SANADIN LABARINA 22


   Page (22)



***A k'asa ta zauna daga farkon falon, Aunty kuma ta zauna daga gefen Baban, kallon tausayi yake wa Jiddan dan sai da ya gama kallon ta sosai sannan ya shiga bayani cikin salon da yasan zai wanke kansa ya kuma wanke Baffa, sannan ya samu ta karbi abinda suka zo mata dashi, nasiha sosai yayi mata akan rayuwa sannan ya kawo maganar auren, wanda ya sakata jin Abu ya tsirga mata tun daga sama har k'asan kafafunta, ta kalmashe kafar cikin son rage abinda take ji din duk da bata san menene ba.


     Dukkan maganganun da Baban ya fada mata sun yi matukar tasiri a gareta, ba zata iya taba kin Ya Tariq ba, tunda har ya fito daga tsatson Baba, mutumin da yake da girma da k'ima a idanun ta. Tana kyautata masa zato, tana fatan yayi halin Baban ko da ba dukka ba. Maimakon ta koma dakin ta, sai tayi bangaren Yaya dan tasan idan ta keba kanta toh dole tunane tunane zatayi tayi, gwara tazo ko ta rage daren.   

   

***Tunda suka bar kofar gidan su Jidda yake kwance a dakin Farouk, kamar wanda ruwa ya cinye haka yake ta kwanciya, babu abinda ya saka acikin sa, sai wani irin suya da kirjin sa yake, babu yadda Farouk be yi dashi ba, akan ya saka ko da wani abu ne a cikin sa, amma yaki sam. Sallah ma da kyar ya tashi ya hada azahar da la'asar haka magriba da Isha. Kansa na tsakankanin kafafuwansa bayan ya idar da sallar Farouk ya sake shigowa, ya dube shi a in da yake zaune ya girgiza kai,ya kira sunan shi, be amsa ba sai dagowa da yayi ya kalle shi


"Bro dan Allah man up mana, ka tashi muje wajen Safeera muyi mata magana, may be ta iya convincing Jiddan, ni nayi mamaki ma wallahi, na zata kace bata da saurayi ko?"


"It's too late, Jidda bata so na, nasan kuma ko shekara dubu zan bata ba zata taba so na ba, na gani a cikin idon ta. Dama nayi ma kaina alkawari idan har tayi rejecting dina ba zan takura mata ba, zan hakura da ita. You can't force anyone to love you."


"Amma kuma you can try your best to win their heart, kayi saurin given up."


"Ba zaka gane ba, inaji a raina ba zan iya cigaba da rokonta ba, har kusan kasa na kai ina rokon ta, and she said no, me kake so nayi?"


"Fight for your love mana, don't be a looser, ka bata time ta kara tunani sosai, dama kamar kayi rushing abun, kaga fa akwai yarinta akan su, kila ma bata san menene soyayya ba, she's just nervous."


"Kasan kiyayya? Ita na gani a cikin idanun jidda, na hakura, bata so na ba zata kuma taba so na ba."


"Shikenan, Allah ya mana zabin alkhairi, karka wahalar da kanka toh, eat something, kalli yadda ka koma, mom ta kira wayar ka na daga nasan tana jiran ka."


"Muje ka sauke ni, ba zan iya cin komai ba."


"Ko tea ne kasha dan Allah "


"Zan sha idan na koma."


"Ok muje toh."


Hannu ya mika masa ya tashi, yayi kamar zai fasi sai da Farouk ya tallafe shi, sannan ya taimaka masa zuwan wajen motar.


***Yadda Mama taga rana haka taga dare, kamr ta jawo gari ya waye haka taji. Ana idar da sallah aka kaita airport ita da Safiyya sai securities biyu, kafin tara tana Kano, kai tsaye doshi part din Baban lokacin ko tashi be ba, Aunty na falon tana hade masa wasu takardu waje daya, knocking akayi, ta tsaya da abinda take cike da mamakin wanda zai knocking a part din Baban dan ko Usman baya biyo ta bare tace shi ne.

  Wajen kofar taje ta dan leka ta jikin dan opening din dake jikin kofar bata ga kowa ba, sai tace waye


"Matar gidan ce."


Rass! Gaban ta yafadi jin muryar Maman, ta tabbata ba zuwan lafiya bane musamman da tunda tatafi idan ba sallah ba, babu abinda yake kawo ta, murda key din tayi ta bude kofar, ta matsa baya da sauri ta shigo ciki.


"Sannu da zuwa." Tace ganin tana mata kallon sama da kasa, bata amsa ba, sai jan dogon tsaki da tayi cikin bacin rai tace


"Munafuka algunguma, muguwa maci amana, saboda ke bakar makira ce, shine kika san yadda kika yi, kika shiga kika fita kika sa aka kakabawa Tariq gwanjon yarki, bayan yadda kika kakabawa mahaifin su kula.da ita, wato dan ina kyale abubuwa ina dauke ido shine har kika samu damar hada wannan shirmammen auren wanda bashi da maraba da auren gangan a waje na."


"Haba Maman Fauwaz, kamar yadda kika ji labarin auren nan wallahi haka naji, bani na hada ba, Yaya ce ta hada kuma nima kaina ba wai inaso bane."


"Dallah rufe mana baki, ai ke babu kalar munafuncin ki da ban sani ba,zanzo kanki bari na gama da shi."


Sai tayi fuuu ta bude bedroom din Baban ta shiga. Zuciyar Aunty ce ta shiga yi mata zafi, ta gaji ta gaji da cin kashin da aunty take mata, ta gaji da tozarcin ta, tana kyale ta ne ba wai dan tana tsoron ta ba, sai duk dan a zauna lafiya, ta amsa tayi laifi a lokacin da ta auri Baba amma ya zatayi da kaddararta? Shikenan ace abu yaki ci yaki cinyewa? Ta kai karshe a wannan karon sai dai duk abinda zatayi tayi amma ta daina bin ta.

  Kin fita tayi daga dakin kamar yadda take yi a baya, ta cigaba da aikin da take tana jiyo hayaniyar Maman sama-sama. 


**Tunda ta shiga dakin ta saka Baba a gaba tana banbanmi, me kulata ba, yana jinta duk abinda zata fada ta fada aure dai ya riga ya dauro, kuma tunda har Jidda ta amsa masa da ta amince shikenan, bashi da matsala da kowa dan yayi wa Yaya abinda take so. 

  Duk yadda Mama taso tunzurashi sam yaki bata hadin kai, cigaba da danna wayar sa yayi rabin hankalin sa na kanta rabi na wayar. Kamar kunnen sa ne yake masa gizo sanda yaji maman na cewa


"Duk wadda ta tsara hada auren nan wallahi ban yafe ba, ko wacece ta cuce ni." 


Sai ta fashe da kuka ganin Baban ya ki kulata, saukar mari taji akan fuskar ta, baban dake tsaye yana huci a gabanta ya nuna ta da dan yatsa


"Duk abinda zaki fada a kaina ko kan mahaifin jidda ko Halima ko ita Jiddan duk ki fada ba zan hanaki ba, amma a hir dinki kika sake sako mahaifiyata, dan dukkanku albarkacin ta kuke ci, kuma wallahi wallahi wallahi, kinji na rantse ko? Idan har kika ce zaki daga min hankali akan dan na yiwa Tariq aure, wallahi sai na nuna miki kuskuren ki,kuma ko da wasa kika kira Tariq ko kika saka yaran nan suka kirashi da maganar wallahi sai mun samu babbar matsala."


"Naga sam baki san kaddara ba, ba kuma ki isa ki ce zaki fadi magana akan Yaya ba, baki isa ba wallahi."


Wajen da ya mareta, ta rike cike da tsananin mamaki, tunda suke da Baba, be taba ko da daga mata murya ba, bare har yakai ga taba lafiyar jikin ta,komai take so tun daga zamanin kuruciya har gobe shi yake mata  

   Ko kwakkwaran motsi ta kasa yi daga wajen da take tsaye, ta san shi sarai bashi da sauki idan har yayi fushi, bare fushi irin wannan da bata taba ganin yayi ba. Ficewa yayi ya barta a dakin,ya samu Aunty a falo ganin yanayin sa ya sakata yin shiru dan da har zatayi magana, har ya kai kofa sai ya juyo yace.


"Ku fara shirye-shiryen tarewar ku a wannan satin."


Daga haka ya saka kai ya fice, be jira yaji ko ta amsa ko bata amsa ba. Kasa fitowa Mama tayi daga dakin saboda tsabar kunya, a mareka kishiya tana ji ai ba karamin zubar maka da mutunci bane, a tunanin ta Auntyn zata fita bayan Baban ya tafi, taji shiru shiru, sai kawai ta yanke shawarar fitowa, ta fice fuuu, bata ko dubi part din Yaya ba, ta fada mota, dan dama a chan main house dinsu aka sauke Safiyya, saboda haka chan ta koma, ta samu Hajiya Babba da maganar, da duk abinda ya faru da abinda Baban yace, shawara ta bata akan ta bar komai har zuwa dawowar Tariq din, dan suna da yakinin ba zai taba amincewa ba.



Da daddare suka koma, ta tattaro su ta fada musu abinda Baba yace akan maganar fadawa Tariq din, dama Safiyya da Fauwaz ne kawai suke magana dashi, kuma wajen kwana uku kenan ma basu yi magana ba, dama kuma Fauwaz ba zai fada ba dama Safiyya ce itama tunda aka yi maganar ba zata fada ba.



***Mom na zaune a falo Isma'il ya shigo, yana tafiya kamar wanda zai fadi, 


"Innalillahi, me faru?" 


Tace tana yin wajen sa, a cikin kujerun falon ya zauna yana jujjuya kansa da yake masa wani irin mahaukacin ciwo, Safeera dake kan dinning tana dinner ta taso da sauri, tazo ta durkusa a gabansa tana tambayar


"Ya Isma'il me ya same ka?"


Da kyar ya bude bakin sa, da yayi masa nauyi yace


"Jiddaaa."


"Me ya samu Jiddan?"


"Ba...ta..so..na." 


ya fada a rarrabe saboda tsabar yadda yake ji, ga yunwa da ta hadar masa ta sake taimakawa wajen rashin kuzarin sa. 


"Kirawo min Dr Aminu Safeera, yi sauri yazo ya duba shi, wannan abu har ina, dama wallahi kamar nasan za'a yi haka, naji tsoron ganin yadda kake son yarinyar nan, kalle ka yau daya Ismail, akan soyayya ka koma kamar wanda yayi jinyar shekaru?"


Jujjuya kansa yake, Safeera ta kirashi ta dawo gaban Ya Isma'il din cike da tausayin sa, ita kanta ta hango faruwar hakan dan tasan Jidda, tasan idan har bata son shi ba zata taba barin shi yayi ta fama ba, zata fada miki ne kai tsaye, sannan kuma ba zata taba sauya raayinta ba.


❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥


*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*


*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*


*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*


😄😄😄😄😄😄😄

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links