SANADIN LABARINA 21

 

   Page (21)


***Alawa da goro aka raba sannan daya daga cikinsu yayi rabon kudi sosai, sannan suka bawa Baffa kudi masu dan kauri kafin suyi sallama su tafi, nan da nan labarin ya zagaye dukka kauyan. Zuciyar Baffa cike take da farin ciki mara misaltuwa, ya rasa in da zai tsoma kansa dan murna..Allah ya dube shi ya dubi maraicin Jidda yayi musu sauyi rayuwar da basu taba hasashe ba.

   Da magribar fari Baba ya shigo gidan, yadda yake cike da farin cikin abinda ya faru ba zai bari har sai Yaya tayi bacci ba sannan ya shigo gidan,shiyasa ya rage schedules dinsa ya barwa gobe.  Dukkan lissafin YAYA akan wannan lahadin ne, Allah Allah tayi, satin ya zagayo amma sai ta ga yayi nisa sosai, gashi bata son a samu matsala komai kankantar ta, shiyasa take cike da wasi-wasin jiran zagayowar ranar. 

   Idar da sallah magriba kenan da tayi, ta mike kafafunta da suke dan mata ciwo akan abun sallar, tana rike da tasbah tana ja lokaci zuwa lokaci tana daga kai ta kalli cikin dakin nata kamar me neman wani abu. Sallamar Baba ya sakata katse abinda take ta mike da dan saurin ta, ta fito falon tana son ta tabbatar shi d'in ne ko kuma dai  muryar sa ce take mata gizo, shi din ne kuwa,nan da nan ta hau murnar ganin sa kamar wannan ne zuwan sa na farko wajenta saboda tsabar yadda ta cika da farin cikin ganin sa, tasan zai iya fasa zuwa wannan satin idan wani abun ya taso masa shiyasa take ta Allah Allah yazo.


"Yaya irin wannan farin cikin duk na gani na ne?"


Yace bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa kamr ko da yaushe


"Eh da murnar ganin naka ma, da kuma murnar na gama cire rai ba zaka zo wannan satin ba, kasan kuma alkawarin mu."


"Yaya baki manta ba?"


"Na manta kace? Tab!"


"Toh Yaya albishirin ki."


"Goro, fari kal kal."


Ledar dake cike da goro da alawa ya mika mata gabanta, taja ta bud'e tana leka ciki


"Me muka samu?"


Ganin alawa da goro yasa ta kalli Baban da sauri


"Ba dai aure kayi ba?"


Darya ta bashi, yayi murmushi yace


" A ah Yaya, goron auren Jiddah ne da Tariq."


"Dan Allah! Kai kai kai kai Masha Allah, Masha Allahu, da gaske kake wai?"


"Da gaske Yaya, mahaifin Jiddah mutumin kwarai ne,wallahi hanya ce ta bi damu, sai na gabatar masa da maganar,anan yayi tsalle ya dire sai dai ayi komai a gama, kuma fafur yace shi bazai karbi sadakin Jidda ba dan nine mahaifin ta, naji dadi kwarai da karramawar da yayi min, su kansu wadanda muka je tare tunda muka dauko hanya suke yaba masa."


"Kai Alhamdulillahi, Abu kamar almara?"


"Wallahi Yaya, kinga dai abinda Allah ya tsara, ko jiddan ba'a fara tuntuba da maganar ba, Allah yasa kar taga rashin kyautawarmu."


"Ba dai Jidda ba, na gamsu da tarbiyyar ta, ko ma zaa bijire sai dai wanchan sahoramin, shima kuma be isa ba."


"Haka ne."


"Allah ubangiji ya saka muku da gidan aljanna, ka gama min komai a duniyar nan, Allah ya kare ka daga sharrin makiya, ya sa 'yayanka kai ma su rama maka, naji dadi nagode nagode."


Sai ta fashe da kuka, kukan da ya saka Baba mikewa dan sarai yasan halin Yaya, yanzu sai ta rikice musu, 


"Amin Yaya, Amin Amin."


Sai ya fice dan yana jin kukan nata har ya fara sauya salo, duk da kukan farin ciki ne amma yasan tsaf zata birkice tayi tayi tana farfado abubuwan da suka faru da irin fadi tashin da tayi dasu suna kanana musamman shi da zai iya cewa itace koman sa a rayuwa, ita ta tsaya masa har yayi karatun da a yanzu yake alfahari dashi.


Waya yayan ta dauka bayan ta ajiye kayan a gefe, ta dinga dannawa tana kiran duk wanda hannun ta yazo kan number sa, tunda ita ba iya karatun tayi ba bare ta gane sunan waye, idan ka daga taji ba kai take nema ba sai kawai ta katse, haka tayi ta kira har tazo kan number Mama da tunda aka saka mata number ba su taba waya da ita ba,kowa dai yana da ta kowa ita Yaya Safwan ne ya saka mata a wayar. Mama na zaune bayan sun fito hutu daga wani taro na matan ministoci, suna zaune a wajen da aka tanadar domin hutawar su, suci abinci da sallah. Da la'asar aka fara taron da magriba tayi sai aka tafi hutun minti talatin sai a sake komawa zuwa isha a tashi. Hajiya huwaila ce a gefenta dama tunda tazo Abuja da ita suka fi sabawa sosai. wayarta ce ta shiga vibrating, ta ciro ta daga yar madaidaciyar jakarta, cike da mamaki take kallon number Yaya, dan bata taba kiran ta ba, bata kuma san akan dalilin da zai saka Yayan kiran ta ba sai dai idan tabbas ba lafiya, tashi tayi da dan saurin ta, ta fita daga wajen sannan ta daga kira


"Assalamu alaikum."


Kallon wayar Yaya tayi jin muryar ta, har zata kashe sai kuma taga ai ita tafi kowa chanchanta da taji wannan labarin, sai kawai ta amsa gaisuwar da take mata


"Lafiya lou, ya yaran?"


"Lafiya lou."


"Kowa lafiya dai ko?"


"Lafiya Alhamdulillah."


"Toh Masha Allahu, kin samu labarin abun farin cikin da ya same mu ko?"


" A ah Yaya, me ya faru?"


" Batun auren Tariq da Jiddah mana, Alhaji be fada miki ba? Duk da dai ni dashi kadai mukayi maganar na kuma hane shi ko Tariq din kar ya soma fadawa har sai yazo da kafafun sa."


Wata irin zufa ce ta shiga karyowa Mama, ta dinga jin kamar kunnenta be ji mata daidai ba, ta kasa bude baki bare ta amsa duk bayanin da Yayan take mata. Daina gane komai tayi har Yayan ta gama jawabin ta, ta kashe wayar.  Wata kujera ce a gefen wajen ta karasa da sauri wajen ta zauna duk ta rikice "Auren Tariq da wannan figalalliyar yarinyar nan? Sannan a rasa wanda zai nemi shawarar ta? d'an ta data haifa a cikin ta, a rasa wanda zai nemi shawarta saboda tsabar karfin hali da nuna iko. Sai yau ta kara tabbatar wa Yaya bata son ta, haka kuma bata son yayan da ta haifa, dan idan har tana son Tariq ba zata taba masa irin wannan auren ba, kamar wani karamin yaro ace har Tariq zaa iya irin wannan auren? Lallai duk wanda ya shirya wannan be so zaman lafiya ba, ko waye kuwa. Tsanar aunty ce ta kara karuwa sosai a zuciyar ta, dan tasan tabbas da saka hannun ta aka kakabawa Tariq munafukar yarinyar me zubin yunwa. Tunanin ta ne ya kawo mata wayar da taji Baban nayi da Tariq, wato dama abinda yake nufi kenan, shine suka boye mata dan kar ta hana, lallai kuwa dole ne ta nunawa Baban itama tana da iko akan Tariq dan ba shi kadai ya haife shi ba. Kasa zama tayi a karasa event din, ta fice bayan ta nemi ayi mata afuwa saboda tasowar wani babban al'amari.

   Tun a hanya take jerawa Baban kira amma be dauka ba, kira ta cigaba da yi dan bata jin idan har be dauki wayar ta ba zata iya zama bata je ta same shi ba. Har ta karasa gidan be dauka ba, ta shiga yaran duk suka tashi suna kallon yanayin ta, zare dankwalin kanta tayi ta jefar da jakar hannun ta da Amira take shirin karba, 


"Wallahi ba zai yiwu ba, ni za'a cutar saboda an ga sanda Muhammad ya mutu nayi hakuri, shine yanzu saboda tsabar wulakanci za'a yiwa Tariq irin wannan wulakantaccen auren, wallahi ba zai yiwu ba."


"Mama please calm down, menene ya faru?" 


Safiyya tace tana rike hannun Maman, ta taimaka mata ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, Maryam tayi sauri ta kawo mata ruwa ta zuba mata a cup ta mika mata, tasha kad'an ta ture ranta idan yayi dubu ya baci, ba dan dare ba a yau zata dira Kano wallahi, amma duk da haka da asubah zata dirar musu wannan karon ba zata kyale ba.


"Dan Allah Mama me faru? Wanne irin aure akayi ma Ya Tariq din?"


"Wai yanzu Safiyya ya rasa yarinyar da za'a hada Tariq da ita sai figaggiiyar yarinyar nan Jidda, saboda tsabar Yaya bata so na, shine aka hada aka rufe min."


"Jidda kuma Mama?"


"Eh."


"Amma waya fada miki Mama? Ko dai an samu misunderstanding dan yanzu muka gama magana da jiddan a WhatsApp kuma bata fada min ba."


"Kakarku ce da kanta ta kirani, ko muna yar wasa da ita bare nace wasa take min."


"Toh Jiddan ma bata sani ba Mama."


"Dallah rufe min baki, idan ma ta sani dole ne ta fada miki? Mutanen da suke munafukai, wato abinda ya faru da mahaifin ku shine shima Tariq aka kakaba masa ita, wallahi toh ba zata sabu ba, sai sun warware auren nan idan har ni na haifi Tariq a cikin ciki na."


"Kiyi hakuri yanzu dai mama ,ki tuntubi Ya Tariq din ko shi yace yana so, kar azo kuma a samu matsala."


"Wanne Tariq din? Lallai ma, Tariq ne zai so yarinyar nan,amma bansan ma baki da hankali ba sai yau, Tariq ba zai taba son mace irin ta ba, ni kawai suke so su bakantawa, a aure min miji a aure min d'a."


"Kiyi hakuri toh."


Mikewa tayi, ta shiga kwalawa Atika me aiki kira, tazo a sukwane dan daga jin kiran Maman a fusace take, ta nuna mata abinda zata biyo ta dashi, tayi gaba ta bita da sauri su kuma sukayi tsaye har sai da suka ga shigewar ta sannan suka hau yar rige-rigen daukar waya,Yaya Maryam ta kira ita kuma Amira ta kira Jidda, Umaima kuma ya Safwan ta shiga kira, daki Safiyya ta tafi kawai ba tare da tace komai ba.


Yaya ce ta fara dagawa dan gama wayar ta kenan da ya Safwan da ta samo shi garin kiraye kirayen ta


"Waye?" Tace tana dagawa


"Maryam ce Hajiya Yaya"


"Hala kin samu labari ne shine kika bugu min kiyi tsegumi."


"Kai Yaya, kiranki nayi fa na gaishe ki."


"Munafuka,nasan me kika kira kiji, aure aka daurawa yayan ku, kuma duk me dogon bakin da ta fada masa sai nazo har Habujan na tattaka ta."


"A jirgi zaki zo ko?" Tace tana kunshe dariyar ta 


"A uwar jirgi zanzo."


Dariya ta kyalkyale da, dan duk sun san yadda Yaya take bala'in tsoron jirgi, katse kiran tayi tana jan tsaki, sai kuma ta tuna ai yau ranar farin cikin ta ce b zata bari su bata mata ba.


  ***Kamar yadda Baba ya jewa Yaya da maganar haka ya jewa aunty, ta shiga shock sosai amma sai ta nunawa Baban ba komai, ta kuma bashi hakuri akan abinda ya faru satin da ya wuce, yaji dadi har ya saka mata albarka, tace zata fadawa jidda yace ta kira masa ita shi da kansa zai fada mata, zuwa tayi kiran jiddan ta sameta rike ta waya a tsaye tsakiyar falon, tana ganin Aunty tayi wajen ta da sauri


"Aunty wai haka ne?"


"Me?" Tace tana kallon yadda duk ta birkice


"Amira ce ta kirani."


"Zo ki zauna." Tace tana jan hannun ta,suka zauna sannan tace


"Gaske ne jiddah,yadda kika ji maganar haka nima na ji ta yanzu, duk da tun satin da ya wuce naji maganar shine har kika ga na fita ranar juma'a, toh ba in da naje illah wajen Baffa, na sameshi da maganar, kinsan me ya faru? 


"A ah.".  Ta girgiza kanta da sauri 


"Kaca-kaca yayi min, ya kuma tabbatar min da be yafe mana ba daga ni har ke idan muka bijire wa Baba. Har ga Allah naso ki da Isma'il, sai dai kinga ba mijin ki bane, shiyasa ma Allah be saka miki son shi ba, kiyi hakuri dan Allah karki ki yi musu biyayya, domin iyaye sun fi gaban nan, ina me tabbatar miki zaki ga haske da budi a rayuwarki "


Kanta a k'asa, hawaye ya shiga bin fuskarta, bata san a wanne yanayi take jin zuciya da gangar jikin ta ba, sai dai tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa, itace aka daura wa aure? 


"Tashi ki share hawayen ki, Baba yana son magana dake."


Da sauri ta shiga goge hawayen da bata san ainahin na menene ma ba, ta mike tabi bayan aunty zuwa bangaren Baban, suka shiga da sallama ya amsa yana kallon Jiddan da kanta yake a kasa tausayin ta na kamashi


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links