Fitowar ta kenan daga wanka ta gama saka kayanta tana goge ruwan da yake akan fuskar ta Amira da ta sato hanya ta leko dakin fuskarta a sake,
"Kawata." Tace tana sako jikinta cikin dakin
"Amira." Ta kira sunan ta da taji Antyn ta fada jiya, hakan yayi ma Amiran dadi
"Jiddah ko?" Kai ta daga Mata
"Kizo muje mu karya, kinsan gaba daya muke yin breakfast har Baba."
"Hadda ni?"
"Eh, kema kin zama yar gidan nan ai, taho muje."
Ta ja hannun ta suka fito, bata so ba dan tana da jin kunya sosai da rashin saurin sabo, bata kuma saba da mutane da yawa ba daga ita sai baffanta sai Inna Lami. Sun firfito dukkan su kowa na zaune wasu a kasa wasu a saman kujera, su biyu ne mata a zaune Maryam, sai Safiyya wajen su Amiran ta jasu, tace
"Ya Sofy, Mero, ga Jiddah."
"Sannun ta."
Safiyyan tace tana danna wayarta, babba ce dan da alama duk ta girme su, murmushi sauran sukayi mata hakan ya sakata sakin jikinta kadan ta zauna a gefen Amiran ta makale. Maman su ce ta fito ta wata kofa taci ado sosai, kamar wadda zata tafi gasar kyau, babba ce dan akalla shekarun ta zasu kai arba'in da biyar amma ba zaka taba cewa ta kai ba saboda gyara da kyawun jiki. Duk suka gaishe ta ta amsa idon ta akan Jiddan, da sauri tace
"Ina kwana?"
"Lafiya lou bararoji."
Tace tana wucewa kujerar da Muhammad da Usman suke zaune,
Suka tashi ta zauna tana hararar Amira. Bararojin ne ya dinga yawo a kwakwalwarta har akayi sallama aka shigo falon. Baba ne ya shigo Anty na biye dashi itama tayi wanka sai dai shigarta very simple ba kamar Mama ba, gaishe da Maman tayi da yake a gaban Baba ne ta amsa a sake, zama sukayi dukka sauran yaran suka gaida Antyn da Baban itama sai tabi sahun su ta gaida Baban.
"Zo 'yata,yanzu nake shirin tambayar ki dama."
Tashi tayi a kunyace taje gabansa ta durkusa ya shafa kanta
"Ki saki jikinki kinji, nan gidanku ne ga yan uwanki nan dukkansu,duk abinda kike bukata ki sanar dani kinji?"
Daga kanta tayi alamar toh, ya sake shafa kanta yace
"Yawwa, Allah yayi muku albarka baki dayan ku."
"Amin."
Suka amsa gaba daya, ran Mama ya baci sosai amma bata so ta nuna ta danne tana kallon Safiyya da itama ita take kallo.
"Maryama jeki kira yayanku, bansan me suke ba na kuma fada musu da wuri zamu fita."
"Wani wajen zaku ne?"
"Eh zamu je a dauko Yaya, hutun ya isa haka gashi lokacin komawa ganin likitan ta yayi."
"Gaskia."
Tace a kasan ranta kamar ta kurma ihu, bata san zaman Yayan tare dasu musamman tun bayan da ta tirsasawa Baban ya kara aure tun daga sannan ta tsane ta, dan tun asali dama Yaya bata son ta, shiyasa sai da tayi yadda tayi ta saka ya auro mata wadda ko a mafarki bata taba kawo ta a matsayin kishiyar ta ba,yar kauye kuma yar talakawa, ita din yar masu kudi ce sannan tana business dinta tana samun kudi sosai, tun daga sannan ta kullaci Yayan, tafiyar da tayi tsawon wata guda ya bata damar sakewa a cikin gidan, jin zata dawo yanzu ya saka ta kasa ko sakewa taci abincin, ta tashi tace zata tafi, Safiyya ce ta rike mata jaka suka fice tare.
A harabar gidan ta hadu dasu, Fauwaz ne a gaba sai shi a baya yana nannade hannun rigar sa zuwa sama, kansa kasa fuskar sa babu yabo babu fallasa Safiyya ta kira sunan sa ganin zai wuce su
"Ya Tariq!" Tsayawa yayi yana kallon ta, kafin yace
"Mah, fita zakuyi?"
"Eh, zamu je cikin gida."
"This early?"
"Past 9 fa, kai kake ganin yayi wuri."
"Ok a gaida su."
Ya sa kai ya cigaba da tafiya zuwa main part din, mota suka shiga Fauwaz ya bi bayan sa, ya sameshi har ya zauna a gefen Baban suna magana, Zama yayi shima ya gaishe da Baban dan shi kadai ya rage a falon duk sun shige ciki. Breakfast din sukayi a tare, sannan Baba yace Tariq yaje ya sauya zuwa manyan kaya, ba a san ransa ba ya chanja zuwa shadda dinkin rigar da kadan ta wuce guiwar sa, ya rike hular a hannu ya fito yana jin shi a takure.
Cikin gidan ya shiga, ya bi corridor din da zai kaishi part din Antyn, ya shiga bakin sa dauke da sallama kasa-kasa. Su uku ne a zaune a falon, Saudah, Amira da Umaima. Fitar Mama ya basu damar biyo Saudan suka zauna suna janta da hira, Amira ta saka musu waka suna ji ya shigo, a rikice ta danne power botton din wayar ta kashe ta gaba daya, kallon ta yayi ,yayi kamar be ji komai ba, ya wuce ya zauna a cikin daya daga kujerun falon yana ciro wayar sa. A tare suka hada baki da Umaima suka gaishe shi, yayi kamar be ji ba, yana cigaba da danna wayar sa. Sum sum sum suka fice ya zama sai Jiddah kawai a falon
"Ke je ki kira min Anty."
Yace be ko dago ba, ta mike ta nufi dakin Antyn ta kwankwasa, daga ciki tace mata ehem alamun tana toilet, dawowa tayi ta tsaya daga bayan kujerar tace
"Tana bayan gida."
Dagowa yayi jin abinda ta fada, sai a lokacin ya ganta, fuskarta fiki fiki, yar firit kamar ka hureta ta fadi saboda rama, mamaki ya kamashi ganin ta
"Wacece ke?"
Yace yana kafe ta da ido, sosai ta duburburce ganin yadda ya kafe ta da ido, idanun sa manya sosai masu ban tsoro
"Na'am?"
Tace cikin hada kalmonin
"Who are you? Daga ina kika zo?"
Ya sake tambayar ta har lokacin kallon ta yake,be taba ganin ramammiya karmashashiyar yarinya irin ta ba, shi ya zata ma aljana ce, saboda tsabar rama har wani rami ne a fuskarta ya shiga ciki. Bata san amsar da zata bashi ba, sai kawai tayi shiru tana wasa da hannun ta. Anty ce ta fito a daidai lokacin
"A ah, Yaya boss yaushe ka shigo?"
"Ban dade ba, ina kwana?"
Yace yana dauke kansa dga kallon yarinyar
"Lafiya lou, baku tafi ba ashe."
"Eh Baba be gama shiryawa ba, shine nace bari na shigo mu gaisa,wacece wannan Anty?"
"Auw wai Jidda? Jiya na taho da ita yata ce, yar wana ce amma ta dawo hannu na da zama."
"Ok." Kawai yace yana tabe bakin sa, sai ya mike
"Nima gobe zan koma in sha Allah, zan dade wannan karon har sai na kammala sannan zan dawo."
"Wai, Masha Allah, zamuyi kewa. Allah ya bada saa da nasarar abinda aka je nema."
"In sha Allah Amin."
Yace yana ficewa, d'aga murya tayi tace masa a dawo lafiya ya amsa daga chan ya karasa ficewa.