×FREE PAGE: 3×
××××××
"Kwaret Waheedah haka sunan yake. Gidan nan idan kuka shiga zaku dauka a wata kasar kuke. Wani irin gidah ne wohoho aljannar duniya. Allah ka yi mana arziki. Wato wasu basusan ana talauci a duniya ba. Allah Hadiza zan iya jefa matashin kai na kwanta bacci a shirgegen wajen adana motocin gidan. AC sai sanyaya wajen take hadiza. Hmm Allah ka iya mana..." Najaatu ta karasa fada tana kada kai
"Ai Najaatu Allah ya kara mana wadatar zuci kawai. Idan kana kallon na sama da kai ba zaka taba sanyawa zuciyar ka salama ba. Wallahi damuwa ba zata sararawa zuciyar ka ba."
"Wallahi hadiza. Alhamdulillah kam. Allah ya aurar da yayanmu ga inda zasu ji dadi. Su dama nera su ture nera su hau nera."
"Toh Najaatu Amin. Amman kar ma su sanyawa zuciar su hangen mazan da suka yi musu nisa. ...."
"Eh ai addua ce muke yi. Tunda ba wanda yasan abunda gobe zata haifar."
"Hakane. Toh Allah ya amsa, Aamin."
"Aamin Aamin. Wato Waheedah kin gane gidan ko?"
"Eh.. Ai kinsan gate din layin yana kallon tsallaken titin dake kallon makarantar mu. To yafi sauki kabi ta layin a zuwa makaranta da dawowa. Wata rana mu da su Fanna mun dawo daga makaranta mun biyo ta layin. Akwai bishiyar fruit acikin gidan. Tun lokacin kafin ma kamar a tare gidan ."
"Kwarai don daga baya suka dawo. A kasar waje suke..."
"Eh tohm. Sai su fannah suka shigaa , Daman kofar gidan a bude muka ganta. Sai suka hango bishiyar. Shine suka daddauki karare da zasu karkado bishiyar don fruits din su fado. Suka shigaa ciki. Ni da Basira muna leken su. To mai gadin ashe yana ta waje. Saboda haka mu ya hango muna lekawa, Shine ya faffalla mana mari. Su kuma suna ganin yana marin mu suka shige da gudu..." Waheedah ta karasa fada tana runtse idanun ta. Tuno marin da suka sha.
"Maganin ku kenan. Gobe ma ai kwa kwara. " Cewar Umman su.
"Ah kiji ki hadiza da wata baudaddiyar magana. Yo ko ina ai ana dandalar arzikin wasu. Wani yaci a jikin me shi haka rayuwar ta gada. .. 'Dan gaba da iska da alama bai san darajar ya mace ba.da zai dora hannu ya mare su ...."
Ita dai Waheedah shiru tayi tana daga zaune . Yayinda mahaifiyar tata da najan Isubu suka cigaba da hirar su.
"Dan Allah ki daure ki kammala komai da wuri. Kinga tana zuwa kawai rakiya za'ayo miki zuwa can din. Idan kika gama aiyukan ki sai ki dawo gidah. "
"Insha Allahu Naja'atu. Allah ya kai mu ya bamu iko."
"Aamin. Ita wadda ta yo mun hanyar ta jaddadamun kan tsafta nan kuwa kinga bana jinki. Idan tsafta tana yawa ma taki tayi. Sai abu na biyu sunasan mai gaskia da amana. Nace mata kaf unguwar nan babu mai rikon amana irin ki.. Kinada gaskia kowa zai shaida. Tace sunason mai ladabi da biyayya. Nace mata sun samu. Bantaba sanin ki da munanan halaye ba Hadiza. Don haka na bada shedar gaskia akan ki. Na kuma san zasu same ki fiye da yadda suke zaton samu. Sai dai fatan Allah yasa ki fara a sa'a. Allah kuma ya hada zuciyoyin ku Amin. Allah kuma yasa su so ki su kauna ce ki. Ku zauna lapia har kawowar karshen zamantakewar ku."
"Allahumma Aamin Najaatu. Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. Allah yabiya miki dukkanin bukatun ki. Ya yaye miki dukkanin kuncin ki. Nagode, Nagode, nagode ."
Nan suka cigaba da maganganun su. Waheedah na mamnatsawa Yaya Kamal kafafun sa dake ciwo tamkar zasu ballo daga jikin sa saboda tsabar wahalar ciwo.
Hamisu autan Inna Sa'adatu ne ya shigaa dakin dauke da faranti da curin taliyar da bata fi cokali daya ba. Yanata lasar hannun sa daya.
"Ga shi Waheedah. Inji Marka. Taliya mai yanka yanka."
Dake tanada madaukakin kyankyami nan da nan ta shigaa girgiza kanta . Dubada yadda kudaje ke bin taliyar.
"Na koshi. ."
"Kai dawomun da abinci na." Cewar marka cikin daga murya.
Nan da nan jikin Umma na bari ta yi hanzarin karbe farantin hannun hamisu . Hadi da lekawa ta kofa tana kakaro murmushi
"Wasa take masa Marka . Zaa ci ai abar marmati ce. "
"Uwar yan kanzagi sarkin fadi ba a tambeya ka ba. Bashi ya dawo mun da taliya ta. Dan ubanta ko ina take cin irinta da zata ce ta koshi? "
"Kiyi hakuri marka."
"Kar ki sake bani hakuri. Ki bashi ya dawo da ita. Ko kunci ban yafe ba "
Jin jaka yasa Umma hadiza ta mikawa hamisu farantin, jikinta a sanyaye ta koma gefe ta tsakure tana mai aikawa Waheedah kallon kin kyauta da abinda kikayi.
Najaatu ta miqe zata tafi. Yayinda umma hadiza tabiye mata zata mata rakiya.
"Su marka ni ba'a rabon da ni?"
"Ah haba Najaatu. Zo ga wannan ki danqa kici ai abar marmari ce."
"Wasa nake wallahi. Bari na tafi, Mu kwan lapia "
"Toh Najaatu. "
Zasu saka kai su fuce sai ga shigar malam na lado cikin gidan. Kunnen sa daya ya nana speaker din rediyo ajiki yana sauraro.
Najaatu na ganin sa ta tsaya da fitar don su gaysa.
"Sannu da zuwa Malam." Cewar umma hadiza
"Yauwa .. Ah Malama Naja."
"Na'am malam Na lado. Ina wuni?"
"Lapia kalau Najaatu. Ai rannan mun gaysa da isubu ta wayar gurere."
"Allah sarki. Suna can "
"Wallahi.. toh ya iyali. Komai qalau.?"
"Kalau. Mungode Allah." Cewar Najaatu. Suka tsaya daga soro suna sake zantawa da Hadiza.
"Ahh. Marka yau taliyar kakkaryawa ce abincin rana? Ahh yau zaa sha dabge. Bismillah." Ya shiga nannade hannu riga zai tsoma hannun sa acikin farantin gabanta da take ci. Da sauri marka ta janye farantin tana afka masa harara,
"Matsa. Sahorami mijin sahorama. Da bakasan hakkin iyalin ka ba akan ka. Kazo fankan fankan zaka tsoma hannu aciki tamkar kai ne ka bada kudin abincin. "
"Kiyi hakuri marka. Najajje wurare da dama na rasa aikin yi. Tun safe Ina kofar dakalin gidan mati "
"Shi Matin ba zuciya yayi ba ya fantsama ya nemi na kansa har ya zama abunda ya zama ba yanzu. ? Ammaa saboda mutuwar zuciya kake binsa "
"Ki gafarce ni Markaa "
Tsakanin uwa da da sai Allah. Ta janyo farantin ta saka shi agaban sa. Fuskarta a yamitse tace,
"Sirikin ka ne ya bayar aka kawo."
"Sirikina kuma marka?. Bangane ba "
"Eh miji na samawa yarinyar nan wahidin. Don ba zamu zauna da zagada zagadan yammata ba bayan sun isa auren. Jikokin lawure baki daya ta aurar su "
Shiru malam na lado yayi. Ya ciko hannun sa ya zura taliyar a baka. Sai daya hadiye tukun yace,
"Wanene sirikin ?"
"Na'Ateeku dai. Kuma kasan kaf unguwar nan idan ka tsame gidan mati ba wanda yakai Na'Ateeku samu da zuciyar nema. .”
Naja'atun Isubu dake tsaye a zaure da umma hadiza sai gata a tsakiyar su marka
"Aure fa kikace Marka.? Auren ma kira sa da wanda zaki bawa sai na ateeku . Mutumin da ya haifeta. ? Haba marka..…..