Wata budurwa ta hada baki da ’yan bindiga suka sace saurayin da ya nemi aurenta don samun kudin yin shagalin bikinta da wani.
Matashin na cikin shirye-shiryen auren ta ne aka samu sabani a tsakaninsu suka raba jiha, sai dai Aminiya ba ta san musabbabin sabanin ba.
Amma duk da cewa sun rabun, tsoffin masoyan ba su yanke hulda a tsakaninsu ba, har zuwa ranar da aka yi garkuwa da shi.
Ranar Alhamis da dare ne aka kame matashin mai shekara 50, ba a sake ganin sa ba, sai gawarsa aka tsinta a hanyar Durbawa da ke Karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato.
Yadda aka sace shi
Majiyarmu ta ’yan sanda ta ce budurwar ta hada baki ne da sabon saurayin da zai aure ta aka sace tsohon saurayin don su samu kudin da za su yi amfani da shi a bikinsu da ke matsowa.
Source: Aminiya