Shafin Instagram na Northern_hibiscuss ya tara wa tsohon jarumi Bashir Bala Ciroki kudi fiye da naira dubu dari biyu a kwanaki baya.
Dalilin tara wannan kudin ga jarumi shine bayan da aka samun labarin cewa yana tallan kunin aya.
A hira da Arewa 24 tayi, tsohon jarumin ya yi ikirarin cewa masu shirya fim din Hausa da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim yanzu, shine dalilin da ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.
Jarumin Ali Nuhu ya kalubalanci wani a shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da tsohon jarumin Bashir Bala, wanda aka fi sanin sa da Ciroki, ya taimaka wa lokacin da tauraruwarsa ke haskawa a kannywood
Ali nuhu ya ce babu wanda yake a Kannywood da zai taimaka wa jarumi Ciroki, ya kamata dai ya dawo shirin fim ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kamar sauran.