- Gwamnatin tarayya ta amince da biyan wadanda suka cika shirin tallafin Survival Fund - An ruwaito cewa, za a fara biyan sama da mutane 150,000 na shirin a fannin kasuwacin safara
- An kuma bayyana cewa, kashi 43 na wadanda suka ci gajiyar shirin na Survival Fund mata ne Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Katagum, a ranar Litinin ta ce tun daga farkon wadanda suka fara cin gajiyar shirin a ranar 17 ga Janairun 2021, an amince da biyan jimilar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin Survival Fund a fannin sufuri.