FARHATAL QALB CHAPTER 1

 



*PAID BOOK*

*FREE PAGES: 1*



*FREE PG: 1*


×NEW G/R/A SHURAH××


  

   *A* nutse take tafiya kanta a kasa, Sanye cikin uniform ruwan sararin samaniya. Yayin da hijabin da ke jikinta fari ne qal da shi. Kafafunta sanye cikin sandal takalmi daya gaji da dinkin zare. Yayinda kafafuwan ta ke cikin safa fara. 


Sai yar jakar goyo ta buhu mai igiya. Idanuwanta na cikin gilashi da alama na kara gani ne wato medicated. Ita da kayan da ke sanye jikinta komai a tsaftace yake. 


Uniform din sun sha ninkin guga ko ina tsaf tsaf da shi. Cikin sassarfa take tafiyar komawa gidah. 


layin shiru. Tsit! Sai kukan karnuka da na kanari. Ko'ina jibga jibgan gate ne. Ya yinda masu gadi ke kofar gidajen da suke gaadi. Su na hira.


Manyan motoci na faffake a kofar gidajen. Dake dauke da shuka da dama. Iska mai ratsa jiki da bargo ce ke faman kaada bishiyu. 


Manyan idanunta dake cikin gilashi ta sauke akan signboard/Tambarin da ke rubuce da: The Adams Family!!  


Saurin wuce wa tayi har tana tuntube. Domin ba zata taba mantawa da gigitaccen marin da me gadin gidan yayi musu ba itada kawayenta ranar wata jumu'ah da sakaliya.


Gaban ta na tsananta bugawa ta fi ce daga cikin layin mai dauke da tankamemen gate mai nishi. Layi ne na masu hannu da shuni. Wato masu kudi. 


Tana ficewa daga layin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kana ta cigaba da tafiya zuwa layin gidan su. Kallo daya zaka yiwa unguwar tasu kasan ta marasa hali ce. Tulin shara mai tsananin tashin hankula ce a gefen wani bingi da suka mayar wajen zubar da shara. 


Ya yinda yan jari bola ke kan bolar suna tsince tsincen su. Wanda baki daya yaran unguwar ne ta:



××UNGUWAR SHURAH××



    Jerin wasu mata tsofaffi ne ke gefen wani tsauni. Sanye cikin riga da zani da dankwali kowanne daban daban. Sunyi butu butu da su suna shiqar masara, Maiwa, Dawa, Gero da kuma masara. 


"Ke zo nan wahidin. " Cewar wata tsohuwa take cikin tsofaffin da ke shiqa. 


Da sauri ta karasa duk kuwa da kasan zuciyaar ta bata kaunar sunan da Marka kakar su ke kiran ta dashi. Sarai tasan yadda sunanta yake. Amman taki ta kirata da ainihin sunan. Sai ta boye shi cikin wata manufa dake kasan zuciyar ta.


"Ina wunin ku.  Ya aiki?" Ta tsugunna har kasa tana gayshe da su baki daya.


"Lapia kalau Waheedah. An taso ku ne kika dawo da wuri haka?" Cewar lawuri aminiyar kakar su Marka.


Girgiza kai kawai tayi. Ahankali tace,


"Kudin makaranta ne ban biya ba."


"Ungo rike ki karasa. Idan kin gama kije ki wajen Na'Ateeku ki ce ya baki sakon."


"Tohm Marka.." Ta amsa, Tare da matsa wa suka ketare ta suka wuce. Har takalmin Marka kasan ya gogi hijabin jikin ta.


 Yayinda ta dauki kwaryoyin ta shiga dagawa sama daya kasa daya. Iska na dauke dattin....


Haka ta jima tana shiqar kowanne. Ta kammala tukun sannan ta dure kowanne a buhu bayan ta a'aauna. 


Uniform dinta ya rine da kura. Hakama gilashin idanunta da kurar ta dabaibaye shi. 


Wajen shagon Na'Ateeku ta nufa. Tana zuwa ta tsaya daga gefen shagon bayan ta gayshe shi.


"Marka ce ta aiko ni..."


"Eh na shi na . " Yana magana yana jan kasan leben sa. Ya dakko leda baka ya saka taliyar kakkaryawa guda daya da tumatirin gwangwani.


"Gashi ki bata."


Ta miqa hannu biyu zata karbi ledar yayi azamar riko tafun hannunta. Take jikinta ya dauki rawa ta saki ledar a kasa gabanta na tsananta bugawa.


"Haka fatar ki ta ke lallausa. ?Tamkar kedin ba yar yankin awaki ba na unguwar shura? Wabillahil lazi wani sai yace a GRA din kike..." Ya karasa, Hadi da daukar ledar ya sake mika mata.


Waheedah dai a firgice ta ke da shi. Taja baya tana girgiza kai.


"Ungo matsoraciya... Ki cewa kakar taki komai yayi, Na wane darajar kaya.? Ki ce harda la'ada za'a. Don na yaba kwarai. "


Sam bata gane zancen sa ba. Ta dai matsa da sauri ta dauke ledar. Ta fuce daga cikin shagon tamkar zata tashi sama dan sauri.


"Waheedah Umman ku na gidah?" Cewar Najan Isubu kawar Umman mu.


"Eh to .Da ke ban koma gidan ba. Ina wuni?"


"Lapia kalau. Idan tana nan kya…Koda yake basshi ma zan biyo da kai na idan na shigaa gidan Furera nayo mata barkar Aina'u. "


"Tohm ..." 


Kai tsaye ta kama hanyar shiga gidan su. Gaban ta na tsananta bugawa da mamakin Na'Ateeku mai shago. Dan iska ne ashe? 


Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kana ta shige cikin gidan su bakin ta dauke da sallama...!!!


Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links