SANADIN LABARINA 19


   Page (19)


***Kusan sati guda kenan da zuwan su Isma'il amma babu wani information daga wajen Jidda, sun yi waya da Safeera da sabuwar number ta amma ba wadda tayi wa wata maganar a cikin su, hakan ya kara tada hankalin Ismail ya samu Safeera da magaanar sai kawai ta bashi sabuwar number din Jiddan da bata so ta shiga abun nasu sosai azo a samu akasi tazo tana jin haushin Jiddah. Samun number ya dan rage masa damuwa ya koma daki ya kirata sai dai har ta gama ringing bata daga ba, tana chan kitchen tare da Aunty ta bar wayar a daki tunda dama babu me kiranta daga Amira sai baffan ta, sai kuma Safeera idan tana so tace mata tazo WhatsApp suyi hira. Sake kira yayi ya dinga jera kiran tunanin sa tana gani ba zata dauka bane dan shine, sai kuma wata zuciyar ta tuna masa ai bata da ma number dinshi bare taki dagawa saboda shi ne, shafa kansa yayi yana mata uzurin kila bata wajen yana kokarin hana waccan zuciyar tashi ta farko tasiri a tunanin sa.  WhatsApp yayi login sai ya duba number din yaga tayi registering WhatsApp din sai kawai ya shiga kai ya tura mata kalamai masu dadi da sanyin gaske, hoping zata duba ta bashi time suyi magana ko da a wayar ne ba sai a fili ba. Cigaba da zama yayi rike da waya yana dakon kiran ta ko kuma zuwan ta online wanda yasan tabbas za'a yi dayan biyu, ko ta biyo kiran ko tazo online. 

   Dakin ta shigo bayan sun gama aikin da Aunty, ta dan gaji dan abinci sukayi na mutane da yawa da za'a fita dashi waje duk da akwai masu aiki amma kuma ya zame musu jiki duk irin wannan aikin tare sukeyi da ita da aunty, kasancewar aunty zata je taga Baffa duk da bata fadawa Jidda in da zata din ba dan bata so tace zata shiyasa ta bar mata aikin ta cigaba da kula dashi ita kuma taje ta shirya, ta fito ita da Usman suka tafi tare da Driver.

   Gama aikin kenan an zuzzuba a manyan kuloli ta baro wajen tasan Abu zata karasa sauran aikin a fidda shi, wanka ta fara yi tana shiga dakin, ta maida doguwar rigar dake jikin ta mara nauyi sosai ta kwanta lamo tana jin kanta na dan sara mata, tasan alamun period dinta ne shiyasa duk take moody ga wata irin kasala da take ji, farko da bata gane ba sai da Safeera ta fada mata sannan ta ganar da ita duk abinda ya kamata ta gane ta sani. Pillow ta daga ta ciro wayar ta duba, missed calls din da ta gani rututu ya sakata saurin cire lock din sai taga bakuwar number, da saurin ta, ta kira number back dan tasan duk wanda zai kirata ya san tane sosai kuma irin wannan missed calls din da yawa sai kaji tsoron ko ba kalou ba.

   A firgice ya dau wayar da take ajiye da a saman chest dinsa yayi rigingine yana jiran kiran gashi yana da fita zai je ya samu Daddy a office dinsa amma duk sai yaji baya son fita kwata-kwata. Yadda yayi mata saving sunan haka ya bayyana akan allon wayar sa, ya daga ba tare da bata lokaci ba yana manna wayar a kunnen sa sannan yace


"Bari na kiraki Jidda."


Sai ya katse kiran, muryar sa tar a cikin kunnenta, bata kawo shi zai daga ba kwata-kwata, sai tayi sakalo da wayar sanda ta dauki burarin shigowar kiran nasa, ganin zata katse ya sakata katsewa ta dan karata kadan a gefen kunnen ta kamar me tsoron shocking tace


"Assalamu alaikum."


"Jidda ,wa alaikisalam. Ashe zaki daga."


"Ina wuni?"


"Lafiya lou, kina lafiya? Ya gida dasu Aunty?"


"Alhamdulillah."


"Ina kika shiga ne, aka bar wayar bawan Allah tana ta neman agaji."


"Ina kitchen ne."


"Ah kice dai ashe da babbar chef nake magana, shikenan kinga ni lafiya lou."


"Uhum." Tace


"Me kika dafa mana? Nazo na karba dan nasan zai yi bala'in dadi."


"Abincin sadaka ne da akeyi."


"Oh okh, next time sai ace muzo muyi tasting ko? Nasan komai kika dafa zai yi dadi sosai."


Dan gajeren murmushi tayi me dan sauti, hakan ya sake bashi hope ya cigaba da zuba kamar be san yanayi ba, so yake dole sai yayi impressing dinta, ko ba komai a hankali zata saba dashi ta saki jikin ta dashi, shawarar da suka tsara kenan shi da zuciyar sa, ya fara kokarin saba mata da kanshi kafin komai ma yazo daga baya, duk maganganun da yake a gajarce take masa masa kanta na cigaba da tsananta mata da ciwo gashi bata so ta katse shi amma kuma maganar tashi ta ishe ta, sai da yayi ya gaji dan kansa sannan ya hakura yace zai kira anjima. Da sauri ta rigashi katse kiran ta kwanta tana tura kanta cikin filon ta yadda zata rage ganin hasken da yake kara mata ciwon kan.



***Ran Baba a bace yake sosai har Aunty ta gama masa bayani da abinda take so yayi idan Baba yazo masa da maganar Jidda, sai da ya bari ta gama tsaf sannan ya kalleta yace


"Kin gama?" 


Sai a sannan taga yanayin fuskarsa, sai taji kamar an dake mata guiwowi, ta tabbatar ba zai goyi bayan ta ba kenan duk da yadda tayi ta kokarin tsara masa maganganun yadda zai fahimce ta


"Kin bani mamaki Innajo, kin bani mamaki sosai."


"Na'am?"


"Yanzu har kece zaki budi baki kice na hana Alhaji auren Jidda? Kenan ma Jidda tana da wani uban bayan shi ban sani ba?"


"Yaya baka fahimce ni ba."


"Bana so na fahimce ki, ni ba butulu bane mara godiyar Allah, me Jidda tafi shi yaron da har zaki dage kai da fata? Wacece Jidda ma? Ke kina ganin ke da yar taki har kun kai wani matsayi da zaku yi abinda kuke so ko me?..."


"Bari na tuna miki idan har ke kin manta, sanda Alhaji ya aure ki ke kanki kinsan ke ba sa'ar auren sa bace, haka yace yaji ya gani ya aure ki ya rufa miki asiri da ni kaina, sannan kika dauki yar taki da kike ganin karan ta ya kai tsaiko da har zaku butulce, kika kai masa ya karba ya rike babu banbanci da Yayan cikin sa, ko akwai banbanci?"

    


Yace yana kafe ta da ido cikin bacin rai 


"A ah." Ta girgiza kai da sauri duk kwalla ta cika mata ido dan bata taba ganin bacin ran Baffa irin yau ba


"Sannan karki manta adalcin Alhaji lokacin da ya rasa Muhammad, kina ganin idan wani mahaifin ne ba shikenan ba kuma maganar auren ku ma zata iya lalacewa akan haka, amma me yayi? Shine ma yake kokarin kwantar miki da hankali ya kuma hana uwar yaron nan yin wani yinkuri, wannan shine mutumin da kike kin dan sa kike ganin be dace da yarki ba tunda ita din yar gwal ce."


"Dan Allah Baffa kayi hakuri, dan Allah."


"Ki barni na gama tuna miki tunda ke kin manta, sanadiyyar waye na samu lafiyar kafata? Idan kin manta sai ki tuna, dan haka..."


Ya nuna ta da yatsa


"Jidda ba 'yata bace, haka kike ba taki bace, yar sa ce dan haka yana da damar yayi duk abinda yaga dama akan rayuwar Jidda, ke ko mutuwa nayi wallahi ba zan yafe muku ba idan kuka kiyi masa biyayya."


"Dan Allah kayi hakuri Yaya, nayi laifi babba, amma dan Allah kayi hakuri."


"Toh kar na sake jin wannan maganar kin daga ta, sannan idan kinsan kin bata masa rai saboda magaanar nan, lallai lallai ki bashi hakuri, sannan ita ma Jiddan zan saba mata idan har tace zata zo min da shashanci."


"Ita bata ma san da maganar ba."


"Idan ma ta sani din, kuma ko yanzu Alhaji yake so ayi auren sai anyi."


"Allah ya huci zuciyar ka Yaya."


"Amin."


 Yace a kufule, sum sum sum ta tashi ta fice zuwa gidan su Saude, daga nan bata wani jima ba tayi sallama ta tafi, dan da tasan ma abinda zai faru ne da bata zo ba, sai bayan Baffan ya karanta mata duk abubuwan da ta manta sannan ta dawo hankalin ta, tasan bata kyauta ba kuma dole zata bawa Baba hakuri akan maganar.



***Baba na zaune a hadadden falon sa na ciki wanda ke cike da ababen more rayuwa, news yake kalla hankalin sa baki daya yana kai har wayar sa ta gama ringing sam be ji ba. Mama ce tazo ta zauna a kubin sa, cikn shigar alfarma kamar ko da yaushe, kamshin turaren ta ya cika ilahirin falon. Dan juyowa yayi ya dube ta, yayi murmushi kawai itama ta maida masa ya cigaba da kallon news din har zuwa sanda aka gama, juyowa yayi ya dauki wayar sa zai yi kira sai yaga missed calls din Tariq, kwana wajen biyu kenan basuyi magana ba, yana taso ya kirashi dama yaji progress din training din nasa dan baki daya yayi dedicating lokacin sa akan son yayi achieving hours din nan, yawanci ma yanzu ya fiyi saboda yanayin busy din da yake shiyasa ya tsirga sosai duk da giant ne a tsaye yake amma hatta idanun sa sun fada saboda rashin isashen lokacin da baya samu. Ko waya ma da Baba kawai sukeyi shima kuma duk maganar akan training din nasa ne sai jefi-jefi yake kiran Mama ko ta kirashi yaga missed call ya kirata idan yana free. Yanzu ma fitowar sa kenan daga cikin wajen yana cike da farin cikin akwai yiwuwar in less than a year da ta rage masa sai iya hada hours din, shiyasa ya cika da murna ya kira Baba dan ya fada masa amma kuma be dauka ba. Cigaba da tafiya yayi zuwa in dai zai hau train dan yau akwai in da zashi ba kai tsaye gida zai koma ba, yana so yaje yayi siyayya kafin a shiga cikin sati ya zama so busy ya kasa siyan abubuwan da bashi dasu. Kiran Baban ne ya shigo, ya daga yana rataya rigar sanyin dake rike da a hannun sa a saman kafadar sa, suka gaisa ya tambaye shi yadda ake ciki, ya sanar masa da duk progress din da aka samu, yayi masa murna sannan yace yana so ya nemi alfarma a wajen sa


"Inaso nayi maka wani katsalandan a rayuwar ka, duk da bazan fada maka ko menene ba, amma ina neman amincewar ka, idan har ka amince shikenan, ina me tabbatar maka da ba zakayi nadama ba."


"Baba... Akwai abinda dama zakayi min da har sai an nemi amincewa ta?"


"Eh."


"Toh na amince Baba, iyaye ba zasu taba yin abu dan su cutar da dansu ba, sai dan su faranta masa, I can't wait na dawo nazo naga ko menene."


"Masha Allah, thanks for trusting me, ba zaka taba dana sani ba, ka kula da kanka kaji? Sai munyi magana Allah yayi maka albarka."


"Amin ya Allah."


 Yace yana jin dadi a duk lokacin da Baba ya saka masa albarka shiyasa yake yawan koyi da Baban dan halayen sa ababen koyi ne.


  Farin cikin sa ne ya karu bayan gama wayar, yana fatan ko menene Baban zai masa ya zame masa alkhairi a rayuwar sa.

   Duk abubuwan da yake bukata ya siyo ya dawo ya samu Ishaq yana kokarin knocking a kofar sa, sai gashi yazo, ya matsa ya bud'e masa ya shiga bayan ya rage mishi kayan dake hannun sa


"Tuzuru ai na dauka ka dawo tun dazu ganin yau Friday da wuri kake dawowa."


"Naje African market ne, na samo yan kayayyaki, dawowa ta kenan."


"Ok naga alama ai, kaga da ka yarda kayi wuf da Yasmin duk wannan wahalar ba zaka sha ba, kuma ka samu cook."


"Don't mention her name please."


"Wai dai na tuna maka, kasan fa tana nan tana zaman jiran ka, wallahi da zaka yarda ko? Da har azumin nan sai ka daina shi, dama duk munsan dalilin azumin katon gauro kamar ka."


Da sauri ya kalle shi, ya ajiye pack din pepper din da ya fito dashi yana maida hankalin sa wajen sa


"Menene reason din fasting dina?"


"Waye be sani ba, oga rashin aure ne zaka wani fake da busy busy baka samu kaci abinci."


"Dan iska." Yace ya jefe shi da wani babban carrot, chafe wa yayi yaje wajen sink ya wanke yazo ya hau ci yana kyalkyalawa Tariq din dariya, murmushi kawai shima yake dan yasan maganar Ishaq din da kamshin gaskiya amma baya so yayi convincing kansa akan haka ne, dan be gama shiryawa aure yanzu ba, be ma fara neman matar da zai aura ba.

[

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links