Page (11)
***Jidda da Usman ne kawai a falon tana karatun Qurani Baban ya shigo, karo na farko tun zuwan ta gidan da taga Baba a part din nasu, da sauri tace.
"Baba sannu da zuwa."
"Yawwa Hauwa'u, ana ta karatu?"
"Eh."
"Toh Masha Allah, a bada himma ko?"
Daga kanta tayi,ya dauki Usman ya wuce dakin Aunty. Tana zaune jigum duk babu dadi, dawowar ta ciki kenan ta bar jidda ta usman a falon so take ta dan kwanta ko kanta dake sara mata da ciwo zai rage, sai ganin Baban tayi ya shigo dauke da usman. Mamakin ganin sa ya sakata tashi da sauri
"Sannu da zuwa." Tace tana kallon shi, shima ita yake kallo, ta rame sosai tayi haske,
"Kin ganki ko Halima?"
Sunkuyar da kanta tayi k'asa, ya girgiza kai yana daga tsayen yace
"Idan fa baki cire damuwr komai ba fa zamu bata gaskiya."
"Na cire, kai na ne yake ciwo."
"Ehen, kinji ko? So kike sai kin kwanta zaki ji dadi ko?"
" A'ah." Ta girgiza kanta tana jin wasu hawaye masu zafi na neman zubo mata
"Toh bana so, ki dawo yadda kike kiyi rayuwarki yadda Allah ya tsara miki, bakya bukatar fahimtar da kowa baki da hannu a abinda ya faru,duk wanda ma ya zarge ki kansa, ke dai ki tsarkake zuciyar ki."
"In sha Allah, Nagode."
"Madallah, a taimaka min na watsa ruwa na dauko gajiya, sannan a dan bani Lipton kadan."
"Tohm." Tace ya juya ya bar part din, turare ta dan fesa a jikinta tabi bayan sa zuwa part din sa.
***Hannun sa dauke da ledoji niki-niki ya shiga part din Yayan, tana ganin shi ta dalla masa harara, kafin idanun ta su sauka akan hannun sa, daga mata ledar ya dinga yi ta washe bakin ta bayan ta hango ayaba, a gabanta ya ajiye ledojin sannan yace
"Gimbiya Yaya ga shi inji sabon angonki, wato ni."
"Me karya?"
"Dan aljanna."
"Kai tafi chan, d'ana ne ya siya min ba kai ba, mai alkawarin da baya cikawa tir!"
"Toh ai Yaya kece da rowar tsiya, kinga ai kin bani ba dan Allah na."
Jefa masa pillow din kujera tayi ya chafe yana dariya.
"Bari na dauko mana plate mu bajeshi mu kwashi dadi."
"Naga uban da ya isa ya taba min, wallahi baka isa ba."
"Ni fa na siyo, naji kamshi amma kice ba zaki bani ba?"
"Ai ba dan Allah ka siyo ba."
"Ai shikenan, aci lafiya."
"Ka ja min kofa idan ka fita." Tace tana tattare kayanta, ta shige uwar daki ta bar shi yana dariya.
***Da safe Tariq ya gama shiryawa cikin kananan kaya bakar long sleeve shirt da black trouser ya dora brown katotuwar rigar sanyi akai,hannun sa sanye da handsocks me kauri, sai kafarsa da ya saka socks wajen hudu ya dora brown takalmi. sake gwada kiran wayar Auntyn yayi hannun sa daya rike da cup din tea me zafi, har ta gama ringing ba'a dauka ba, a aljihun wandon sa ya saka wayar ya goya jakar da tarkacen takardun sa hade da system ke cika, ka fito ya hau lift ya sauka kasan building din, ya shiga takawa a kafa zuwa cikin makarantar da basu da nisa da gida, pcap ce akan sa da ta sauko har wajn girar sa, baya kallon kowa tafiyar sa kawai yake yana shirya abinda zai gudanar a ranar.
"Hi."
Ta tsaida shi ganin kamar be lura da ita ba, dagowa yayi ya kalle ta, ta sakar masa murmushi tana kallon fuskar sa
"Hi." Shima ya maida mata kafin ya cigaba da tafiyar sa, da dan saurin ta, ta cimmasa, ta sake tsaida shi
"Baka gane ni ba?"
Ta tambaya ganin yana mata kallon wacece ke? Girgiza kansa yayi, sannan yace mata
"Ban gane ba."
"Okh, mun hadu a library last week har na karba pen dinka nayi signing, ka tuna?"
"Oh yeah, na tuna. Sannu."
"Yawwa, thank you."
"Amm...sauri nake ina da meeting da supervisor dina, bye."
"Bye!" Ta daga masa hannu, ya juya ya cigaba da tafiya, ta tsaya a wajen tana kallon sa har ya shige cikin building din.
"Perfect!"
Ta furta tana jan ajiyar zuciya.
Apartment dinsu daya tun ranar da suka hadu a library ta bishi sai ta ga ashe gida daya suke shi amma yana 5th floor ita kuma tana 2nd, tun daga ranar take min duk wani moves dinsa,shi kadai yake rayuwar sa, sai abokan sa biyu daya shima dan Nigeria ne sai wani dan China, sosai yayi mata har ya zama kullum sai ta makale ta leka shi da safe idan ya fito zai tafi exercise, wani lokacin har chan take bin shi ya gama ta sake biyo bayansa su dawo tare amma bata taba bari ya gane ba.
Bata da abinda zatayi a cikin school sai kawai ta koma gida ta kwanta sai da rana take da lectures dama dan kawai su hadu ya sakata fitowa a lokacin. Yau da taji muryar sa sosai sai take jin kamar an saka ta a aljanna, he has something a cikin voice dinsa da ya sakata kusan suman tsaye, very deep and sweet.
****Shigowar aunty kenan daga part din Baba ta dau wayarta, taga missed calls dinsa, ta tuna jidda ma tace ya kira shaf ta manta bata kira shi ba, yanzu kuma ya sake kira bata kusa, tasan shi da naci akan abu ta kuma tabbata magana zai mata akan wani abun tunda har ya sake kira. Kiran sa tayi tana fatan koma menene dai yasa ba babban abu bane, shigar sa kenan library yaji wayar sa da take a vibration na motsi, dubawa yayi yaga Auntyn ce, sai ya tashi ya fito daga ciki dan kar ya damu masu karatu ya sako kasan ya bi ta kofar baya zuwa wani dan karamin garden da yake cikin library din, ya zauna a cikin daya daga cikin kujerun wajen ya kira dan dama katse kiran nata yayi. Yana kira ta daga,
"Tariq?"
"Na'am, barka da safiya Aunty."
"Barka dai, ya karatu?"
"Alhamdulillah, ya karin hakuri?"
"Da godiya, alhamdulillah." Ta fada a sanyaye
"Na kira ranar nayi miki gaisuwa yarinyar nan ta daga."
"Jiddah, eh tafada min sai na manta ban kira ba."
"Mmm... Dama Aunty magana ce nake so muyi."
"Toh ina jinka.*
"Akan maganar abinda ya faru ne, da abinda su Mama suke cewa, kiyi hakuri pls."
"Ba komai ai Tariq, ba komai wallahi."
Shiru yayi kamar zai sake magana sai kuma yace
"Shikenan toh, sai anjima."
"Okh sai anjima."
A sanyaye ta rike wayar, a kasan ranta tana godiya wa Aallah da ya saka akwai mutanen da suka fahimce ta, suka fuskanci halin da take ciki. Mutanen kuma da suke da kusanci da Muhammad idan ka dauke mahaifiyar sa.