Page (17)
***Shiru ne ya biyo bayan zaman, kowa da abinda yake sak'awa a ransa. Safeera ce ta gaji da shirun ta mike
"Ya Isma'il muje sai muyi waya ko Jidda?"
Gid'a mata kai jidda tayi, tana kallon Safeera taje tayi wa Aunty sallama tazo suka fice ita dashi tana zaune kamar wadda aka dasa a wajen. Aunty ce ta fito ta sameta a zaune a wajen kamar wadda aka ce karta motsa daga wajen, kunyar Auntyn ce ta lullube ta, ga wani irin yanayi da take ciki me wahalar fassarawa
"Jidda ba dai korar su kikayi ba ko?"
Girgiza kanta tayi sannan tace
"A ah Aunty."
"Toh ya akayi? Bani labari."
Dariya ta bawa Jiddan yadda ta zauna tana kallon ta, tana jiran ta bata labari
"Ni suka fara samu da maganar jiddah, da farko ma mamaki nayi a tunani na Ismail yafi karfin ki, ban taba kawo hakan ko a hasashe na ba, kina ganin zan bari wannan babbar damar ta wuce mu?"
"A ah." Tace a sanyaye
"Shiyasa na bashi dama kuyi magana duk da nasan halin ki, ba lallai ma ki bashi wannan damar ba."
"Uhum."
"Muyi addu'a mu nemi zaɓin Allah, idan da alkhairi Allah ya tabbatar mana."
A ciki ta amsa, ta tashi ta shiga ciki dan tana bukatar zama ita kadai tayi tunani sosai.
***Tun bayan tafiyar su aunty take jujjuya maganar a ranta ta rasa Wanda zata fadawa, a yau take saka ran zuwa Baban, weekends yake zuwa Kano sai yayi kwana biyar a Abuja, ta gama duk abinda zatayi tunda tasan ko yazo ma sai ya gama da mutanen sa a waje sannan yake shigowa ciki, jidda tayi kulewar ta a daki yan miskilancin sun motsa sai ta kyale ta tayi nazarin abun sosai.
Yanke shawarar zuwa wajen Yaya tayi kawai ta rage zaman kadaitar, ta yafa mayafin ta ta nufi shashen Yayan, ta sameta a zaune ita da aabu suna zare ganyen zogale daga jikin sa, sa hannu tayi aka cigaba tare da ita suna hira har aka gama tas abu ta dauka ta tafi kicin ta dafa mata. Fitar abun ya saka Auntyn yin shiru tana tunanin sanarwa Yayan abinda yake faruwa da yake ya nukurkusar zuciyar ta, yanke shawarar sanar da Yayan tayi kawai dan idan abu na cin ka idan baka fada ba baka taba jin dadi.
"Yaya kin gane kawar Jidda Safeera ko?"
"Na gane ta, bikin ta yazo ne?"
"A ah, su ai yan boko ne Yaya."
"Ai sai ayi tayi dai, yaran nan jiran Alhaji nake yazo ayi wacce za'a yi, ko zasuyi karatu sai sun fara fidda miji, dazu muna maganar da jiddah dariya ma ta mayar da abun."
"Gaskiya ne yaya."
"Toh Allah,zaka bar zagada-zagadan yan mata ne a gabanka haka? Wannan ai shirme ne."
"Ita Jidda dama maganar da zan miki kenan, Yayan kawarta ta, Ismail yazo yace yana son ta."
Da sauri Yayan ta kalle ta kamar bata shirya jin hakan ba, kamar kuma ba ita ke maganar a samu miji yanzu ba
"Ita Jiddan ce tace yazo?"
" A'ah, shine dai ya sameni da maganar, shine nace bari na fara fada miki."
"Toh ita Jiddan tana son shi ne?"
"Wallahi Yaya ban sani ba, amma dai kinga yadda suka shaku da kanwar sa, kuma suna son Jiddah sosai har mahaifiyar su wallahi, shiyasa nayi mata sha'awar shi."
Shiru Yaya tayi, ta bata fuska nan da nan tayi kicin kicin, hakan ya bawa Aunty mamaki ta rasa dalilin hakan daga Yayan, kasa hakuri tayi tace
"Baki ce komai ba Yaya."
"Toh me zance? In dai tana so kuma an tabbatar da halin sa ai shikenan."
Shiru duk sukayi, ganin kamar ran Yayan ya baci sosai ya saka Auntyn tashi ta tafi, tana fita Yayan ta mike itam
"Ai ba zata sabu ba wallahi, gida be koshi ba a kai dawa, yarinya me hankalin zan bari ta kubce mana ina, bari ubansu yazo."
A fili take maganar tana tsaye, sai ga Fauwaz kamar wanda aka jeho hannun sa rike da ledar wayar Jidda da Baba ya siya musu ita da amira na gama school, sai kuma sakon snacks da Mama ta bayar a kawo ma Yayan. Tafiya yayi da dan sassarfa kamar zai rungume Yayan ta goge tana dariya
"Shakiyin banza, shakiyin wofi, rungume ni fa zakayi da ko?"
"Eh wai irin na turawa ba, irin nayi missing din nan naki."
"Allah ya shirye ka kaji, zuwan Kenan?"
"Wallahi Yaya, zuwan kenan dan Baba ma ya tsaya wani meeting ga wata gaisuwa da zasu kawai nayi gaba dan na matsu naga my heart beat."
Ya tallafe zuciyar sa, bugu ta kai masa ya zille yana kyalkyala dariya
"Zo ka zauna dama neman wanda zan fadawa damuwa ta nake sai gaka."
"Faduwa tazo daidai da zama, ga sakon ki inji Hajiya Mama, part din ki kuma ya kusa kammaluwa na daina missing dinki."
"Toh ajiye nan tukunna, an gode."
Ajiyewa yayi ya zauna, itama ta zauna tana tattaro hankalin ta waje daya kana gani kasan magana zatayi me muhimmanci
"Ya labarin Yayan ku?"
"Lafiya kalou, ya gama ai har ya fara training, kinsan wasu awowi ake so ka hada kafin ka zama babban matukin jirgi."
"Shi kuma abin da ya dame shi kenan, saboda tsabar rashin son mutane shine ya zabi bangaren da ba zai dinga zama ba kenan koyaushe yana sama kamar tsuntsu."
"Da dadi fa Yaya, babban aiki ne."
"Kai ka sani, ni ba wannan ba, zaka iya kira min shi yanzu?"
"Yanzu nasan baya kusa dan dazu muna magana ma ya kashe zai kirani."
"Toh shikenan, wai kuwa yana da budurwa ni Hajara?"
"Tab! Ba dai Ya Tariq ba, karatun ya saka a gaba idan fa ba gani yayi ya karbi cert dinsa a hannu ba, toh fa ba zai nutsu ba, yana da naci duk abinda yasa a gaba."
"Toh Masha Allah, wani tunani nayi. Zan je takanas na roka masa auren Jidda a wajen mahaifin ta."
"Jidda kuma Yaya?"
"Ita, dan Malamin da ya bashi rubutu ya fada min, idan aka basshi haka sakaka toh ko auren ma ba zai ba, haka zai kare rayuwar sa, ni kuma sai na duba kaf dangi babu me halin Jidda, ita kadai zata iya taimaka mana ta rufa mana asiri."
"Amma Yaya Jiddah fa, da Ya Tariq?"
"Menene a ciki?"
"Ba komai, amma a fara jin ta bakin ta kar ayi mata dole."
"In sha Allahu ma babu wata matsala, ina ji a raina zasuyi rayuwar aure ingantacciya."
"Toh yanzu ta yaya hakan zata kasance?"
"Ni dai kai zaka taimaka min, ka sami Jiddah da maganar naga kuna shiri sosai, ni kuma zan fadawa Baban KU."
"Toh Ya Tariq din fa?"
"Karka fada masa, irin matsalar sa ai baa fada musu sai dai kawai ayi dan aka daka ta tasu wallahi ba za'a yi ba."
"Auren dole kenan za'a masa."
"Dallah ana kaika."
"Toh ai Yaya abin ne, nasan halin ya Tariq da taurin kai, kar ya bata ma yarinya lokaci azo ba'a barta ta zabi miji da kanta ba shi kuma yazo yace ya fasa."
"Ai wallahi ina me tabbatar maka be isa ba, kai dai kawai kayi abinda nace, sauran ka bar komai a hannu na, Dijengala nake me abun mamaki "
"Toh Allah ya taimaka dije."
"Ka fadi sunan uwarka."
"Hahaha, Allah sai na fasa taimaka miki."
"Yi hakuri toh."
"Ban hakura ba, sai kince please."
"Ni zaka wulakanta dan zaka taimaka min?"
"A ah, amma sai kin bani hakuri da turanci."
"Kasan dai bana son shegen turancin nan? Kaga ana ciccize baki wai a dole ana turanci, mtswws! Aikin bur inji tusa."
"Shikenan tunda bakya son taimako na, kuma sai na fadawa Ya Tariq abinda kike shirya masa idan yaso ya hawo jirgi yazo ya sameki."
"Yazo din mana, tsoron sa nake? Karka taimaka din idan baka taimaka ba ai ubanka zai taimaka tunda shi na isa dashi."
"Calm down My heart beat, wasa fa nake miki, ai ban isa naki abinda kike so ba, yanzu zanje na fara aikin ki."
"Yawwa dan albarka, yi maza ka gama kai ma na samo maka taka ko a karkara ne."
"Wait what? Wallahi kar ma a fara dan ina da fine babe dita idan ba haka ba kuwa zan bar gari na hada kayana na tafi karkashin gada."
"Ka tafi bangon duniya ma, dan nema."
"Maimakon ki lallaba ni,o matar nan."
"Ba zan lallaba din ba, nima ba uban da ya lallaba ni da za'a auran min dunkum din kakanku."
Da sauri ya sa hannu ya toshe bakin sa saboda yadda ta bashi dariya sosai, ya mike ya fice dan idan ya biye mata ba zata gaji ba sam.
Tsohon part dinsu ya shiga, ya ciro sabuwar wayar Jidda ya bude ta, ya tura hotunan Ya Tariq masu yawan gaske sai nasu dasu Amira dan kar ta kawo komai, sannan ya kashe ta, ya maida ita kwalinta, ya nufi bangaren Auntyn.
Jidda na kwance a daki tayi rigingine taji usman na ihun ya Fauwaz, da sauri ta duro ta fito ta same shi a tsaye ya daga Usman sama yana dariya.
"Ya Fauwaz." Tace ya sauke Usman yana mata murmushi
"Jidda ce tayi kiba haka?" Yace a sigar tsokana, dariya ta saka
"Kai Ya Fauwaz yaushe ka ganni last zaka ce nayi kiba."
"Allah kuwa, idan na ganki a hanya ma ai ba zan gane ki ba."
Dariya kawai take dan tasan hadda tsokana, duk da tasan tayi mugun chanjawa sosai dan baki daya jikinta ya murje duk ramukan nan sun ciko sai wanda ba za'a rasa ba. Bangaren chest da bayanta a lokaci daya tayi su dan bata taba ma tunanin zata yi ba, girman lokaci daya yazo mata shiyasa yanzu koyaushe da Hijab dinta take yawo a cikin gidan saboda ma'aikatan da masu gadin gidan.
Ledar wayar ya mika mata ta karba tana leka ciki, tayi tsalle cike da murna,
"Sakon Baba,."
"Mungode Allah ya kara budi."
"Amin Amin, Amira ma jiya aka bata tata, number ta na ciki tace ki kirata kina kunna wayar akwai gist."
"Toh shikenan, yau ba zan iya bacci ba, kusan kwana zamuyi muna hira nasan."
"Lallai gandoki, zaku yi ku bari ne, ina Aunty ta shiga?" Ya waiga yana kallon bangaren bedroom din Auntyn
"Tana part din Baba."
"Ok, gidan shiru,kuma ku tattara ku dawo ma dinga zuwa hutu kawai."
"Aikuwa."
"Shine, dama akwai plan din Baba, amma wannan zuwan nasan har da magaanar tafiyar ma, kinga ya maida hankalin sa waje daya ya dinga zuwa ko duk after two weeks ne, yanzu kuwa yana chan hankalin sa na nan."
"Ai kamar Yaya ce bata son tafiya ko?"
"Haka zata hakura, an gama.mata part dinta ma fa."
"Lallai dole ta hakura."
"Aikam, in baki labari." Yayi kasa da murya
"Nayi new babe wallahi."
"Dan Allah, aina take?"
"A chan Abujan ne."
"Lallai, Masha Allah."
"Ki bari kawai, zuwa zan na shige daga ciki, na bar Ya Tariq tunda shi ya tsaya kure wa boko guda."
"Be gama ba har yanzu? Ya dade."
"Ya gama wani course yake, kinsan pilot ne."
"Wai, ban ma sani ba ai."
"Aiko yana chan ya kusa ma, dazu muka gama waya ma."
"Allah sarki, idan kunyi waya ka gaishe shi."
"Gaki da sabuwar wayar ki, na ma saka miki number kowa har tasa, ki kirashi kawai."
Zaro ido tayi
"Wai... Tsoron sa nake ji, ba zan iya ba wallahi."
"A ah zaki iya mana, menene abun tsoro?"
"Uh um, ka gaishe shi kawai."
"Toh shikenan, zaiji."
"Nagode."
"Bari na dubo Jamil mu gaisa, zan dawo idan aunty ta fito."
"Ok sai ka dawo."