SANADIN LABARINA 12


    Page (12).



***Daidai gwargwado yaran sun fara dawowa kamar da duk ba dukka ba amma suna shigowa wajen jiddan ko su hadu a wajen Yaya, saura kwana uku a koma school sai ya zama kawai shirye-shiryen komawa suke tunda sabon session ne. Text books din Ss1 amira ta bawa jidda ita kuma ta karbi na Maryam a kalla an samu sauki. Duk da Baba babu laifi alhamdulillah harkoki na kara bud'e masa musamman da yanzu siyasar ta juyo kansa da gaske yake yin ta,ana kuma saka ran zai samu babban matsayi a gwamnatin tun kafin zabe yazo. Gidan da yake jikin nasu akayi masa talla bayan Maigidan ya rasu ya zama na magada, siyewa yayi ya fashe ya shigo dashi cikin gidan nasu dan so yake ya fitarwa da kowa part dinta me zaman kansa tsakanin Mama da Auntyn yadda kowa zata ci gashin kanta, sannan yana so ayi gyaran part din Yaya itama. 

   Ana jibi zaa koma makaranta Safeera ta kira wayar aunty daga cikin wayar Mom dinta tace zato zo, kwatance aunty tayi ma Maman Safeeran bayan sun gaisa tace zata saka a kawota dan tun da akayi hutu take maganar jiddan.  Ita ma jiddan tana maganar ta amma tasan ba kamar Safeeran ba dan ta damu sosai da ita, ta kan kira a wayar Aunty su yi magana. Wanka jidda ta tashi tayi, ta sake gyara dakin ta ta zauna zaman jiran bakuwar tata ko wajen Yaya bata je ba, tana zaune Usman yazo ya kirata yace tazo in ji Aunty wai kawarta tazo, da sauri ta fito ta samu Safeeran a zaune a kujera ita da wani saurayi wanda zai yi sa'an Ya Fauwaz ko ya dan girme shi, da sauri Safeeran ta tashi ta rungumeta, cikin farin ciki, dariya suka bawa su Aunty da saurayin da ya gaza boye farin cikin sa


"Sannun ku da zuwa." Tace bayan sun saki juna sun zauna a tare


"Yawwa." 


Yace idanun sa na kan jiddan, be taba ganin yarinya me kyawun ta ba, take tashiga ransa duk da shekarun ta basu kai shekarun da yake jin ya kamata ta san soyayya ba, tashi yayi bayan sun gama gaisawa yace zai je ya dawo anjima ya dauki Safeeran, har ya mike tace


"Ya Isma'il dan Allah ka bari sa dare."


"Ko? So kike mom ta hanani shiga gida kenan."


"Ba zata ce komai ba Allah."


"Da yamma dai zan dawo."


Bata fuskar ta, tayi kamar zatayi kuka, ya juya ya fice yana jin dukkan wani karsashin da yake dashi yana gushewa, love and first sight kenan, zai iya jira a yadda yake ji, zuwa lokacin da ya chanchanta. Da kyar yayi driving kansa zuwa gida ya shiga falon ya tarar da Mom da wata Aunt dinsu kanwar Daddy, gaishe su yayi, ya shige dakin sa ya kwanta rigingine yana kallon sama.

 

"I'm in love." Ya furta a hankali yana lumshe idanun sa.


Gidan su Safeera babban gida ne sosai kuma suna da kudi dan Baban su babban dan boko ne kuma business man, su biyu iyayen suka haifa daga ita sai Ya Isma'il, suke nan su daga kansu Mom bata sake haihuwa. Rayuwar su suke cikin jin dadi sosai, gashi sun shaku da Ya Isma'il ko yaushe suna tare da junan su, yau ma da driver ne zai kaita gidan su jiddan amma sai yace zai kaita dan shima yaga jiddan da kullum take maganar ta, sai gashi abinda be yi tunani ba ya faru, a cikin dan kankanin lokaci ya kamu da soyayyar yar karamar yarinyar da ba dan kar yayi karya ba sai yace Safeera ma zata iya girman ta, be sani ba amma ko yanayin jikin ne dan mafi akasari fulani basu da girman jiki.

    Juyi ya dinga yi shi kadai ya rasa abinda yake masa dadi sam,har sai da Mom ta biyo shi jin shiru be fito ba, a tunanin ta bacci yake amma sai ta ganshi a kwance, ta tambaye shi abinda yake damun sshi, kamar ya fada mata gaskiya sai ya kasa ya girgiza kai kawai yace hutuwa yake, fita tayi sai ya tashi kawai ya bi bayan ta dan zaman haka ba zai amfane shi da komai ba.


****Zuwan Safeera yayi ma jiddah dadi sosai, ta ware sosai har ta bawa Aunty mamakin yadda ta sake da Safeera bata sake da kowa haka ba, tare suka ci abinci sannan ta ja ta wajen Hajiya Yaya, suka dade anan har Amira tazo itama tayi joining dinsu, suka saka Yaya a gaba ta dinga biye musu ana dariya. La'asar din farko farko sai ga Ya Isma'il yazo, suna part din Yayan Usman yazo kiransu, Safeera bata so ta zata zai kyaleta sai daren, dan idan sun koma gidan ma babu abinda zatayi gashi ba kowa. 

   Turo baki tayi sanda suka shigo falon Auntyn yana zaune a kujerar dake facing hanyar shigowa, idanun sa akan hanyar yana jiran ya ga ta in da zasu bullo, ajiyar zuciya ya sauke da karfi sanda suka shigo wanda har da Aunty ta kalle shi, ya waske da sauri yana mikewa


"Nace fa sai dare Ya Isma'il."


"Ni kuma nace dama da yamma zanzo ai."


"Muna shan hirar mu."


"Wai haka jiddaaaah?" Ya ja sunan batare da ya san yayi ba


"Eh." Tace tana murmushi, murmushiin shima yayi mata sannan yace


"Zamu sake dawowa aunty, akwai in da zanje anjima ne shiyasa nazo yanzun."


"Ba komai Isma'il, itama Jiddan zatazo in sha Allah."


"Yaushe?" Ya fada da sauri, sai ya hau sosa kansa bayan yayi maganar


"Ko weekends dai, tunda an koma school."


"Ok, Allah ya kaimu."


"Amin." 


"Ungo jidda, rakasu."


"Tohm." 


Ta karbi yar madaidaciyar ledar suka fita tare, ta rakasu har wajen mota sannan ta mika ma Safeera ledar da Auntyn ta bata, ta karba tana leka ciki sannan tace ta gode.


"Wai kuwa kuna da hoto tare ku biyu?" Ya tambaya bayan dogon nazarin da yayi, girgiza kai Safeera tayi ta fasa shiga motar


"Yawwa Yah snap us dan Allah."


"Ok." Ya ciro wayar sa, ta dafa kafardar Jiddan ya dauke su tare, yana lura da yadda kunya ta kama jiddan, yayi murmushi yace


"Bari ayi ma kowacce ita kadai, na tarihi."


"Yes, fara dani."


"A ah bari na fara da jidda " 


yace yana maida wayar saitin ta,ya kashe flash din ya shiga daukar ta pretending ba dauka yake ba, sai da ya dauke ta sosai sannan ya kunna flash din yayi mata guda daya, sannan yayi ma Safeera ma. Daga nan suka tafi ita kuma ta koma cikin gidan.

   Suna shiga gida Safeera tayi dakin Mom shi kuma ya wuce dakin sa, ya bude wayarsa ya shiga photos ya zauna  zaman kallon hotunan yana admiring kyauwun ta, idanun ta da dan karamin lips dinta shi yafi komai burge shi da ita, yana zaune yana ta kalla Farouk ya shigo, ya fizge wayar yana kallon screen din, kafin ya kalli Isma'il din irin kallon tuhumar nan,


"Kana nufin... No no no it's not possible, wannan ai child abuse ne."


"Inji waye? Rainon ta zanyi."


"Are you serious? Wannan yar yarinyar zaka tsaya jira?"


"Yes of course, menene a ciki?"


"No you most be kidding, ai ba zai yiwu ba."


"Kasan Allah? I'm serious, very very serious. I love her, with every bit of me,love at first sight, so mara algus kenan."


"But she looks so local, beside yarinya ce karama sosai, not your type though."


"Kai kaga haka, ni na san me na gani."


Kifa wayar Farouk yayi a saman gadon yana zama akan couch din dake dakin ya maida kansa baya yana rufe idanunsa sannan yace


"Ba zan iya cigaba da sauraran wannan tale din ba."


"Yafi maka, kuma zan baka mamaki."


"Allah ya bada sa'a, mu namu dai ido ne."


"Yafi dai." 



***Monday akayi resuming school, da wuri Isma'il ya tashi ya shirya ya fito falo ya samu Safeera tana breakfast, Mom kuma tana karasa hadawa daddy breakfast dinsa, kallon shi tayi cikin yanayin mamaki tace


"Ina zaka? Kai da baka tashi sai kusan 11, ko kana da morning lectures ne?"


"Safeera zan kai school." Yace yana hayewa saman dinning din, kallon sa duk sukayi da mamaki, ya share ya hau bude warmers din yana lekawa, ba zai iya cin komai ba sai ya dawo dan he's so eager ya ganta baya so su riga su zuwa har su shiga class shiyasa ma ya shirya da wuri ya samu itama Safeera ta shirya. Ajiye ragowar sandwich din hannun ta,tayi ta mike ta sakala school bag dinta a kafadar hannun ta daya tace


"Na gama Mom." Mikewa yayi shima yace


"Oya let's go karki makara."


"Malam Sa'idun fa?Kamar yazo fa tun dazu."


 Mom tace cikin rashin gane kan Isma'il din.


"Na hutassheshi, muje kid sis."


"Ok."


 Tace tayi ma mom sallama suka fita tare, girgiza kai mom tayi a ranta tasan dole akwai dalilin da zai saka shi fita da safen kawai ya boye mata ne. Malam Sa'idu dake zaune a cikin mota yana jiran ta yaga sun fito ya bude motar da sauri Isma'il yace


"Zan sauke ta Baba, kaje gida kawai."


"Toh toh, shikenan." 


Ya tada motar ya fita daga gidan suma suka bi bayan sa. Suna cikin tafiya ya tambaye ta


"Karfe nawa su jidda suke zuwa school?"


"Umm, ina rigasu zuwa gaskiya, kaga suna da yawa sai sun gama shiryawa."


"Good!" Yace yana murmushi


"Na'am?" Ta kalle shi


"No ba komai." Ya basar yana sake rike motar, cikin kankanin lokaci suka isa school din, kudi ya ciro a cikin wallet dinsa ya bata, 


"Mom ta bani fa."


"Eh ku kara ke da Jidda, ku siya duk abinda kuke so."


"Ok thank you." Ta karbe ba tare da ta kawo komai ba, ta shiga school din bayan ya ja motar a tunanin ta, ya tafi. Gefe ya samu yayi parking ya zauna zaman jiran zuwan su, idanun sa na kan duk me wucewa ta cikin layin, har zuwa sanda suka iso, ya bude murfin motar da sauri ya fito ya tsaya jikin motar yana kallon su, a in da yake tsaye ba zasu ganshi ba amma shi yana kallon su, Amira ce ta fara fitowa sai ita, cikin uniform din nasu navy blue da white Hijab wanda yayi matukar yi ma yar fuskarta kyau, tamkar yar tsana haka ya ganta, gashin da ke kwance a gaban goshin ta ya fito sama-sama wanda ya karawa kyakyawar fuskar ta kyau. Wani abu yaji ya tsirga masa, ya jingina sosai da motar dan ji yake tamkar yana yawo a gajimare, yana nan tsaye har suka shige cikin school din sannan ya sauke ajiyar zuciya ya fada motar ya bata wuta ya fita daga cikin line din a guje.



Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links