TARIHIN ABEX (ABBA M YUSUF)
Cikakken sunansa Abba M Yusuf (an haife shi a ranar 23 ga watan Yuni a Maiduguri, jihar Borno, Najeriya) wanda kuma aka fi sani da Abex
Yakasance jarumin Kannywood ne na Najeriya kuma mai shirya fina-finan Hausa.
Ya shiga masana’antar fina-finan Hausa a tsakanin shekarar 2002 – 2003 a matsayin ma’aikacin cigaban shiri daga baya Kuma ya ci gaba da shiryawa.
RAYUWA
Farkon Rayuwa da Sana'a
“Abba M. Yusuf sunan sa ne da aka fi sani da Abex a fagen waka, an haife shi a ranar 23 ga watan Yuni a Maiduguri babban birnin jihar Bornon Najeriya, ya halarci makarantar firamare da sakandare a Maiduguri. Daga baya a kusa da 2002 - 2003
Daga bisani yakoka izuwa jihar Kano ta Najeriya inda ya shiga masana'antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood a Arewacin Najeriya a matsayin ma'aikaci bayan fage da Kuma cigaban samar da shiri.
A Hira da akai dashi ya bayyana aniyarsa kan dagewa don tabbatar da burinsa a wajen harkar fim wadda yafara tun 2004.
Mashiryin ya bayyana kansa a matsayin furodusa tare da shirya wani fim mai suna Linzami bisa ga nufinsa.
Sannan kuma ya gabatar da kansa a matsayin jarumi, cikin nasara fim din ya ba da sakamako a matsayin daya daga cikin fitattun fina-finan Hausa a wancan lokacin da ya ja hankalin duniya kan ci gaban masana’antar.”
Mata
Abba m Yusuf nada mata daya yazuwa yanzu
Net Worth
Adadin kudin Abba M. Yusuf a shekarar 2022 an kiyasta kusan dala 250,000.