FARHATAL QALB CHAPTER 2




 


×FREE PAGE: 2×



××××××


   Kukan Yaya Kamal ta jiyo tun daga soro kafin ma ta karasa shigaa cikin gidah.


"Wayyo Allah na .., Wayyo Allah na Umma..."


Daga can kurya ta jiyo muryar umman ta su tana lallashin sa.


"Kayi hakuri Kamal. Allah zai baku lapia da yardar sa , Da dukkanin masu rashin lapia na gidah dana asibiti."


"Kafa ta Umma.. kafa ta"


"Dena kuka Najeeb. Zaku samu lpy idan Allah ya yarda."


Kifa kanta tayi a jikin bangon soron. Yayinda ziraren hawaye suka shigaa reto a kyakkyawar fuskarta.


Marka taja dogon tsaki tana mai cigaba da sakatar hakoran ta .Ta zauna a saman turmi kafa daya na kan daya. 


"Garin aure auren ka. Gashinan ka auro jalli jogam. Da yara shanyayyu ko wata biyu basa yi da lapia. Kash Assh. Allah wadaran na ka ya lalace. Wohoho."


Duk maganganun da Marka kakar su takeyi. Waheedah na jiyo ta daga soro. Ta share hawayen da ke cigaba da kwarara da kasan hijabin jikinta. Kana ta shigaa cikin gidan kan ta a kasa.


"Gashi marka.."


Da sauri marka ta wafce ledar tana mai leka cikin ta 


"Taliyar kakkaryawa da tumatirin gwangwani. Lallai yau ta ke sallah. Wannan yaro Na'Ateeku yasan abun arziki. Bai gayan ki sako ki sanarmun ba?"


"Au yace komai yayi zai bada har da la'ada. "


" A hayye sama mata...!!" 

Cewar marka. Hade da dora hannunta akan katon hancin ta ta saki gud'a ... Ta kuma fara taka rawa tana shilla hannuwa .


Ita dai Waheedah wucewar ta kawai tayi cikin dakin su tana dafe kwankwason ta.


"Ke wahidin .. " Marka ta sake kirawo ta.


"Na'am  "


"Kin gama shiqar ne da zaki shige 'daka?"


"Na kammala Marka."


Marka dake bin taliyar hannunta da kallo taja dogon tsaki. 


Ita dai Waheedah bata sake cewa komai ba. Ta cire kayanta ta daura zani hadi da zura hijabi. Sauran omon wankinta ta dauka ta hade shi da kayan makarantar ta acikin bokiti. Tayi hanyar dakin su Yaya Kamal 


Bakinta dauke da sallama ta shigaa ciki. Umman su na tsakure daga gefe ta zabga tagumi.  Ta gayshe da Umman su da ya Kamal yayanta. Kafin ta bisu da ya jikin su? Ta hada da adduar Allah ya basu lapia. 


Gwanin ban tausayi haka ta tsaya tana bin yan uwan nata da kallo. Hakika suna jin jiki shekara da shekaru. Ga shi su ba hali ne da su ba da zasu yita sintirin asibiti. 


Ta sake sauke numfashi a karo na ba adadi tana mai zabga tagumi 


"Ya akai ..Ki ka dawo da wuri Waheedah?"


"Bakomai ummah.  "


Umman ta danyi yaqe kafin ta girgiza kai kawai 


"Kawai dai ki ce saboda baa biya kudin wata bane ko?"


Waheedah ta daga kai alamun eh.


"Allah ya kyauta .. Ina su Zainab su suna makarantar ko?"


"Eh.... Marka ce ta je ta biya musu." Ta karasa fada tana mai lankwasa yan yatsunta 


"Abincin ki na daki wajen randa. Tashi kije ki ci. Ko wanka zaki?"


"Uniform dina zan wanke tukun. Shiqar su dawa Marka ta sa ni."  Tana gama fada ta miqe tayi waje. 


 Tuqa tuqa ta je da ke ta gidan su ta baya ta taro ruwa. Nan da nan ta durje kayan ta 'dauraye ta shanya. Ta sake debo wani tayo wanka taci abinci. Tayi sallah. 


Ko da ta karasa cin abincin tayi sallah,  Ruwa ta shiga jidowa tana zubawa a inda suke adana ruwan su. Ta cika ko'ina tsaf sannan ta koma dakin da su Ya Kamal suke. 


"Kije ki sallah umma. Kici abinci" Tace da Umman su da ta hada kai da gwiwa. 


Batayi musu ba ta tashi ta fice daga dakin. Waheedah ta matsa kusa da yan uwan nata tana jera musu sannu.


Baa jima ba sai ga Sa'adatu nan ta dawo. Daya matar Malam Nalado mahaifin su Waheedah. Itace ta biyu,/ Amaria. 


Da waqa ta shigo gidan tana jujjuya kai. 


" A hayye wata tafi wata... A   sa'a wata tafi wata. A hayye ko ni na fi. Uhm uhm kamshin menene wannan marka?"


"Taliyar kakkaryawa ce dan arziki irin albarka Na'Ateeku ya aikon harda tumatirin gwangwani "


"Lallai yau zamu ci dabge....."


"An dade ba a hadu ba kam." Cewar marka da ke gaban murhu tana gyara karairakin ciki. 


Hadiza (mahaifiyar su Waheedah) Ta fito daga cikin daaki ta nufi wajen Marka ta sunkuya da ladabi,


"Marka kawo na karasa."


"Ki karasa me? Matsa kafin na kai miki bugu.."


Da sauri hadiza ta miqe ta shige dakin su Kamal jikinta a sanyaye. Yaran suka bita da kallo cikeda tausayi. Dukkanin su su biyun suna kwance akan katifu kanana irinta yan boarding dinnan . Kana kallon su kasan majinyata ne dake bukatar kulawa. Yayinda Waheedah ke gaban su tana musu sannu. Ita kadai ce mai lapia acikin yan uwan nata. 


Cikin haka sai ga Najan Isubu ta shigaa gidan bakinta dauke da sallama. Sa'adatu ta dubeta ta watsar. Najan ma ta mayar mata da kallo sheqeqe tana mai tura daurin dankwalin ta gaban goshi.


"Marka ina wuni?"


"An kwan kalau? Ya iyali ?"


"Alhamdulillah! Ya fama da mu? Ya jikin su Najeebu?"


"Da godia. Ya wajen su Isubu. Yana tashi ko?"


"Eh suna can. Shi da su gurare."


"Allah sarki..."


Sallama tayi ta shige dakin su Kamal. Nan da nan kowannen su ya shigaa gaisheta. Tayi musu ya jiki tana duban su cikin tausayawa. 


"Ungo nan Waheedah." Ta zuge dan tofi ta janyo jaka daya (dari biyu) ta miqawa Waheedah.


"Me zan siyo.?" Cewar Waheedah, 


"Ba abunda zaki sayo. Kudin makaranta na baki. Kije ki biya idan Allah ya kai mu gobe. Kinji ko?"


Nan da nan fuskar Waheedah ta kyakkyabe da farin ciki. Hawaye daya na bin daya suka shigaa reto a fuskar ta. Ta tsugunna har kasa tana godia 


"Nagode. Ubangiji Allah ya saka miki da mafificin alkhairin sa. Allah ya biya miki bukatun ki na duniya da lahira . Allah ya..."


"Godiar me ake ne. ?"


"Godiar kudin wata ce marka. "


"Aiho to..."


"E.. Ina ce wani bayani ne... Na karya miki dankwali Markatu." Najan Isubu ta sake daga murya tana mai sakin shewa. Abunda ya sake rura wutar zuciar marka. Taja tsaki tana mita.


Hadiza tayita yiwa najan Isubu godia .


"Bakya gajiya. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya yaye miki dukkanin kuncin da ke damun ki ya wanye miki da burukan ki.. Mungode, Mungode "


"Kaiya bar godia hakanan hadiza ai mun zama daya. Menene amfamin amintar idan har babu taimakekeniyar juna aciki? Kada kuma ki manta kafin nayi miki kece kika yiyyi mun. Don haka abar zancen. Ni magana ce muhimmiya ta kawo ni...."


"Toh... Ina sauraron ki Najaatu."


"Magana ce akan aikatau. Ko ince wankau."


"Toh Alhamdulillahi. Aina ne?"


"Acan GRA dinnan. Yan kananan kayyayaki zaa dinga wanke musu. Domin inji ne ke musu na manyan sannan kuma mota ce ke zuwa ta dauki wankin su ta kai kamfanin wanki ayi ta dawo musu da shi. Sai yan tsince tsincen gyara da ba za'a rasa ba."


"Tohm Najaatu. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi..."


"Kai wannan godia. Yauwa gidan da zaki dinga yi din gidan dogaye ne. Inkiyar ahalin gidan ce. Wai ahalin dogaye, idan kaga gajere to baqo ne. Kinsan da ba a kasar nan ma sike ba, daga baya suka dawo. Wadda ta samamun aikin tace na fara zuwa gobe. Nace mata zan kawo wadda zata musanye ni. Ni cin ruwa nake a hannaye na. Na dena wankau. Amman tace da albashi me tsoka wallahi. Kuma ba yunwa. .."


"Ahh Masha Allahu. Allah ya biya ki Najaatu."


"Aamin. Kinji sunan gidan da turanci. Adams menene.?" Ta daga kai tana tunani.


Waheedah dake gefe ta dan jujjuya kai tana tunowa kafin cikin daga murya tace.


"The Adams family.........


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links