SANADIN LABARINA 18


 


                  Page (18)


***Tunda suka shigo mota be kara magana ba, tsoron sa daya kar Jiddah taki shi, be san ya zai yi da rayuwar sa ba idan har tace bata son shi. Da kyar ya kaisu gida suna zuwa yayi saurin yin hanyar dakin sa, jiki a sanyaye itama Safeeran tayi nata dakin tana fatan kar a samu matsala dan ta san yadda Ya Isma'il yake son Jidda. 

   Tunda ya shiga dakin ya kasa zaune ya kasa tsaye,duk da ba wai tace bata son shi bane, amma kuma ai be kamata ta rikice haka ba, ya kamata ko yaya ne ta bashi amsa. Wayar sa ya dauka ya kira Farouk yace ya shigo dan Allah, nan da nan sai gashi, ya kwashe komai ya fada masa , shiru yayi yana nazari kafin yace


"Kila shock ne, kasan har yanzu fa da sauran su, kila bata taba tunanin hakan ba shiyasa tayi acting haka, give her some time, in sha Allah Khair."


"Kana ganin ba matsala, tari ne fa ya sarketa kamar zata shid'e."


"Calm down, ina ji a raina ba matsala bace gaskiya, ka bata time ka barta da Safeera suyi magana, kawarta ce tafi kowa sanin ta, hopely zata iya convincing dinta ma."


"I hope so, I'm just nervous ne, ba zaka gane ba. I don't think zan iya daukan rejection."


"Ba matsala fa, ka kwantar da hankali ka, as you come fine like this akwai wata babe da zata ki ka ne?"


"A ah fa, banda irin Jidda."


"Hadda wadda tafi Jidda ma."


"Kana dai fasa min kai ne kawai."


"Da gaske fa "


"Toh naji, bari na duba me akayi a kitchen yunwa nake ji yau ko breakfast ban ba."


"Kaji ko?"


"Bari kawai." 


Yace ya fita shi kuma ya mike kafarsa yana tausayin Isma'il din idan har aka samu matsala.


   ***Zaman jiran Baba yayi tayi har bayan isha, sannan ya shigo a gajiye duk da haka sai da ya tsaya a wajen Yayan dan yasan tana nan tana jiran sa, a zaune kuwa ya sameta tana kallo tana dan gyang'adi, sallamar sa ta sakata wartsakewa ta mike da sauri


"Yaya baki bacci ba, Allah yasa bani na rike ki ba nasan da wuri kike kwanciya."


"Kai nake ta jira wallahi, sannu da hanya."


"Yawwa, ai da kin kwanta idan Allah ya kaimu da safe sai muyi maganar."


"Ba zan iya hakura bane ai, magana ce me muhimmanci."


"Toh, Allah yasa lafiya "



Yace yana zama a kasan carpet din,daga gefen kafarta, baya taba zama kujera da mahaifiyar sa tunda ya taso, yana bala'in so da kaunar Yaya dan baya hada duk wani abu da ya shafe ta da kowa har kuwa da yayan cikin sa, shiyasa duk abinda take so shi yake mata. Gaba daya ya tattaro hankalin sa waje daya ya kara tankwashe kafarsa, dan yasan idan ba fada masa matsalar Yaya tayi ba ko baccin kirki ba zata iya ba.


"Maganar yaran nan ce Alhaji."


"Ina jinki Yaya."


"Ajiye 'yaya mata a gaba haka be kamata ba, ba daya ba har su biyar rigis, wanda duk cikin su babu wadda akayi wa aure ba zata zauna ba, abun nan kullum dashi nake kwana nake tashi, ya zama lallai duk su fito da miji ko da za'a yi karatun dai ya zama akwai maganar aure."


"Haka ne Yaya, dama dai akwai maganar Safiyya da Umaima a k'asa."


"Ah toh Masha Allah, ai ban sani ba, sai ayi abinda ya kamata, daga su sai azo maganar na k'asan."


"Wai da suma su fara jami'ar, tunda Maryam ta fara yanzu tana ajin farko, Amira da Hauwa'u kuma zasu fara suma bana,sai a hade su, su uku idan sun kai ajiye biyu ."


"Hakan ma yayi, amma ni ina da wata alfarma da nake nema a wajenka, buri na kenan idan ka cika min burin nan ka gama min komai."


"Babu alfarma a tsakanin mu Yaya, me kike so ayi? Fada kawai zakiyi ni kuma zan cika miki da yardar Allah."


"Magaanar yaron nan ce Tariq, da yarinyar nan Jiddah."


"Na'am!"


"Na duba na dubo gaba daya dangi kaf banga wadda ta dace dashi ba, sannan na gamsu da tarbiyyar yarinyar nan dari bisa dari, ina kaunar ta har cikin raina bana so mu rasa ta, shine nake so ka kaini wajen mahaifinta na nema wa Tariq auren ta."


"Toh Yaya, duk yadda kika ce haka za'a yi, da ni da yaran nan duk ikon ki ne."


Washe baki tayi cikin tsananin jin dadi tace


"Allah yayi maka albarka,ya raba ka da duniya lafiya, ya sa yaran nan su rama maka."


"Amin Yaya."


"Yanzu yaushe zamu je?"


"Toh Yaya, ko wani satin idan Allah ya kaimu, sai muje."


"Toh shikenan, Allah ya kaimu."


"Amin ya Allah, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."


"Amin Amin,sai da safe."


"Allah ya tashe mu lafiya."


    ***A daki ya samu Aunty, ta tare shi da fara'arta, ya fara watsa ruwa ya zura sabuwar jallabiyar sa sannn ya dawo falon ya zauna, abinci ta kawo masa wajen da yake zaune, yaci kad'an dan cikin sa a chushe yake, ta tattare ta kwashe ta maida kitchen sannan ta dawo ta zauna a gefen sa, zuciyar ta na azalzalarta da maganar Jiddah, kallon ta yayi yaga kamar akwai abinda zata fada masa, sai ya ajiye remote din hannun sa ya tattara hankalin sa ya bata yana fuskantar


"Ya akayi Halimatu, kamar da magana a bakin ki."


Murmushi tayi ta sauke kanta k'asa, 


"Yanzu na baro wajen Yaya, tazo min da wata magana me girman gaske, duk da na amsa mata da toh dan dole a lallaba ta, amma kuma ina hasaso gaba, duk da ni kaina na dade ina hasaso dama hakan ta kasance a raina, amma na share saboda sanin halin yaran yanzu ba irin mu bane, kar kayi musu abu su ga kamar ka takura musu, shiyasa nayi hakuri na bar magaanr a raina, amma kuma sai ga Yaya tazo da maganar, kuma ga dukkan alamu idan har aka ki yi mata abinda take so za'a samu matsala."


"Toh, Allah yasa ba wani babban abu bane."


"Babba ne a wajen yaran idan har aka samu akasi, amma kuma idan suka hada kansu zan fi kowa farin ciki da wannan hadin."


Kanta ne ya kulle bata gane in da Baban ya dosa ba, ganin bata fahimta ba ya saka shi yi mata gwari-gwari.


"Yaya ce take so muje mu samu Yaya, a nemawa Tariq auren Jidda."


Wani gingirim taji kanta yayi, ta kalli Baban sannan tace


"Tariq kuma?"


"Eh."


Ranta ne ya dan sosu, har Baban ya fuskanci bata ji dadin maganar ba, duk da bata ce komai ba amma fuskar ta, ta nuna rashin jin dadinsa. Ido ya zuba mata cike da mamakin yadda ta karbi maganar, a tunanin sa zata fi kowa murna da hakan dan ko ba komai Tariq dan dakin tane, sannan be yi tunanin zata ki jinin sa ba, tunda duk tsiya ai Tariq dan sa ne, kuma idan da kara itama ai dan ta ne


"Akwai matsala ne?" 


Yace mata fuskar shi na sauyawa zuwa bacin rai, girgiza masa kai tayi kawai. Sai ta mike ganin ba zata iya rike abinda take ji ba, ta fice daga dakin ya rakata da ido cikin tsananin mamaki.

   Daki taje ta zauna ta rasa abinda yake mata dadi, bata taba kin Tariq ba, ba kuma zata taba kin sa ba, amma Mama fa? Ya rayuwar Jidda zata zama a auren wadda mahaifiyar sa bata so ko kaunar ta? Har ga Allah tafi wa Jidda sha'awar Isma'il, tunda shi da mahaifiyar sa duk suna san jidda, zata fi samun nutsuwa dasu dan zasu tallafi rayuwar ta, sannan zata samu uwa da zata dubi lamuran ta.

    Safa da marwa ta dinga yi a tsakanin dakin ta, shiyasa Yaya dazu ta bata rai kenan akan maganar, shine tayi saurin fadawa Baban, da tasan hakan ne zai faru da bata yi mistake din fara sanarwa Yayan ba, dama ance ciki ba dan abinci kawai aka yi shi ba, da ta sani ta rike sirrin su ya zama tsakanin ta ne kawai da Jiddan har zuwa sanda zasu fahimci juna daga nan duk abinda za'a yi sai ayi. Yanzu ya zatayi? Zata cewa Baba a ah ne bayan abinda yayi wa Jiddan da bashi da maraba da abinda yayi wa Yayan cikin sa, ko zasu ki dansa Tariq ne bayan shi be kyamace su ba. Ko kuwa Baffan Jidda zai hana dan Baba auren Jidda ne? Bata da mafita, mafita daya ce idan har jidda taki, amma kuma tayaya ma Jidda zata ki? Baba ko Yaya su nemi alfarma a wajen ta, ta kasa yi musu. Ai da ta cika babbar butulu kuwa.

    Har kusan awa daya bata koma dakin Baban ba,tana ta sakawa da kwancewa har bata san lokaci yaja haka ba, dakin Jiddan ta shiga a tunanin ta ko tayi bacci dan tana da baccin wuri, ga mamakin ta, idanun ta biyu tana kallon hotuna a wayar ta, akan hoton Tariq take, jin Auntyn ya sakata saurin kifa wayar amma duk da haka Auntyn ta riga taga abinda take yi, maimakon tayi abinda ya kawo ta dakin sai kawai ta fice ta jawo mata kofar.

   Tashi Jidda tayi dan tunda ta zauna take kallon hotunan Ya Tariq dake cikin wayar, har sai da Auntyn ta shigo sannan ta dawo senses dinta, takashe wayar ta makala ta a charge ta kwanta ta rufe idanun ta, maimakon tayi bacci sai ta samu kanta da tunanin sa, ta dinga juyi tana so baccin ya dauke ta amma sam, haka tayi ta fama har dare ya tsala sosai, da kyar bacci ya dauke ta.

  Tashi tayi da safe idanun ta a kumbure saboda rashin bacci, ta gyara dakin ta dan yanzu part din Auntyn baki daya masu aike ne ke gyarawa. bayan ta gama ta fito falo ta zauna kenan tana kallon TV Ya Safwan ya shigo, ta gaishe shi ya amsa yana nuna mata fuskar ta


"Me ya faru da face dinki?"


"Bacci ne wallahi."


"Wai da gaske kike dama da kika ce raba dare zakuyi da Amira kenan."


"A ah, wajen 9 fa muka gama waya da ita, sai kuma baccin yaki zuwa."


"Kina me? Kallo ko?"


"A'ah, hotunan daka saka min na zauna ina ta faman kalla ashe har dare yayi ban sani ba."


"Ah shiyasa, kinga ai kin more kallo."


"Kai Ya Fauwaz."


"Allah kuwa."


"Fauwaz." Aunty ta kira sunan sa tana shigowa, kallon kofar yayi dan jiya be dawo ba, da yaga dare yayi sai kawai yace ya shigo da safe.


"Ina kwana aunty?"


"Lafiya lou, ashe tare kuke jiya da Baba."


"Eh wallahi, wajen Jamil naje kuma sai muka tafi wata sabgar sai dare muka dawo."


"Lallai, an kwana biyu ai ba'a hadu ba."


"Wallahi."


"Ya kowa da kowa?"


"Duk suna lafiya suna gaishe ku."


"Muna amsawa."


 Sai ta wuce ta dauki flask ta fita zuwa part din Baba, dama abinda ya shigo da ita kenan. Ko da ta koma jiya da daddare Baban ya kwanta, da safen nan kuma ba'a tada maganar ba, a ransa yaji babu dadin yadda tayi amma kuma ya mata uzuri sosai, tunda ko da Mama ce haka zatayi itama, tunda yanzu ko a hakan ne yasan akwai kalubale a gaba ma, shiyasa kawai ya bar maganar yaga abinda Allah zai yi.

   Ko da yaushe idan Ya Fauwaz ya shigo sai yayi mata maganar Ya Tariq, duk kusan rabin hirar su akan sa yake mata, yana sanar da ita duk kyawawan halayen sa, hakan ya saka ko bayan da ya tafi ta kasa mantawa da duk magangan da sukayi,ta dinga bitar su kamar wadda take bitar karatu


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links