Page (10)
***
"Karka kuskura ka bude min kwano."
Tayi saurin cewa ganin har ya zauna rike da flask din
"Hajiya Yaya rowa dai babu kyau, gani zan me muka samu kinsan fa ni da ke akwai amana."
"Yanzu na gama saka abu kaki yi, wacce amana kuma."
Ta harare shi tana tabe baki, da sauri ya dauki wayar da ya manta yayi kira, yaga har Tariq din ya d'aga har ya katse kiran ma
"Kinga har ya d'aga fa, na manta na kira."
"Ina zaka tuna kaga kwano."
Dariya Jidda tayi, ta gaida Yayan ta zauna tana kallon d'aurin da tayi a kafarta
"Yaya kunshi kikayi?"
"Eh yar albarka, kinsan mu bama iya barin kafarmu kod'ai kod'ai ba lalle, kiga kafa fara kal babu kyawun gani, wannan sai yaran zamanin nan, mu ina."
"Yaya gashi ya daga, video call ne ma."
Matsowa tayi da sauri, ta zauna a kubin sa sannan tace
"Hasko min shi, kaga ba hannu."
Matso da fuskar ta tayi, Tariq dake tsaye rike da water bottle jikin sa sanye da riga armless, hannun sa da yake a murde Yaya ta kalla, sai kuma ta kalli fuskar sa da take kamar kowanne lokaci tace
"Menene haka kake zaune babu kaya?"
"Babu kaya?" Yace a kasa sosai, amma duk da haka sai da taji, sai kuma ya kalli kanshi
"Eh wannan ai sakarci ne."
"Bamu gaisa ba fa Yayah, ina wuni?" Yace yana kin biye mata
"Lafiya lou, kana lafiya?"
"Eh, kefa?"
"Oho ban sani ba."
Kallon ta yayi, ta harare shi yayi saurin dauke idon sa, yana barin wajen da yake, yana jin ta tana magana da Fauwaz k'asa -kasa, yayi kamar be ji ba ya cigaba da zare igiyar takalmin dake kafarsa,
"Kana ji ko? Kana shan maganin naka kuwa?"
"Magani?" Sai ya tuna da sauri yace
"Eh ina sha."
Washe baki tayi,
"Ka kyauta." Sai kuma ta rage murya ta kalli Jiddah dake zaune a dayan gefen nata tace
"Maganin ya fara masa aiki.".
Ya jita sarai sai yayi kamar be ji ba yace
"Yayah zan fita school, zan kiraki idan na dawo."
Yace bayan ya gama zare takalmin
"Toh babu damuwa, ka dai cigaba da shan maganin kaji? Karka yi wasa dan aljanu mugaye ne wallahi, duk abinda kake yi nasan ba yin kanka bane aljanun gado ne."
"Bye."
Yace ya katse kiran,sai kuma yayi murmushi kadan, matar baki dayan ta drama queen ce, zatayi kyau da acting.
Sai ya sake murmushi ya girgiza kansa yana ajiye wayar
Haushi ne ya tirnike Yaya ganin bata gama bayani ba ya katse kiran, har Jiddah taso a bawa su gaisa gashi tana son ta masa wata magana amma dan wulakanci shine yace mata wani bye ya kashe
"Uwar bye din, mtsw!" Tace tana mikewa
"Kar ya makara school ne fa Yaya, Amma zai kira nasan yana dawowa, baki ga alamun ya chanja ba? Ai maganin yana aiki sosai."
"Allah?"
"Da gaske baki gani ba?"
"Umm na gani fa."
"Ehen, da kansa ma zai fara kiranki ne da maganin ya gama bin jikinsa."
"Eh gaskiya kuma haka ne, toh shikenan yanzu ka tashi ka je, tunda yar fillon nan tazo sai muyi zaman mu.*
"Abincin fa Yaya? Yunwa nake ji." Ya kai hannun sa akan flask din da sauri tace
"Karka kuskura ka taba min funfulaye (foodflask) kaji na fada maka."
Zare hannun sa yayi ya mike, ya daga hannun sama yace
"Ban taba ba, bari naje na samo balangu me zafi da lemon exotic naci kayana nima."
"Tsaya, balangu zaka siyo?"
Tace tana washe baki
"Eh ba, amma ko guntu ba zaki ci ba."
"Haba kai kuwa, wasa fa nake maka, dauki kaci ka rage min, sai kaje ka siyo mana naman amma nawa kar su saka yaji ulcer, lemon ma bana son me gas kaji?"
"An gama."
Ya dawo ya dauki plate ya zuba rabin alalar ya zauna ya cinye tas, ya sha ruwa yayi gyatsa, sannan ya mike yana zura hannu a aljihu
"Tunda dai ciki ya dauka, bari naje na dan yi siesta."
"Wajen me naman ne sita?"
"Eh eh, nan ne kuwa, bari naje." Yace yana kunshe dariyar sa
"A dawo lafiya."
Tace dadi na kamata, ba zata ci alalan ba har sai ya kawo balangun ta ayyana a ranta. Ido daya ya kashe wa jidda sannan ya fice yana dariyar mugunta.
Shiru shiru babu shi babu alamar sa, tun da zata cire kunshin take cewa safwanu shiru, har ta gama Jidda ta zuba mata ruwa ta wanke shiru be dawo ba.
"Jeki dubo min shi jidda, kar dai yaron nan wayo yayi min."
"Toh." Tace tana mikewa, ta fito tana tunanin ina zata dubo shi, part din Aunty taje ta kira Usman tace ya dubo mata Ya Safwan a bangaren su, yaje ya dawo yace mata bacci yake, komawa tayi ta fada ma Yaya aikuwa ta dinga balbalin masifa da kyar ta hakura tayi shiru amma ta shirya rama abinda yayi mata.
****Washegari Baba ya dawo, kai tsaye part din Yaya ya wuce ya tadda ita tana zubawa kadangaru ruwa da abinci me manja, kasancewar part din nata ginin kurzu kurzu ne ya saka wajen ya zama matattarar gadangaru shikenan take zuba musu ruwa da abinci kullum. Shigowar Baban ya sakata dakatawa.
"Sannu da aiki Yaya?"
"Yawwa, dawowar Kenan?" Tace tana ajiye kwanon hannun ta,
"Eh wallahi, saukar kenan Yayah, mun sameku lafiya?"
"Lafiya lou ba lou ba."
"Me ya faru Yaya?"
"Bari na kawo maka ruwa kasha."
Tace tana nufar randar ta da ta saka aka kawo mata tun daga chan wai tafi ruwan firij sanyi, kawo masa tayi ya sha yayi hamdalah sannan yace
"Me ya faru Yaya?"
"Uhum. Menene ma be faru ba? Gida ya zama kamar kango babu me yi da wani, fisabillillah, abinda ya riga ya faru ai ya riga ya faru ko?"
"Haka ne."
"Ni gaskiya bana son shirun nan, ita Halima tana jin cewa bata kyauta ba ita kuma Aishatu tana jin ba'a kyauta mata ba."
"Duk nayi magana dasu wallahi Yaya, na kuma nusar da kowaccen su akan hakuri da daukar kaddara, amma ba komai zan yi maganin abun."
"Yawwa, gwara duk su yi hakuri sannan su kyale yara su cigaba da rayuwar su kamar dah, shirun ya ishen baki na har doyi yake saboda zaman kadaita, na gaji."
"Zaa gyara in sha Allah."
"Yawwa Allah yayi albarka, shi kuma me babban suna Allah yasa me cetonmu ne."
"Amin Yayah."
"Bari na shiga ciki Yaya,babu wata matsala dai ko?"
"Babu sai guda daya take, yaron nan ni yayi wa wayo yace zai siya min balangu, na saka rai yazo ya hanani, wallahi har mafarkin balangun nan nayi."
"Kai Kai kai, be kyauta ba, yanzu yanzu zaa kawo miki balangu da tsire da kuma me?"
"Leman bawo da yar ayaba."
"Shikenan an gama."
"Allah yayi albarka, yasa kaima yarannan su rama maka."
"Amin ya Allah."
***Maimakon ya wuce part dinsa sai ya nufi bangaren su Fauwaz din ya kwankwasa masa kofa ya kira sunan sa, tashi yayi da sauri jin kiran Baba ya bude.
"Mutanen garin ku, shine ka sakawa uwata rai kasan ba bata abu zakayi ba ko?"
Dariya yayi shima Baban ya saka dariya
"Maza kaje ka samo mata balangu da tsire, ka hado mata da lemo da ayaba masu kyau, kayi sauri kuma."
Ya mika masa kudi, hannu yasa ya karba sannan yace
"Ok tohm."
Juyawa Baban yayi shi kuma ya koma daki ya chanja kayan jikinsa ya fito, ya dauki motar ya tafi siyo mata abinda Baban yace, tun ranar be je part dinta ba dan yasan haduwar su ba zatayi kyau ba.
Part din Mama ya wuce kai tsaye, dan ba wanda ya san ya dawo, yaran duk suna falon a zaune maimakon yadda suke zama a main falon gidan tun bayan abinda ya faru Mama ta hana suna kunshe a part dinta, shigowar Baban ya sakasu duk mikewa Safiyya dake waya da saurayinta Mahfouz tayi saurin katse kiran. Bin su Baba yayi da kallo dukka yana nazarin maganar Yaya
"Sannu da zuwa Baba."
Suka hada baki dukka suka fada a tare, be amsa ba sai ya gid'a kansa kawai yana wucewa bedroom din Maman. Jikin su ne ya basu sai suka tashi suka shige bedroom dinsu.
Umaima ce tare da Maman tana tayata jera wasu sabbin kaya da tayi a wardrobe sallamar Baban ta iske su,ajiye rigar dake hannun ta tayi, ta russuna ta gaida Baban sannan tayi saurin ficewa daga dakin.
"Sannu da zuwa." Mama tace tana ajiye kayan hannun ta, ta nufo wajen Baban
"Yawwa Maman Yara." Yace cikin shigar tsokana
"Banji dawowar ka ba Sam."
"Ai ban dade ba, na fara zuwa wajen Yaya ne, kuma dai Malam Basiru be shigo da motar ba akwai sakon da zai karbo min shiyasa."
"Sannu da hanya."
"Yawwa, a bani wajen zama Maman Yara."
Da sauri ta jawo babban carpet din da take sallah akai me taushi ta shinfid'a masa a gaban gadon, ya zauna itama sai ta nemi gefen sa ta zauna.
"Yawwa ko kefa, a bar matafiyi a tsaye?"
"Ban dauka zaka zauna ba wallahi, bari na dauko ruwa da abinci."
"Barshi tukunna, babu yunwa dan tun rana muka dawo na tsaya ne dai a government House, kuma Yaya ta bani ruwan randar ta me sanyi nasha."
"Masha Allah, fatan an samu abinda aka je nema."
"Alhamdulillah, gaskiya."
"Toh Masha Allah."
Sai ya gyara zaman sa
"Ya karin hakurin mu?"
Fuskarta ce ta sauya nan da nan, ya yi murmushi yana girgiza kansa
"Alhamdulillah." Tace bayan wasu yan dakiku
"Toh Alhamdulillah, Allah ya kara mana hakuri."
"Amin." Tace tana jin abun na taso Mata
"Abu daya nake so daga gareki dan Allah, ki cire komai ki barwa Allah, ki sani Muhammad ya tafi ba zai dawo ba, kiyi masa addu'a dan ita kadai yake bukata,maganar yaran nan da kika hana su zuwa ko ina har wajen mahaifiyarta na soke shi, ki barsu su yi rayuwar su yadda suka saba, duk wannan ba shine zai hana abinda zai faru ya faru ba sai dai idan har Allah be kaddara ba."
Shiru tayi, ranta ya sosu, tasan dole Yaya ce ta fada masa, dan tasan hakan ba halin Aunty bane ko me ya faru tsakanin su bata taba fadawa Baban, tayi mata wannan shaidar sai dai kawai ba zata fada bane.
"Kinji ko? Ayi hakuri a barwa Allah komai."
"In sha Allah."
Tace tana sauke kanta kasa, Abu daya da yake kara birge Baban da ita kenan, bata taba ketare maganar sa sai dai idan be yi ba, shiyasa yake respecting dinta sosai domin tayi masa abubuwa masu tarin yawa a rayuwar sa,da ba zai iya mantawa ba. Mikewa yayi yana karkade jikinsa, sai ta daga kai tana kallon sa
"Dama dalilin zuwan ka kenan?"
"A ah, zuwa nayi naga matata, uwargida sarautar mata!"
Murmushi ne ya subce mata, ta tashi ta rakashi har kofar falon, sannan ta dawo ciki shi kuma ya nufi bangaren Aunty.