Guguwa Ce Ta Sa Na ‘Samu Juna Biyu’ —Mace

 


Yan sandan na binciken wani abin al’ajabi da ya faru da wata mata mai shekara 25 wadda ta yi ikirarin cewa ta haihu bayan samun juna biyu da awa daya, kuma wucewar iska ce ta samar mata da juna biyun.

Matar mai suna Siti Zainah wacce ake ta yada ta game da batun ta hanyar izgilanci, bayan ta ce wucewar guguwa ce ta sa ta samu juna biyu a ranar 10 ga watan Fabrairun da ya wuce.

Zainah ta ce, “Na haifi jaririya bayan awa daya da samun juna biyu.” A cewar kafofin labarai na kasar Indonesiya.

Mai jegon ta ce tana hutawa a gidansu da ke garin Cianjur, a Gundumar Java ta Yamma tare da danta na farko, sai ta ji iska ta shiga jikinta, bayan dan lokaci sai ta fara nakuda.

“Bayan Sallar Azahar, sai na kwanta kan cikina, jim kadan sai na ji iskar na saduwa da ni.

“Lokaci kadan sai cikina ya girma, sai ya ragu kamar yadda yake a baya, sannan ya sake girma,” inji ta.

Zainah ta yi zargin cewa, cikin nata ya fara girma ne kimanin minti 15, bayan ta gaza fahimtar abin da ke faruwa da giftawar iskar guguwar sannan ta fara jin ciwon ciki.

Daga nan ta fahimci ba daidai take ba, sai ta bukaci ’yan uwanta su kai ta cibiyar kiwon lafiya ta Cidaun da ke unguwar.

Bayan ganin likita, sai ya ce tana da jariri a mahaifarta, kuma lokacin haihuwar ya yi.

“Na firgita saboda lokaci guda na samu juna biyu, sannan na haihu,” inji ta.

Source: Aminiya

Previous Post Next Post
Sponsored Links
Sponsored Links