Tuzurai Zasu Fara Biyan Haraji na Rashin Aure


 

Matasa da tazurai sun ga ta kansu a kasar Afirka ta kudu inda aka sanya dokar biyan haraji ga duk wani matashi ko tazuru da bai yi aure ba a yankin Nkuthu dake Arewacin Kwazulu Natal na kasar, kamar yadda talabijin na Enca ta ruwaito. 

Majiyar Trustposts.com ta ruwaito duk wani matashin yankin daya kai munzalin aure daga shekara 18 zuwa abinda yayi sama kuma bai yi auren ba zai biya harajin Randi hamsin(R50) da aka yi ma lakabi da harajin ‘Samari marasa aure’, kamar yadda hukuma ta tanadar. 

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links