SANADIN LABARINA 20


  Page (20)


***Yana ajiye wayar Mama da take kallon sa tace


"Me ake shiryawa ba'a sanar dani ba?"


Murmushi ya sakar mata dan yana kyautata zaton idan ya fada mata zata iya bori ta tada hankalin kowa shi kansa Tariq din ta tayar masa da nasa


"Wannan tsakanin uba da dansa ne."


"Inyee, haka ne dama honourable?"


"Toh idan kuna sirrin ku ke da yan matan ki ina sani ne?"


"Ai shikenan, zamuji ai idan tayi tsami."


"Ba ma zatayi ba in sha Allah."


"Shikenan."


 Tace tana hasaso kila gida ne Babba Baban ya samawa Tariq din ko dai wani abun babba.

   Waya ya shiga yi ba kakkautawa, hakan ya saka Maman zamewa ta barshi shi kadai,ta koma dakin ta, ta dauki wayarta ta kira Aunty Mimi sukayi magana sannan ta fito ta nufi part din girls din nata, ta samesu kowacce tana zaune da waya ana fama,   Maryam na karanta novel a arewabooks, ita kuma Umaima tana kan tiktok tana more kallo, Safiyya na waya da saurayin ta Dr sufyan (urologists ne). Sai jidda tana buga game din candy crush a sabuwar wayarta, shigowar Maman ya sakasu duk maida hankalin su kanta,kowa ya ajiye waya ta zauna tare dasu suka kunna TV suna kalla. Kusan 30min ta dauka a part din nasu, sannan ta tashi ta tafi, haka take musu kullum musamman idan Baba be shigo gida da wuri ba toh tana tare dasu har sai dare ya raba kafin ta tafi bangaren Baban.


     ***Duk yadda Isma'il yaso ya share amma ya kasa, ba sosai Jidda take hawa WhatsApp din ba ko yayi mata magana bata dubawa ma kwata-kwata, gashi ko kiran ta yayi sama-sama take amsa masa, shiryawa yayi kawai ya tafi gidan dan a kalla idan face-to-face ne zata saurare shi ko babu yawa, duk da yasan akwai yarinta a al'amarin ta, amma kuma ya san ta san komai, ya kamata ace ta bashi dama ko yaya ne.


    Haka kawai taji sam beyi mata ba ko kad'an, dan kiran da yake mata ma ba karamin takura mata yake ba, ji take kamar ta kashe wayar ta hakura gaba daya, dan da tasan Safeera zata bashi number da bata ma fara kiran ta da number din ba. Jujjuya wayar take a hannu suna zaune su biyu ita da Aunty kowa da abinda ya dame shi, ta lura tun zuwan Baba Auntyn bata da walwala har ya koma,sai dai kuma bayan da ta fita ranar ta dawo sai ta sake ganin sauyi sosai a tattare da ita dan hatta kuzarin ta sai da ya ragu, gashi bata ce mata komai ba balle tasan abinda yake damun ta.

   Knocking akayi a kofar, suka kalli juna ita da Aunty kafin ta tashi ta bud'e kofar, 


"Hajiya tayi bako."


 Sai ya juya Isma'il dake tsaye a bayan sa tun farko ya bayyana a gaban ta, da sauri ta janye kanta daga kofar cikin tafiyar sauri-sauri ta wuce falon zuwa bedroom dinta dan dan siririn mayafi ya saka ta yane kanta, jikinta sanye da riga me gajeren hannu da skirt. Tashi Aunty tayi ganin mutum a tsaye sai duk kunya ta kamata tace ya shigo ciki,ya shigo jikin sa a sanyaye, ya zauna sannan ya gaida Auntyn cike da girmamawa, ta amsa ranta duk babu dadi dan har ga Allah bata so Jidda ta rasa miji kamar Isma'il.


"Bari a kawo maka ruwa." Tace tana neman hanyar barin falon, dakatar da ita yayi ta hanyar cewa


"Aunty dan Allah a bar ruwan nan a koshe nake wallahi."


"Toh shikenan, ina zuwa."


Sai tabi bayan Jiddan, zuwa dakin Jiddan ta sameta a zaune a saman drawer ta zurma Hijab har k'asa fuskar ta babu fara'a ko kad'an, kallon ta Aunty tayi da ta gama gano bata son Isma'il din tun ranar farko tace


"Kije kuyi magana, dan Allah ki saki ranki, Usman zaizo ya zauna."


Dan sakin fuskar tayi, tayi gaba har ta fita Aunty ta kirata


"Kina ji? Baka wulakanta mutum ko baka sansa Jiddah,kokari za'a yi a rabu lafiya, duk tsiya mutumin da yace yana son ka ai ya gama maka komai a duniya , kuma be kamata ya zama makiyi a wajen ka ba."


Kara sakin fuskar tayi ta gid'a wa Aunty kai sannan tafita, maimakon ta tsaya a falon sai ta wuce shi ta fice ko kallon sa batayi ba, sai da taje ta riko hannun Usman sannan ta dawo falon, ta zaunar dashi a gefen ta, kanta a kasa ta gaishe shi, 


"Lafiya lou." Yace duk ya gama tsorata da yanayin ta. Shiru tayi tana taba botir din jikin rigar Usman, har lokacin bata yarda ya dago ba bare har su hada ido, kamar wanda aka tsoma a cikin ruwan zafi haka yake jin sa, ga wata iriyar fargaba da faduwar gaba, shi be taba samun kansa a irin wannan yanayin ba, baya iya komai sai tunanin ta, haka duk abinda yake ita yake gani, amma kuma zuciyar sa ta soma karaya ganin irin tarbar da ya samu daga wajen Jiddan a yau bayan ba haka ya santa ba


"Jidda, maganar ranar nan ce tasa na sake dawowa, kinga ba zan hanaki karatun ki kawai dai inason a san dani ne, you can take all the time you want, ba zan taba magana ba, zan jira ki shiga university, idan ma har sai kin gama ne fine, zan iya jira."


Banza tayi masa dan bata tsinci komai a maganganun sa ba, ita ba dan karatun ta, take kin sa ba, shi so halitta ne, haka kawai taji bata son shi so na soyayya, tana dai respecting dinsa a matsayin shi na Yayan Safeera.


"Jidda baki ce komai ba, dan Allah say something, my heart is beating so fast, ba zan iya jure shirun ki ba, just say yes, ba zan sake takura miki ba, zan baki duk lokacin da kike so."


Dagowa tayi, tayi masa kallon cikin ido, sai kawai shaidan ya hasaso mata shi da wani irin zumemen kai, wanda bata taba gani ba sai ranar, sauke kanta tayi da sauri ta hau girgiza kanta hawaye na biyo kuncin ta


"Kayi hakuri ni dai."


"Dan Allah Jiddah, ki taimaka min wallahi zan miki duk abinda kike so, idan ma bakya so na dinga miki magana zan daina, ni dai kar kice min a ah dan Allah."


Cigaba da girgiza kanta ta dinga yi dan bata jin zata iya zaman aure inuwa daya dashi, be mata ba ko kad'an..ita kanta mamakin kanta take dan tasan idan banda fuskar ta da take da wani irin sihirtaccen kyau babu abinda zata nunawa Isma'il da har zata ki shi saboda shi.


Kamar zai jamo kasa haka yayi, rabin jikin sa baya kan kujerar saboda tsabar dimuwar da ya shiga, 


“Ina son ki Jiddah, ina son ki fiye da yadda nake son kai na, dan Allah ki ceci rayuwata ki so ni ko da kwatan son da nake miki ne.”  Ya furta bakin sa ararrabe yana rawa, shafe idanun ta, tayi da toka ta mike ta sungumi Usman tace


“Kayi hakuri Ya Isma’il, ba zan iya ba, ba zan iya ba.”   sai tayi gaba da sauri har da dan hadawa da gudun ta, daga muryar sa wadda take rawa yayi yace


“Shikenan Jidda, shikenan sai watarana!”


Amsa kuwwa karshen kalamen sa suka dinga mata a kunne, har ta dangana da bedroom dinta, in da ta bar aunty a zaune rike da wayarta tana kallon hotunan Tariq da suka kusa cinye dukkan gallery din, a yanayin da Jiddan ta shigo ya sakata dire wayar ta fita da sauri. Kansa a k'asa ya dora shi akan tafukan hannayen sa ta same shi, kiran sunan sa tayi a dan tsorace, ya dago idanun sa da suka rine sukayi masifar ja


"Subhanallahi, Isma'il." Aunty tace ganin yadda idanun suka kad'a sukayi ja


"Aunty Jidda bata so na, Jidda bata so na." Ya fada kamar wani zararre, sai ya mike yayi hanyar fita daga falon da sauri, Aunty ta kira shi amma yaki tsayawa, ya dinga sassarfa har ya dangana da wajen da yayi parking motar sa, ya shiga sai ya kasa kunna ta, hannun sa na wani irin kakkarwa, key din ne yafadi kasa, sai kawai ya kifa kansa akan sitiyarin motar yana jin wani irin makaki a makogwaron sa. He's shattered, be san ya zai yi ba, be san yadda ta ina zai fara ba, da kyar ya lalubo wayar sa, ya kira Farouk yace yazo ya tafi dashi, cikin kankanin lokaci yazo Nabil ya kawo shi, taimakawa Isma'il din sukayi ya koma baya ya zauna yana rintsa idanun sa da suke masa masifar zafi da zugi. Farouk ne ya ja motar Nabil ya bisu a baya. 


    Washegari Baba yazo Kano, tare da wasu ministoci su uku, gaisuwa suka je sukayi sannan suka je wani kauye chan da aka samu matsalar bandits suka duba su suka kai musu tallafi, hanya ce ta biyo dasu ta garin su jiddah sai kawai Baba yace su tsaya garin su duba su. Baffa be san da zuwan su ba, dawowar sa kenan daga gona ana ta kokarin nome amfanin gona, wanka yayi ya chanja kayan jikin sa sababbi kasancewar juma'a ce yaje masallaci yayi sallah ya dawo ya zauna kofar gidan, kamar daga sama yaga motoci na nufo shi, ya tashi da sauri sanin waye yazo, dan tunda Baba ya samu mukamin nan be samu shigowa ba sai dai yana yawan waya da Baffan kuma yana masa aike akai akai dan hatta gidan sa an gyara masa shi sosai, ga kuma shago babba da Baban ya bude masa a chan kasuwa yana saida kayayyaki nan da nan yayi fes dashi kamar bashi ba. Dama iya Lami tunda taga ya dawo daidai ta daina rashin mutuncin ta dan tasan ba kamar da bane da tayi masa zai auna ta gaba, duk da haka bakin halin nata yana nan shi ma kuma ya sani sarai kawai yana rabuwa da ita ne.

  Tun kafin motacin su ta tsaya DSS din suka dire kowannen su fuskar nan a tamke, jama'ar gari da suka soma tururuwar zuwa gani su duk suka lallabe daga baya dan dama labari ya karade ko ina sai gashi kuma sun gani da idanun su. 

   Dukkannin su mutane ne masu cike da kamala tamkar Baban, tarar su Baffa yayi cikin tsananin farin ciki gami da mamakin ganin su, suka gaisa a mutunce sannan yayi saurin shiga gida ya dauko babbar tabarma ya shinfida musu daga gaban gidan, suka zazzauna su kuma securities din suka tsaya daga gefe.


"Alhaji sannun ku da hanya, wallahi ban yi tunanin zuwan ku ba,nayi mamaki matuka wallahi."


"Hanya ce ta biyo damu Yaya, duk da dama lahadin nan na sa rai zamuzo da Alhaji Adamu da Malam Nura, sai kuma naga kawai tunda muna kusa mu karaso kawai."


"Masha Allah, nagode nagode Allah ya saka da Alkhairi."


"Amin Yaya, mun zo ne gaisuwa da kuma rokon iri, idan babu damuwa."


Da sauri Baffa ya katse shi


"Kar muyi haka da kai Alhaji, idan har akan maganar da Halima tazo min da ita ne akan Jiddah, toh babu ni a cikin wannan harkar, kaine mahaifin Jiddah bani ba, dan haka ba zaa tambaye ni amincewa ta akan Jiddah ba."


"Yaya ba haka bane ,wai dama kaga..."


"Alhaji kayi hakuri, amma kai ne mahaifin Jiddah, duk abinda ka yanke akan ta daidai ne."


"Duk da haka da ka saurari honourable muji me zai ce."


Daya daga ciki yayi maganar yana yabawa da dattakon Baffan


"Toh ina jinku Alhaji, ni dai idan har akan maganar auren jidda ne da yayanta toh wallahi na amince, na bashi duniya da lahira, idan a shirye kuke ga mahaifin jidda nan a zaune (Ya nuna Baba) ku bashi sadakin Jidda a hannun shi, zan kira makwaftana tunda duk yan uwana basa raye a daura auren nan kafin ku bar wajen nan "


"Yaya babu takura kuwa hakan?"


"Babu ko daya Alhaji, idan ma har na bari kuka bar nan bamu gama magana ba ai anyi ba'a yi ba kenan bari Kuga."


Sai ya mike ya zagaya bayan gidan, jim kadan sai gashi da mutane dattawa su shida, ya shiga yakaro wasu tabarmin sannan ya gabatar dasu a matsayin shaidu. Ba karamin mamaki su Baba sukayi ba, nan da nan cikin kankanin lokaci aka gabatar da komai, aka daura auren MUHAMMAD TARIQ NASIRUDDEEN DA HAUWA'U IBRAHIM JIMO, akan sadaki naira dubu dari.


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links