SANADIN LABARINA 15


         Page (15)


***Shiru yayi bayan ya ajiye wayar, mamakin sa na karuwa idan ya tuna yanayin yarinyar, tsaki yaja ya mike ya rasa dalilin da yasa shi damuwa da al'amarin ta har haka, ya kuma rasa dalilin da duk lokacin da ya ganta sai ya ji duk maganar dake dauke akan harshen sa ta dauke. Tsaki ya sake ja a karo na biyu yana dan murza saman goshin sa. Tunawa yayi da abinda yake kafin shigowar wayar, kashe datar sa yayi dan kar a sake damun sa ya cigaba da duba takardun sa har zuwa lokacin da yaji ya gaji sosai sannan ya hakura. ID card dinsa ya dauka da wayar hannun sa ya fito, ya bi ta wajen office din masu apartment dinsu da suke zama kullum Monday to Friday, jinin su ya hadu da ogan dan sosai yake son shi suna ganin shi suke fara murna shiyasa yake yawan tsayawa idan zai fita su gaisa. Ogan ne yau shi kadai a office din yana duba sabbin washing machines din da za'a kawo. Daga jikin kofar ya dan yi knocking, ya taso da sauri


"Hello James."


"Hello Tariq, please come in." Yace yana nuna masa ciki 


"No thank you, just want to check on you, i'm on my way."


"Ohh, not bad."


"I'll see you later."


"Ok Tariq, i sent you an email, see ya."


"Ok , bye."


Wayar sa ya bude ya shiga mail dinsa, sai yaga wai ashe gift card ne me dauke da £80 suka bashi a matsayin lucky winner na duk yan gidan da suke bayarwa duk karshen wata, murmushi yayi kawai ya maida masa reply da 


"Thank you, I hope it's not cheating."


Dariya James yayi dan da gaske cheating din ne, wata baturiya ce taci dan shi Tariq ko participating be yi ba amma ya bashi, reply yayi masa


"It's cheating bro. Lol😅"


Murmushi Tariq din ya sake yi kawai, ya maida wayar yana kara sauri akan tafiyar da yake a dah.

  A dan garden din cikin school din ya hangi Yasmin suna zaune da wani dan kasar ghana, so close kamar zasu shiga jikin juna, tabe baki yayi yazo zai wuce su ta tashi da sauri tana kiran sa


"Tariq please ka tsaya."


Dan rage tafiyar yayi har ta daidaita dashi, yaki kallon ta suka cigaba da jerawa har zuwa cikin building din, I'd card dinsa ya ciro yasa a kofar itama tasa nata suka shiga still be kalle ta ba suna dai tafiya a tare, sai da yazo in da yake son kaiwa sannan ya ja ya tsaya yana mata kallon me faru?


"Please magana nake so muyi."


"Ina jinki." 


Yayi folding hannun sa a kirji ya jingina da bangon wajen


"I want us to be friends, pleaseeee."


"Kin taba ganin friendship mace da namiji?" Yace yana kallon ta


"Na'am?"


"Yes, kin taba gani?"


"Sosai, ina da friends both maza da mata, and I see nothing wrong with it."


"Ok, ni I'm exceptionally different, bana friendship da other gender, it's haram in Islam, sorry."


Yayi gaba abin sa ya barta a tsaye cike da takaicin wulakancin sa, juyawa tayi taga babu kowa a wajen sai su biyu, ta yi saurin barin wajen tana jin kamar ta kwala ihu, bata taba ganin dan rainin hankali irinsa ba, but ba zatayi given up ba zata cigaba da gwada sa'ar ta.



***Kanwar Yaya ce wadda ake kira da Gwaggo tazo dan taya Yayan murnar Baba ta kuma yi kwana biyu, halin su daya sak da ita da Yayan wajen surutun su, sai dai ita tafi Yaya sauki wajen fada dan Yaya akwai masifa bata ragawa kowa duk girman ka sai dai idan baka tabo ta ba. Kwanan su Mama biyar suka dawo suka bar Baba achan, a ranar kaf yan uwan Mama suka zo taya ta murna, tamkar ana shagalin biki haka aka taru Yan uwan da abokan arziki aka ci aka sha. Aunty da jidda suna bangaren Yaya anan suke nasu zaman su isu dan basu da hurmin shigarwa Maman abu. Amira ce ta kawo abinci a yar madaidaciyar kula inji Aunty Mimi tace a kawo ma Auntyn, sai kuma na Yaya shima daban. 


"Zo muje part dinmu, su salma sunzo duk muna dakin mu."


Amira tace wa Jidda, kallon Aunty jidda tayi alamun taje? Ta daga mata kai dan ba zata iya hanata ba dan ita tun dama chan bata taba hanata zuwa ba ita dai Jiddan ce bata so,. Tashi tayi ba ason ranta ba dan dai kawai kar Amiran taji babu dadi ne shiyasa. Ta bita suka shiga part din nasu. Duk suna zazzaune a falon an baje ana ta hira suka shigo sai duk suka bi Jiddan da kallo, aunty Mimi ce tace


"Amira kawarki ce tazo?" 


"A ah Jidda ce fa, ta gidan nan."


"Ku wuce malama." 


Mama tace tana bata rai,


"Wacece?" Suka tambayi Maman bayan su jiddan sun wuce ciki


"Yarinyar chan ce ta dauko ta, yar brother dinta ce daga kauye."


"Inyee samun waje tusar asuba." 


Aunty Nafi tace tana rike haba


"Tubarkallah Masha Allah, me kyau da ita wallahi." 


Aunty Mimi tace tana kokarin dauke maganar Nafin


"Ai ke Mimi bansan wacce irin zuciya ce dake ba, har wani kod'a kyawunta kike a gaban Yaya."


"Toh laifi ne Ya Nafy? Ni fa ban ga abin tada hankali ba anan, beside har yanzu fa Ya Aisha ce a sama wajen his excellency, ko wannan kadai ya isa ai mutum ya hakura, wasu in sun yi auren ai wulakanta da gida suke, amma kiga fa ko tafiya Abujan nan Mama ce fa zata koma, tsakani da Allah mu ajiye son zuciya muyi maganar Allah, menene laifin Halima?"


"Mimi bana son maganar nan dan Allah, a barta ranar farin ciki ce bana son abinda zai bata min rai."


Mama tace tana mikewa


"Nayi shiru." Ta rufe bakin ta, tabe baki sauran sukayi dan duk basa goyon bayan Anty Mimi kawai dan dai babu me ce mata komai kowa yana respecting dinta dan kaf gidansu babu kamar ta a kirki da son yan uwanta.


***Duk suna zazzaune wasu na danna waya wasu kuma na hira Amira ta shigo tare da jiddah,


"Maryam yau ga jidda na sakata shigowar dole."


"Kai Amira da kai na fa nace zan biyo ki."


"Ban yarda ba wallahi." Umaima tace tana dariya


"Wace ita?"


 Salma da tun shigowar ta taji sam yarinyar batayi mata ba, in dai taga wadda ta fita kyau a waje sai kawai taji tana jin haushin ta, tafi so duk in da taje ta zama ontop


"Jidda ce, yar gidan Auntyn mu ce."


"Daga kauye take kenan." Tace tana dariya


"Salma." Ya Safiyya dake gefe tana chatting tace tana bata fuska


"Bana son irin wannan maganar, jiddah shigo ki zauna."


 Ta dora tana yi wa jiddan murmushi abinda yayi matukar daure mata kai, toh ko dan dama bata cika magana bane shiyasa Jiddan ta zata ko bata da kirki ne? Jikinta a sanyaye ta zauna kusa da Maryam, sai Salma ta tashi fuuuu ta fice daga dakin.


"Yarinyar nan bata da hankali, amma zan yi maganin ta."


Safiyya tace tana mikewa, ta bar musu dakin ya rage daga Jidda, Amira, Umaima, Maryam sai yar gidan Aunty Mimi Nu'ayma. Sukayi zaman su har jiddah ta saki jikinta sosai dan dama Salma ce tasa ta darare da farko, tare suka ci abinci a dakin sukayi zaman su har lokacin tafiyar su Nu'ayma yayi Salma ta shigo tana kumbure-kumbure tace tazo su tafi. Biyo ta sukayi ya rage saura jidda a dakin tayi zaman ta, suna fita suka ji Aunty Nafi na fada


"Akan wata bare Safiyya zata wulakanta yar uwarta yanzu Ya Aisha"


"Kiyi hakuri zamuyi magana, duk wannan ba abin tada hankali bane dan Allah."


Mama da bata cika son irin wannan abubuwan ba, ta fada tana kallon gefen da Safiyya take akan dinning tana duba wata magazine kamar ba da ita ake ba. Ashe biyo Salman tayi ta rar rankwashe mata kai tace kuma kar ta sake musu irin haka, shine harda kukan ta, ta fadawa uwarta shine ita kuma taji haushi take ta banbami.


***Babban Album jidda ta hango akan wata akwati, ta tashi ta dauko ta bude ta fara kalla, hotunan su ne tun suna yara zuwa girman su, sosai wasu hotunan suka bata dariya, ta dinga dariya tana kalla, har tazo kan hotunan Ya Fauwaz da Ya Tariq, tsayawa tayi tana kallon hoton idanun ta akan sa, fuskar sa kamar sanda yazo part din Antyn a duk hotunan, kamar dole akayi masa baya so. Taba kofar dakin taji anyi, ta tsaya da abinda take tana kallon kofar, turo kofar Safiyya tayi ta shigo tana kallon hannun Jiddan


"Kina ciki dama jiddah?" Tace tana zama daga gefen ta, cikin rashin sakewa Jiddan tace


"Ina ciki hotuna nake kalla." 


"Kin ganmu muna yara kanana ko?" Tace tana murmushi


"Amira duk tafi bani dariya."


"Ai Amira muguwar mummuna ce taana yarinya, ni da Ya Tariq ne kawai dama masu kyau."


"Gaskiya."


 Tace tsakanin ta da Allah dan safiyyan kamar su daya da Tariq din hatta yanayin shirun su da yadda suke magana.


"Bari kiga sabon Album din kwanan nan." Ta tashi ta dauko mata sabon da suka yi ranar graduation din ta, ta dora akan kafar jiddan ta bud'e mata


Shine a farkon page yana sanye da dogon jeans da farar t-shirt, fuskar sa sake yayi murmushi wanda yayi matukar yi masa kyau, 


"Dama yana murmushi?" Ta samu kanta da tambaya


"Kai sosai ma, sai dai ba kowa yake ma ba, wannan ma ni na saka shi yi wallahi."


Bata ce komai ba, ta bude next page ta cigaba da kalla, kusan dukka hotunan su ne shi da Safiyya, sai wanda Safiyyan da su Amira amma nasa yafi yawa. Hotunan sun yi kyau dukka kamar zaka yi musu magana su amsa ta ciki dan yadda ya dauku sosai.


Dawowa sukayi daga rakasu suka tarar da jiddan tana kallon hotunan suka zauna aka cigaba da kalla tare ana tuna baya,wanda zaa yi dariya ayi


"Kinga na Ya Tariq yana karami?" Maryam tace tana dariya


"A ah." Ta girgiza kai


"Ya Sofy ina album din Ya Tariq dan Allah."


"Salon kuyi masa dariya,ajiya ya bani ba zan baku ba."


"Dan Allah jidda ce zata gani, Yaya boss yana karami."


"Noo ba zan ci amana ba."


"Jidda kice kinaso ki kalla zata dauko, musha dariya"


" A'ah kar a dauko ni dai ba ruwana."


"Kin kwafsa, da mun sha kallo wallahi."


"Dan dai baya nan ne, kunsan da baku isa ba wallahi."


 Ya Safiyya tace tana dariya, abinda ya sake bama jiddah mamaki ganin yadda ta sake tare dasu kamar ba ita ba. 


  Har bayan magriba tana wajensu,dan ji tayi ma kamar tayi ta zama a chan yadda taji dadin yinin ranar. Sai da Aunty ta turo tazo sannan suka rankaya tare da Amira suka koma wajen aunty, basu ga Mama a falo ba kamar ma bata nan dai.



***Kwana biyu Baba ya kara ya dawo cikin rakiyar mutane da yawa, a hanya sukayi magana da Tariq dan tun ranar be samu kansa ba, tare yake da sababbin masu kula dashi DSS har su hudu, sai wasu motocin, dole zaman sa a unguwar ba zai yiwu ba musamman yanayin aiki dole ya zama yana kusa da Mr President sannan kuma da yanayin yadda kasar ta zama dole yanzu sai an samu wadanda zasu zauna da family dinsa su kula dasu kafin ya tattara su dukka su koma chan saboda security purpose.

   Gidan a cike yake taf, Baffa da Iya Lami sunzo duk da be so tahowa da ita ba amma ta nace a dole sai tazo ba yadda ya iya suka taho tare har da Innar su Saude da Sauden, duk sun zo taya Aunty murnaz Baffa kuma Baba.         Kafin isowar Baban gidan ya cika ba masaka tsinke hatta bangaren Yaya a cike yake da yan uwanta da na Malam, Mama ma wajen ta aciken yake da kawaye da yan uwa. Mom din su Safeera ma tazo da kanwar Daddy da Safeeraan. Aunty ce fa gayyato su duk dai dan itama bangaren ta kar ya zama babu kowa tunda su ba yawa ne dasu ba, ba kuma ta san mutanen anan din ba

   Duk girke-girken da akayi Mama ce ta saka akayi order ta fitar ma da Yaya na part din ta haka ma aunty sannan ta bar nata a wajenta. Ta shirya cikin shiga ta alfarma wadda tayi bala'in karbar zubi da tsarin ta, dama Mama yar gayu ce tun da bare yanzu da likafa ta daga ta zama matar minister wadda take jin a yanzu ne tayi daidai da level dinta.

  Itama Aunty tayi shigar ta daidai da ita tayi kyau kuma abinka da dama chan kyayyawa ce sai ta fito fes sosai. Iya Lami tana ta zak'ewa a wajen Auntyn duk da taki yarda sam da ita, Jiddah kuwa daga gaisuwa ko kallon ta bata sake yi ba, tayi zaman ta a daki ita da Safeera.

   Part din Yaya, Baban ya fara shiga kamar yadda ya saba ya gaggaisa da mutane. Yaya kamar ta zuba ruwa a k'asa tasha, dan farin ciki. Daga nan ya shiga wajen Mama itama da nata mutanen suka gaisa sukayi masa Allah ya sanya alkhairi, sannan ya shiga wajen Aunty a karshe.  Daga nan ya dawo wajen su Baffa da aka saka rumfa a harabar gidan suna zazzaune a wajen.

[11/25, 3:54 PM] Rano2: __SL__**

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links