Page (13)
***Wakar perfect wadda Ed Sheeran yayi wadda ake cewa I found a love, for me... ce take tashi a motar tasa a hankali wadda ta saukar masa da yanayin shauki, bi ya shiga yi a hankali tamkar dan shi da ita akayi wakar zuciyar sa fes har yaa isa gida. Yayi parking a tsanake yana cigaba da rera baitin
_ "Cause we were just kids when we fell in love, not knowing what is was,I will not give you up this time.... Darling just kiss slow, your heart is all I own,and in your eyes, you're holding mine... Baby...."_
Sakin murfin motar yayi ya rufe sanda sukayi ido hudu da Daddy yana tsaye yana jin shi yana rera waka, kunya ce ta kama shi, ya hau sosa keyar sa kafin yace
"Good morning Daddy.
"Morning Son, daga ina haka?"
"Nayi dropping Safee a school ne."
"You...?" Ya nuna shi da hannu
"Yaushe ka fara kai ta school ban da labari."
Dariya yayi yana cigaba da sosa keyar tasa, murmushi Daddy yayi amma yasan dole akwai abinda ya sakashi chanja mind dinsa haka,
"Ka kyauta sosai."
"Nagode Daddy."
Sai suka jera zuwa cikin gidan a tare tamkar wasu abokai.
***Tun daga ranar kullum shi yake kai Safeera school Malam Sa'idu ya dauko ta, kuma kullum sai ya labe yaga zuwan su Jiddah. Be taba bari sun ganshi ba, a hakan ya sha daukar ta a hoto dan a yanzu hotunan ta da yake dasu a wayar sa ba zasu kirgu ba, duk da yayi ma kansa alkawarin sai sun shiga ss3 sannan zai mata maganar a time din yana da yakinin zata karbe shi, hannu biyu su fara soyayyar su wadda ya tanadar mata da zazzafar soyayya.
Duk sanda yake free idan a daidai lokacin short break dinsu ne sai ya siyo abubuwa ya kai ma Safeeran school yace ita da jiddah, duk da ko be fada ba ma taren zasu ci amma sai ya sake jaddadawa har Safeera ta fara suspecting dinsa, he care so much akan jiddah har ya fita ma, duk sanda suka zauna a gida sai yayi mata maganar Jidda, me tayi a school yau, me tace hirar su kenan duk sanda suka zauna ko zai koya mata assignment.
Bangaren Jiddah kuwa sosai take picking karatun fiye da yadda kowa yayi tunani, duk da kusan kaso hamsin cikin dari Safeera ce dan kaf class din babu me kokarin Safeera shiyasa kawancen su ya taimakawa jidda sosai ta fanni daban -daban, hatta yanayin yadda take magana da yanayin shigar ta Safeera take kwaikwayo, shiyasa cikin kankanin lokaci ta washe a cikin class din har take iya tsayawa a tsakanin yan class din tana jin itama daidai take dasu. Abubuwa da yawa tare Mom din Safeera take siya musu na gyara da gayu,tun tana jin kunyar karba har ta dawo bata jin komai.
Wani weekend tace ma aunty zata je gidan, bata hanata ba sai dai dole ta rakata har gidan ita da Usman, anan suka gaisa da Maman Safeera sannan ta bar Jiddan, suka ce zasu kawota. Murna wajen Safeera ba'a magana, da farko ganin irin gidan ya saka jikin jiddan sanyi amma kuma yanayin yadda aka karbeta ya saka ta sakin jiki dan hatta masu aikin gidan sun san labarin Jidda a bakin Safeera da Isma'il, ita kanta mom kamar zata goya ta dan murnar ganin ta, labari ya kare yau dai taga Jiddan da Safeera take bala'in so kuma kwarai ta yaba da nutsuwar ta shiyasa taji dadi da ya kasance irin kawayen da yarta take mu'amula dasu.
Kamar wanda aka jeho haka Ya Isma'il ya shigo gidan,waya suke da Mom tace masa Jidda tazo ai ba shiri yayi sallama da su Farouk ya taho gida yana Allah Allah ya iso bata tafi ba. A dakin Safeera ya iske su, ya tsaya daga bakin kofa yana yin kasa da idanun sa sanda suka hada ido da Jidda a lokacin da take kyalkyala dariya, dariyar da ta saka bugun zuciyar sa tsaya chak na dan wasu dakiku.
"Ya Isma'il." Safeera tace tana mikewa daga kan gadon
"Look who's here."
"Jidda." Ya kira sunan ta kamar wani dolo
"Na'am, ina wuni?"
"Lafiya lou, ashe zaki zo da gaske."
"Umm.." Tace tana wasa da hannun ta, hannun ya kalla yaga yatsun ta zara-zara, juyawa yayi da sauri ya bar kofar, Safeera ta dawo ciki suka cigaba da hirar su, daga nan suka dauko books din Safeeran sukayi karatu, wajajen karfe biyar Mom tace Ismail suje su kai ta, kafin ma ta rufe baki ya mike cike da zumudi, kallon sa tayi, ya dauki car key din motar ta, ya ajiye nasa sannan yace
"Bari na jira su a mota." Yayi gaba yana kada key din motar, tashi Mom tayi taje dakin ta, ta hadowa jiddah sha tara ta arziki tun daga kan underwears zuwa turare da kayan kwalliya, sai atamfa da veil, sannan ta saka mata 5k a cikin envelope ta fito ta iske su a dakin Safeeran tace su taso, turo baki Safeera tayi cikin shagwaba ya hau bubbuga kafarta kamar zatayi kuka
"Dan Allah Mom ki bari sai anjima ðŸ˜."
"A ah kar dare yayi, ni nayi ma Maman ta alkawarin zaa kawota, gwara ido na ganin ido ko Jidda? Kar babanku ya dawo yayi fada."
"Eh." Jidda tace tana yafa dan madaidacin veil dinta
"Allah ni...." Ta cigaba da buga kafarta, dariya kawai Mom tayi ta mikawa jidda kayan ta russuna har kasa ta sa hannu ta karba tayi godiya
"Kuje yayanku yana mota yana jiranku, sai yaushe Jidda?"
"Wataran." Tace tana murmushi
"Kice ma ba zaki sake zuwa ba." Safeera ta fada tana hararar ta
"Sorry mana."
Tace tana kallon ta, shiru tayi dan taji haushin tafiyar da jiddan zatayi, ta bude wardrobe dinta ta dauko veil ta dora akan inner cap din dake kanta ta zura slippers suka fito hannun ta rike da ledar kayan da Mom ta bawa jiddan.
Yana zaune a mota ya hango sun fito, ya cire lock din motar ya fita ya budewa Jidda baya ta side din driver, ita kuma Safeera ta shiga gaba, ta sama Mom ta hango duk abinda ya faru, ta girgiza kai kawai tayi murmushi dan dama tana suspecting Isma'il din son yarinyar yake, sai dai bata tabbatar ba sai yanzu da taga abinda ya faru, sakin curtains din tayi bayan sun fice daga gidan.
A hankali sosai ya shiga driving din kamar baya tafiya ma, sanyi da wakar da ke tashi motar ta saka duk basu lura da yadda yake tukin ba, maimakon ya wuce gidan su Jiddan kai tsaye sai ya tsaya dasu sahaibco stores ya siya musu chocolates masu yawa da ice-cream sannan suka cigaba da tafiyar wahainiya har suka iso ba dan ya so ba, yayi parking suka fita tare da Safeera ta rakata har cikin gidan sannan ta dawo suka tafi gida.
***A harabar gidan sukayi kicibis da Mama, tana fitowa daga part din Yaya wanda tun sanda tazo gidan be fi sau biyu taga Maman a bangaren Yaya ba, kallon ta Maman take dan ta kwana biyu bata ganta ba, sai taga tayi shar da ita ta kara wayewa tamkar ba ita ba, durkusawa tayi a tsorace ta gaida Maman, ta amsa kamar taga kashi ta wuce ta bata sake ko kallon ta ba. Bata ji komai ba dan dama ba wai suna haduwa bane tunda ba zuwa wajen ta take ba, haka kuma ko a compound din gidan basu cika haduwa ba dan idan Mama na gida ko yaushe tana part dinta itama kuma Jiddan ba yawo take ba wajen Yaaya kawai take zuwa shima ta dayar hanyar take bi taje ta dawo. Ita har ga Allah tsoron Maman take dan ba karamin kwarjini take mata ba musamman da taga hatta Aunty ma shakkar ta take shiyasa ta shafawa kanta lafiya bata taba shiga part din ta ba ko da wasa duk nacin su Amira sun gaji sun hakura dan ita bata cika son shishigi a in da ba'a son ta ba.
Rayuwar ta, ta chanja a dan lokacin nan babu abinda zata ce sai godiyar Allah dan ko a haka Allah ya barta ta gode dan bata yi tunani ko hasashen ta a irin wannan rayuwar ba, rayuwar ta ta baya ta tuna ta girgiza kanta ta furta alhamdulillah, daga haka ta wuce wajensu ta samu Aunty tana bude kayan da Mom din Safeera ta bata cike da yabawa dan ba karamin kaya tabata ba masu kyau kuma da tsada, ita kanta Auntyn tayi mamakin gidan su Safeeran dan yadda suke babu girman kai ba zaka taba zaton haka gidan su yake ba
"Bafa karamin kaya matar nan ta baki ba jidda, ko wannan atamfar Babba ce wallahi."
"Taki ce ai atamfar Aunty."
"Tawa?" Ta waro ido tana daga
"Eh cewa tayi na kawo miki."
"Kai, kai hadda ni kuma?"
"Eh."
"Kai amma naji kunya, Nagode zan kirata dama in sha Allah nayi mata godiya, hade kayan ki kai daki."
Toh tace ta tattare kayan ta kai daki sannan ta dawo suka zauna da Auntyn suka cigaba da hira. Daga nan ta kira musu Baffa suka gaisa sannan suka tashi don yin sallar magriba da aka soma kira a wasu masallatan.
***Kwanan sa hudu yana avoiding yarinyar, ta shiga rayuwar sa sosai komai yake ko ina yake sai ta bishi, gashi shi mutum ne da baya son a shiga rayuwar sa idan har ba shine ya gayyato mutum ba. Nacin ta shi yafi komai damun sa gashi sam bata da zuciya duk yadda ya kai da nuna mata baya son yadda take bin sa amma bata ganewa, shi ko sunan ta be sani ba sai ranar da ta fada masa da kanta, daga ranar be kuma sake tuna sunan nata ba ya manta. Zaman sa ya cigaba da yi a daki duk da yana da lectures amma baya son ya fita su hadu shiyasa ya hakura ya zauna yana bin lecture din online yana following komai, baya so ko kadan ya dauke idanun sa daga kan system din baki daya ya tattara hankalin sa waje daya yana yi yana jotting down key words din. Door bell dinsa ce tayi kara alamun yana da bako, ya daga kai ya kalli agogon dake makale a saman table din nasa, be san wanda zai kawo masa ziyara a irin wannan lokacin ba, duk da yasan bazai wuce Ishaq ko xuo kaiy ba, amma kuma ya san suna class a wannan lokacin kuma babu abinda zai fito dasu, sake kad'a bell din akayi, ya tashi yana jan siririn tsaki, ya shiga takawa kafarsa sanye da white socks zuwa kofar dake gaban dan corridor kafin main cikin gidan. Budewa yayi ya kalleta cike da mamakin ganin ta, basket ne a hannun ta me kyau, ta sakar masa murmushi ya dan saki fuskar sa kadan yana tsaye still akan kofar
"Zan iya shigowa?" Tace tana kallon cikin gidan, da sauri ya girgiza mata kai
"Ba zan iya ba?"
"Eh." Yace kai tsaye, dan jim tayi a tsaye, shima ya cigaba da tsayawa a wajen sai tayi murmushi ta mika masa basket din
"Lunch nayi maka naga baka fita school ba"
Sai ta mika masa ya miko hannun sa ya zai karba hannun su ya hadu da na juna, da sauri ya janye yana bata fuska saura kadan basket din ya fadi abinda yayi matukar bata mamaki.
"Shikenan?" Yace yana rike da basket din a kaikaice, kasa magana tayi dan tsabar takaici, ta daga masa kai alamar eh
"Ok, thank you."
Yace ya juya rike da basket din, ya tura kofar sa ya barta a tsaye a wajen kamar wadda aka dasa saboda tsabar mamakin sa. Kusan minti biyar ta dauka a tsaye a wajen ta gaza aiwatar da komai, kafin daga bisani cikin yanayi na bacin rai ta bar wajen fuuuu.
A gaban kofar ya dire basket din, yai gaba abinda ko budewa be yi ba bare yaga abinda yake cika.